Go to full page →

Babi na 24—Cikin Wuri Mafi-Tsarki BJ 421

Batun haikalin ne mabudin da ya bude asirin yankan burin nan na 1844. Ya bayana cikakken tsarin gaskiya da ya nuna cewa hannun Allah ne ya jagoranci babban aikin nan game da zuwan Kristi ya kuma bayana aikin da ya kamata mutanensa su yi yanzu. Kamar yadda almajiran Yesu, bayan daren bakincikinsu da yankan burinsu, suka ga Ubangiji, haka wadanan yanzu suka yi farinciki, su wadanda sun yi begen zuwansa na biyu da bangaskiya. Sun yi begen bayanuwarsa cikin daukaka domin ba da lada ga bayinsa. Da shike burinsu bai cika ba, suka manta da Yesu, tare da Maryamu a kabarin kuma suka ce: “Sun dauki Ubangiji daga chikin kabarin, ba mu san inda sun ajiye shi ba.” Yanzu kuma sun gan shi a wuri mafi-tsarki, Shi Babban Priest nasu wanda jima kadan zai bayana a matsayinsa na sarkinsu mai-kubutar da su. Haske daga haikalin ya haskaka baya da yanzu da nan gaba. Sun san cewa Allah ya shugabance su tawurin kadararsa mara kuskure. Ko da shike, kamar almajiran farkon, su kansu basu fahimci sakon da suke dauke da shi ba, duk da haka sakon daidai ne ta kowace fuska. Shelarsa da suka yi sun cika nufin Allah ne, kuma aikinsu bai zama banza ba, ga Ubangiji. Da shike an sake samo su zuwa ga bege mai-rai, suka yi murna kwarai “da murna wadda ta fi gaban a fadi, chike da daukaka kuma.” BJ 421.1

Annabcin Daniel 8:14 cewa: “Har yamma da safiya guda alfin da dari uku: kana za a tsarkake wuri mai-tsarki,” da sakon malaika na fari cewa: “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukunchinsa ta zo,” suna batun hidimar Kristi ne a wuri mafi-tsarki, game da shari’a ta bincike, amma ba zuwan Kristi domin fansar mutanensa da hallakawar miyagu ba. Kurskuren bai shafi lissafin zamanun annabcin ba, amma a kan abinda zai faru ne a karshen kwana 2300 din. Ta wurin kuskuren nan masu bi sun sha cizon yatsa, amma kuma duk abinda annabcin ya fada da dukan abin da suka yi bege, sun cika. Daidai lokacin da suke bakincikin yankan burinsu, al’amarin da aka yi annabcin sa ya cika, kuma dole ne a cika shi kafin Ubangiji ya bayana domin ba da lada ga bayinsa. BJ 422.1

Kristi Ya zo, ba a duniya ba yadda suka zata, amma kamar yadda alamar ta nuna, Ya shiga wuri mafi-tsarki ne a haikalin Allah a sama. Annabi Daniel ya nuna cewa a wannan lokaci yana zuwa wurin mai-zamanin da ne. Ya ce: “A chikin ruyai na dare na gani, ga shi, tare da gizagizan sama, wani ya zo mai-kama da dan mutum; ya zo kuma har wurin mai-zamanin da, aka kawo shi a gabansa har ya yi kusa.” Daniel 7:13. BJ 422.2

Annabi Malachi ma ya yi annabcin wannan zuwan. Ya ce: “Ubangiji ma wanda ku ke bidassa za ya zo a haikalinsa ba labari; malaikan alkawali kuma, wanda ku ke murna da shi, ga shi, yana zuwa, in ji Ubangiji mai-runduna.” Malachi 3:1. Zuwan Ubangiji haikalinsa faraf daya ne, ba tsammani ga mutanensa. Basu zata zai zo wurin ne ba. Sun zata zai zo duniya ne, “chikin wuta mai-huruwa, yana daukan ramako bisa wadanda ba su san Allah ba, da wadanda sun ki yin biyayya ga bisharar.” Tasalunikawa II, 1:8. BJ 422.3

Amma mutanen ba su shirya saduwa da Ubangiji ba tukuna. Akwai aikin shiryawa da za a yi masu. Za a ba da haske da zai bi da tunaninsu zuwa haikalin Allah a sama, kuma yayin da tawurin bangaskiya za su bi Babban priest na su cikin hidimarsa a can, za a bayana masu sabon haske. An kuma shirya ba ekklesiya wani sakon gargadi da umurni kuma. BJ 422.4

Annabcin ya ce: “Amma wane ne za ya daure da ranar zuwansa? Wane ne kwa za ya tsaya kadan ya bayana? Gama yana kama da wutar mai-gyaran karfe, kamar sabulun mai-gyaran tufa; za ya kwa zamna kamar mai-gyaran azurfa mai-tsarkakenwatta, kuma za ya tsarkake yayan Levi, yana sabtatadda su kamar zinariya da azurfa; har su mika ma Ubangiji hadayu chikin adilchi.” Malachi 3:2,3. Wadanda ke raye a duniya sa’anda tsakancin Kristi a cikin haikali na sama za ya kare za su tsaya a gaban Allah Mai-tsarki ba matsakanci. Dole tufafinsu su kasance babu la’ani, a tsarkake halayensu daga zunubi ta wurin jinin yayyafawa. Ta wurin alherin Allah da kokarin kansu, dole su yi nasara cikin yaki da mugunta. Yayin da hukuncin binciken ke gudana a sama, yayin da ake cire zunuban masu bangaskiya daga haikalin, za a yi aiki na musamman, na kawas da zunubi daga mutanen Allah a duniya. An fi bayana wannan aikin a cikin sakonin Ruya 14. BJ 423.1

Sa’anda an kamala aikin nan, masu bin Kristi za su kasance a shirye domin bayyanuwarsa. “Sa’an nan hadayar Yahuda da Urushalima za ta zama abu mai-dadi ga Ubangiji, kamar chikin kwanakin da, chikin shekaru na tuntuni.” Malachi 3:4. Sa’anan ekklesiyar da Ubangijinmu za ya karba ma kansa zai kasance “ekklesiya mai-daraja, ba tare da aibi ko chira ko kowane abu misalin wadannan.” Afisawa 5:27. Sa’an nan za ta kasance “mai-leke kamar safiya, kyakyawa che kamar wata, garai kamar rana, mai-ban tsoro kamar rundunar yaki da tutochi.” Wakar Wakoki 6:10. BJ 423.2

Ban da zuwan Ubangiji haikalinsa, Malachi ya kuma yi annabcin zuwansa na biyu, don zartas da hukuncin. Ya ce: “Zan zo kusa da ku domin shari’a; zan zama shaida mai-samri a bisa masu sihiri, da mazinata, da masu-natsuwa da karya, da wadanda ke yi ma mai-aikin lada zalumchi wajen zanchen hakinsa, suna aikin zalunchi ga gwamruwa, da maraya, suna hana ma bako wajibinsa, ba su kwa ji tsoro na ba, in ji Ubangiji mai-runduna.” Malachi 3:5. Yahuda ya ambaci al’amri dayan inda ya ce: “Ku duba ga Ubangiji ya zo da rundunan tsarkakansa, garin ya huykumta shari’a bisa dukan mutane, domin shi kada dukan masu fajirchi kuma a kan dukan ayukansu na fajirchi da suka yi chikin fajirchinsu.” Yahuda 14,15. Wannan zuwan da zuwan Ubangiji wurin haikalinsa abu biyu ne daban dabam. BJ 423.3

Zuwan Kristi a matsayin Babban Priest namu a wuri mafi-tsarki don tsarkake haikalin da Daniel 8:14 ya ambata; zuwan Dan mutum wurin mai-zamanin da, wanda Daniel 7:13 ya ambata, da zuwan Ubangiji haikalinsa da Malachi ya yi annabcinsa suna bayana abu dayan ne, kuma an misalta wannan a wurin zuwan angon a wurin bukin auren, wanda Kristi ya bayana a cikin misalin nan na budurwai goma na Matta 25. BJ 424.1

A cikin damina da kaka na 1844, an yi shelan nan cewa: “Angon ya zo!” Sassa biyu da budurwai masu azanci da marasa azancin suka misalta sun bayyana: sashi daya masu sauraron zuwan Ubangiji da farinciki, suna kuma shiri sosai don saduwa da shi, wani sashin kuma cike da tsoro suka gamsu da ganewar gaskiyar kawai, amma ba su da alherin Allah. Cikin misalin, sa’anda angon ya zo, wadanda suna nan a shirye suka shiga tare da shi wurin anganchi.” A nan an nuna cewa zuwan angon zai faru kafin auren ne. Auren yana misaltar karban mulkinsa da Kristi zai yi ne. Birni mai-tarkin, Sabuwar Urushalima wadda ita ce babban birni da wakiliyar mulkin, ana kiran ta “amarya, matar Dan rago.” Malaikan ya ce ma Yohanna: “Ka zo daganan, ni nuna maka amarya, matar dan rago.” “Ya dauke ni cikin ruhu,” in ji annabin, “ya nuna mani birni mai-tsarki Urushalima, tana sabkowa daga chikin sama wurin Allah.” Ruya 9-10. A bayyane dai amaryar tana misaltar Birni Mai-tsarki ne, budurwai da suka fita domin su sadu da angon kuma misalin ekklesiya ne. Cikin littafin Ruya an ce mutanen Allah ne aka gayyace halartar bukin auren. Ruya 19:9. Idan gayyatattu ne, ba za a misalta su da amarya ba. Annabi Daniel ya ce Kristi zai karbi sarauta da daukaka da mulki daga wurin mai-zamanin da, za ya karbi Sabuwar Urushalima, babban birnin mulkinsa, “shiryayya kamar amarya da ado domin mijinta.” Daniel 7:14; Ruya 21:2. Sa’an da ya karbi mulkin, zai zo cikin darajarsa, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, domin fansar mutanensa, wadanda za su zauna tare da Ibrahim da Ishaku da Yakubu a tebur dinsa a cikin mulkinsa (Matta 8:11; Luka 22:30), don shiga bukin auren Dan ragon. BJ 424.2

Shelar cewa “Ga Ango!” da aka yi cikin daminan 1844 ta sa dubbai suka yi tunanin zuwan Ubangiji nan da nan. Daidai lokacin, Angon ya zo, ba a duniya ba, yadda mutane suka zata, amma zuwa wurin Mai-zamanin da a sama, zuwa auren, watau bukin karban mulkinsa. “Wandanda suke shirye suka shiga tare da shi wurin anganchi: aka rufe kofa.” Ba a ce za su kasance a wurin angancin su kan su ba; domin a sama ne anganci ke gudana, su kuma suna duniya ne. Masu bin Kristi za su zama “masu duban hanyar Ubangijinsu, sa’anda za ya koma daga bukin anganchi.” Luka 12:36. Amma za su gane aikinsa, su kuma bi shi tawurin bangaskiya yayin da zai shiga wurin Allah. Ta hakanan ne ake cewa sun shiga wurin angancin. BJ 425.1

Cikin misalin budurwai din, masu mai a cikin santulansu da fitilunsu ne suka shiga wurin angancin. Wadanda, hade da sanin gaskiya daga Littafin, suna kuma da Ruhun Allah da alherinsa, wadanda kuma cikin daren gwajinsu, suka yi hakurin jira, suna nazarin Littafin don Karin haske, su ne suka ga gaskiya game da haikali na sama, da kuma sakewar hidimar mai-ceton, ta wurin bangaskiya kuma suka bi Shi cikin aikinsa a haikali na sama. Kuma dukan wadanda tawurin shaidar Littafin su ke karban gaskiya dayan, suna bin Kristi ta wurin bangaskiya yayin da ya ke shigowa gaban Allah don aiwatar da aikin tsakanci na karshe, a karshensa kuma Shi karbi mulkinsa; dukan wadannan ana misalta cewa sun shiga wurin angancin ne. BJ 425.2

Cikin misali na Matta 22 an gabatar da misalin nan na aure, an kuma misalta cewa shari’a ta binciken tana faruwa ne kafin angancin. Kafin angancin. Sarkin ya shigo domin ya ga wadanda aka gayyata, domin ya ga ko kowa ya sa rigar angancin, tufafi mara aibi na hali wanda aka wanke ya zama fari cikin jinin Dan ragon. Matta 22:11; Ruya 7:14. Wanda aka iske ba ya yafe da rigar, an fitar da shi, amma dukan wadanda an bincika an ga suna yafe da rigar angancin, Allah ya karbe su, an kuma tabbatar cewa sun cancanci rabo cikin mulkinsa, da wurin zama kuma a kursiyinsa. Wannan aiki na binciken hali, na sansance wadanda ke shirye domin mulkin Allah shi ne shari’ar bincike, aiki na karshe a haikali na sama. BJ 426.1

Sa’anda aikin bincike ya kare, sa’anda aka kamala shari’ar dukan wadanda a dukan sarraki suka ce su masu bin Kristi ne, sa’an nan ne, ba kafin nan ba, za a rufe gafara, a kuma rufe kofar jin kai. Ta hakanan, cikin furcin nan, “Wadanda suna nan a shirye suka shiga tare da shi wurin anganchi: aka rufe kofa,” ana kai mu ta wurin hidimar karshe ta mai-ceton, zuwa lokacin da za a kamala babban aikin nan na ceton dan Adam. BJ 426.2

A hidimar haikali na duniya, wanda misali ne na hidimar haikali na sama, sa’an da Babban Priest a Ranar Kafara ya shiga wuri mai-tsarki, aiki a wuri na farin yakan tsaya. Allah Ya umurta cewa; “Babu mutum da za ya kasanche a chikin tent na taruwa sa’anda ya shiga garin ya yi kafara a wuri mai-tsarki, har lokacin da ya rigaya ya fito.” Leviticus 16:17. Saboda haka sa’anda Kristi ya shiga wuri mai-tsarki don aiwatar da aikin karshe na kafara, ya dena hidimarsa a wuri na farkon. Amma sa’anda hidimar wuri na fari ta kare, hidimar wuri na biyu ta fara kuma. A hidimata misalai din, sa’anda babban priest ya bar wuri mai-tsarki a Ranar Kafara, ya kan shiga a gaban Allah ya mika jinin hadaya ta zunubi a madadin dukan Israilawa da suka tuba da gaske daga zunubansu. Sabo da haka Kristi ya kamala sashi daya na aikinsa ne a matsayinsa na matsakancinmu, domin shiga wani fannin aikin kuma, ya kuma nuna jinin sa a gaban Uban a madadin masu zunubi. BJ 426.3

Adventist ba su fahimci batun ba a 1844. Bayan lokacin da aka zata Mai-ceton zai zo ya wuce, sun ci gaba da zaton cewa zuwansa ya kusa, suka aza cewa sun kai wani muhimmin hargitsi ne, kuma aikin Kristi na matsakancin mutum a gaban Allah ya kare, suka dauka cewa Littafin yana koyar da cewa za a rufe gafara jima kadan ne kafin ainihin zuwan Ubangiji cikin gizagizai na sama. An dauka cewa wannan a bayane yake daga nassosin da ke annabcin lokacin da mutane za su nema, su kwankwasa, su kuma yi kuka a kofar jin kai, kuma ba za a bude ba. Tambayar a gare su ita ce ko ranar da suka zata Kristi zai zo ba ita ce farkon lokacin nan da zai gabaci zuwansa ba? Sa’anda suka ba da gargadi cewa hukumcin ya kusa, suka ji kamar sun gama aikinsu ga duniya ke nan, suka rasa himmarsu ta ceton masu-zunubi, yayin da ba’a da sabon masu fajirci ya zama masu kamar wata shaida kuma cewa an rigaya an janye Ruhun Allah daga masu kin jin kansa. Dukan wannan ya karfafa su cikin zatonsu cewa an rufe gafara, ko kuma an rufe kofar jin kai. BJ 427.1

Amma Karin haske ya samu sa’anda aka yi nazarin batun haikalin. Sai suka ga cewa daidai ne da suka gaskata cewa karshen kwana 2300 din nan a 1844 farkon wani muhimmin hargitsi ne. Amma yayin da gaskiya ne cewa wancan kofar bege da jinkai da mutane sun rika bi don saduwa da Allah har shekara 1800 ta rufu, an kuma bude wata kofar, aka kuma mika ma mutane gafarar zunubi ta wurin shiga tsakani na Kristi a wuri mafi-tsarki. An rufe wani sashi na hidimarsa, domin a fara wani sashen kuma. Akwai dai “budaddiyar kofa” zuwa haikali na sama inda Kristi ke hidima a madadin mai-zunubi. BJ 427.2

Wannan lokacin ne aka ga cikar maganar Kristi zuwa ga ekklesiya a wannan lokacin, inda ya ce: “Ga magana da wannan ya fadi wanda yake mai-tsarki, shi wanda yake mai-gaskiya, wanda yake da makublin Dawuda, wanda ya bude, ba mai-rufewa, ya rufe, ba mai-budewa; na san ayukanka (ga shi, na sa kofa a gabanka budaddiya, wadda ba mai-rufewa)” Ruya 3:7,8. BJ 428.1

Masu bin Yesu ta wurin bangaskiya cikin babban aikin kafaran nan ne su ke samun moriyar tsakancinsa a madaddinsu, yayin da masu kin hasken da ke bayana wannan aikin ba sa cin moriyarsa. Yahudawa da suka ki hasken da aka bayar a zuwan Kristi na farko, suka kuma ki karban shi a matsayin Mai-ceton duniya, basu iya samun gafara ta wurinsa ba. Sa’anda Yesu, lokacin komawarsa sama ya shiga ta wurin jinin kansa cikin haikalin sama domin shi zuba ma al’majiransa alabrkun tsakancinsa, aka bar Yahudawa cikin bakar duhu suna ci gaba da hadayunsu da baye bayensu marasa anfani. Hidimar misalai da alamu ta kare. Kofan nan da da ake bi don zuwa wurin Allah an rufe shi. Yahudawan sun ki nemansa ta hanyar kadai da za su iya samunsa a wancan lokacin ta wurin hidima ta haikali na sama, sabo da haka ba su sami sadarwa da Allah ba. A garesu an rufe kofar. Ba su da sanin cewa Kristi ne ainihin hadaya, kuma shi ne kadai matsakanci a gaban Allah, sabo da haka ba su iya samun moriyar tsakancinsa ba. BJ 428.2

Yanayin Yahudawa marasa ba da gaskiyan nan yana misalta yanayin Kirista marasa ba da gaskiya ne, wadanda da gangan suka jahhilci aikin Babban Priest namu mai-jinkai. A hidimar alamu, sa’anda babban priest ya shiga wuri mafi tsarki, akan bukaci dukan Israila su taru a haikalin, cikin saduda kuma su kaskantar da kansu a gaban Allah, domin su karbi gafarar zunubansu, kada a yanke su daga taron jama’ar. Ashe kuwa wajibi ne gare mu a wannan Ranar kafara na ainihin mu fahimci aikin Babban Priest namu, mu kuma san aikin da ake bukata daga wurin mu. BJ 428.3

Mutane ba za su iya kin kashedin da Allah cikin jin kai Ya ba su, ba tare da sakamako ba. An aika da sako daga sama a zamanin Nuhu, kuma cetonsu ya dangana ga yadda suka yi da wannan sakon. Da shike sun ki gargadin, aka janye Ruhun Allah daga garesu, suka hallaka a ruwan ambaliyar. A zamanin Ibrahim mazamman Sodom sun dena samun jin kai, kuma dukansu, ban da Lot da matar sa da ‘ya’yan sa biyu suka kone cikin wutar da aka aika daga sama. Haka a zamanin Kristi ma. Dan Allah ya bayana ma Yahudawa marasa ba da gaskiya a cewa: “Ga shi am bar maku gidan ku kango.” Matta 23:38. Game da kwanakin karshe, Allah dayan Ya furta game da wadanda “ba su amsa kamnar gaskiya da za su tsira ba.” “sabili da wannan fa Allah yana aike masu da aikawar sabo har da za su gaskanta karya: domin a hukumta shari’a bisa dukan wadanda ba su gaskanta gaskiya ba, amma suka ji, dadin rashin adilchi.” Tasalunikawa II, 2:10-12. Yayin da su ke kin koyaswar Kalmarsa, Allah yana janye Ruhunsa, yana kuma barinsu ga rudun da suke so. BJ 429.1

Amma Kristi da yana tsakanci a madadin mutum, kuma za a ba da haske ga masu bidarsa. Ko da shike da farko Adventist ba su gane wannan ba, daga baya an bayana shi sa’anda suka fara gane nassosin da suka bayana ainihin matsayinsu. BJ 429.2

Bayan wucewar lokaci a 1844, wani lokaci na babban gwaji ga wadanda suka ci gaba da rike bangaskiyar zuwan Yesu ya biyo baya. Saukin su kadai, game da gane ainihin matsayinsu, shi ne haske da ya kai hankulansu haikali na sama. Wadansu suka janye bangaskiyarsu ga fassararsu ta annabcin lokaci, suka danganta tasirin Ruhu Mai-tsarki game da aikin, da akin Shaitan ko mutane. Wani sashe ya nace dai cewa Ubangiji ne ya bishesu can baya; kuma yayin da suka jira suna tsaro da addu’a don sanin nufin Allah, suka ga cewa Babban Priest na su Ya shiga wani aikin hidima ne, kuma da suka bi shi ta wurin bangaskiya, aka kuma nuna masu aikin karshe na ekklesiya. Suka sami karin ganewar sakon malaika na fari da na biyu, suka kuma kasance a shirye domin su karba su kuma ba duniya kashedin nan na malaika na uku na Ruya 14. BJ 429.3