Go to full page →

Babi na 11—Yardar ‘Ya’yan Sarkin BJ 195

Daya daga cikin shaida mafi kyau da aka taba bayarwa game da Canjin ita ce rashin yardar Kirista ‘ya’yan sarki na Jamus da suka nuna a Majalisar Spires a 1529. Karfin hali da bangaskiya da naciyar mutanen Allahn nan ya samo ma sararakin baya yancin tunani da na lamiri. Kin yardar su ya ba ekklesiyar da aka canja din suna masu kin yarda; kaidodinta su ne “ainihin kin yardan.” BJ 195.1

Rana mai duhu da barazana ya taho ma Canjin. Duk da dokar Worms din nan, wadda ta ce Luther mai ketare doka ne, ta kuma hana koyarwa ko yarda da koyaswarsa, yancin addini har yanzu ya ci gaba a kasar. Ikon Allah ya tsayar da ikokin da suka yi jayayya da gaskiyar. Charles V ya nace wai sai an murkushe Canjin, amma kullum ya daga hannunsa, akan tilasta shi ya fasa kai bugun. Akai akai kusantuwar hallakawar dukan wadanda suka yi jayayya da Rum ta dinga bayanuwa; amma daidai lokacin, mayakan Turkawa sukan bayana ta gabas, ko kuma sarkin Faransa, ko paparuma kansa, cike da kishi sabo da karuwan da girmar babban sarkin ke yi, ya yi yaki da shi; sabo da haka yayin da ake fama da tashe tashen hankulan al’ummai, an bar Canjin ya yi karfi, ya kuma yadu. BJ 195.2

Amma a karshe dai, shugabannin ‘yan paparuma sun rage fadace fadacensu, domin su hada hannu su fuskanci ‘yan canjin. Majalisar Spires a 1526 ta ba kowace jiha cikakken yanci game da harkokin addini har sai gamayyar majalisun ta yi zaman ta; amma da zaran damuwar da ta sa aka ba da ‘yancin nan ta wuce, babban sarkin ya kira taron Majalisa na biyu a Sires a 1529 da manufar murkushe ridda. Aka shirya lallabar ‘ya’yan sarki, cikin salama, in ya yiwu, domin su yi jayayya da Canjin; amma idan hakan bai yiwu ba, Charles ya shirya zai yi anfani da takobi. BJ 195.3

‘Yan paparuma fa sun ji dadin wannan. Suka taru a Spires da yawansu, a fili kuma suka bayana kiyayarsu ga yan Canjin da masu goyon bayansu. Melanchthon ya ce: “Mu ne tarkace da karmomin duniya; amma Kristi za Ya dubi mutanensa, zai kuma kiyaye su.” Aka hana ‘ya’yan sarki da suka halarci Majalisar baza bishara har a masaukinsu ma. Amma mutanen Spires sun ji kishin maganar Allah, kuma duk da hanawar, dubbai sun halarci taronni da aka rika yi a majami’ar mai-zaben Saxony. BJ 196.1

Wannan ya zaburar da hargitsin. Aka sanar da Majalisar cewa da shike kudurin da ya ba da yancin lamiri ya haifar da hargitsi mai-yawa, babban sarki ya bukaci cewa a soke shi. Wannan abu ya ta da fushin Kirista masu baza bishara. Wanin su ya ce: “Kristi Ya sake faduwa cikin hannun Kayafa da Bilatus kuma.” Yan ekklesiyar Rum fa suka kara nuna fin karfi. Waninsu mai matsanancin ra’ayi ya ce: “Turkawa sun fi Luthawa, domin Turkawa suna kiyaye ranakun azumi, Luthawa kuma suna ketare ranakun. Idan ya zama dole mu zaba tsakanin Littafin da kurkuran ekklesiya, ya kamata mu ki Littafin.” Melanchthon ya ce: “Kowace rana a taron dukan Majalisa, Faber yakan jefa sabon dutse a kan masu shelar bishara.” BJ 196.2

An kafa yancin addini bisa ga doka, jihohi masu baza bishara kuma sun dauki kudurin yin jayayya da ketarewar hakkokin su.luther, da shike har yanzu dai yana kalkashin takunkumin dokar Worms, baa barshi ya kasance a Spires ba; amma abokan famar sa sun cika gibin, gama Allah Ya shirya su domin su kare aikin Sa a wannan mawuyacin lokacin. Mmai-halin kirkin nan Fredrick na Saxony,wanda ya kare Luther a da, ya rigaya ya rasu; amma kanin sa John,wanda ya gaje shi, ya marabci Canjin da farin ciki,kuma ko da shike mai-son salama ne shi, ya nuna karfi da rashin tsoro kuma sosai game da duk ani day a shafi bangaskiyar. BJ 196.3

Priestoci suka bukaci jihohin da suka karbi Canjin su amince da mulkin Rum kawai. Yan Canji kuwa suka rike yancin da aka rigaya aka bayar. Basu yarda cewa Rum ta sake jawo jihhin nana da suka karbi maganar Allah kalkashin ikon tq akuma ba. BJ 197.1

Domin sasantawa, aka bad a shawara cewa inda yan Canjin basu rigaya sun kafu sosai ba, sai a aiwatar da dokar Worms da karfi, kuma “a wuraren da mutanen sun kauce ma canjin, da inda ba za su iyabin sa ba tare da tashin hankali ba, a takaice dai kada a yi sabon canji, kada su taba wani batu da ake musu akai , kada su kushe bukin mass, kada su yarda wani dan roman Katolika ya rungumi Luteranci.” Majalisar ta amince da wannan, priestocin paparuma kuwa suka gamsu. BJ 197.2

Da an aiwatar da dokan nan “dab a iya fadada Canjin ba...inda ba a san shi ba tukuna, ko kumama a kafa shi kan harsashe mai-karfi, inda da ma akwai shi.” Da an hana yancin magana kenan. Da ba a yarda da tuba ba. Wadannan takunkumi da dokokin ne fa aka so abokan Canjin su amince da su nan take.begen duniya ya nuna alamar bicewa. “Sake kafawar mulkin Rum...da ya dawo da cin mutunci irin na da;” kuma da an sami dammar kamala rushewar aikin da an rigaya an girgiza shi sosai ta wurin matsanancin ra’ai da sabani. BJ 197.3

Sa’an da masu bisharan suka taru don yin shawarwari, sun rika kallon juna da mamaki. Suka rika tambayan juna: “Me za mu yi?” manyan al’amuran da suka shafi duniya ne sun taso. Ko shugabannin Canjin za su mika wuya su karbi dokar? Yana da sauki a wanan babban hargitsin a iske cewa yan Canjin sun yi ta musu har suka daukikuduri na kuskure! Akwai kyawawan hujjoji da yawa da za su iya bayarwa donmika wuyar. An ba Lutherawa da ke yayan sarki yancin sun a addini. Aka mika kyauta dayan ga dukan mabiyan su wadanda kafin a yi dokar, sun rigaya sun karbi koyaswar Canjin. Ko bai kamata wannan ya ishe su ba? Ina yawan matsalolin da mika wuya zai hana! Ina yawan kasada da hargitsi da jayayya za ta jefa su ciki! Wa ya san zarfin da za a samu nan gaba? Bari mu rungumi salama; bari mu karbi tayin salama da Rum ke mika mana, mu kuwa rufe raunukan Jamus. Da irin ra’ayoyin nan ne yan Canjin suke iya anfani da su a matsayin hujjojin daukan matakin da lallai day a kai ga rushewar aikin su. BJ 197.4

“Abin farin ciki, suka dubi kaidar da aka kafa wannan tsari akai, suka kuma aikata cikin bangaskiya. Mene ne kaidar? ‘Yancin Rum ne ta tilasta lamiri, ta kuma hana ‘yancin bincike. Amma ko bai kamata su kan su da masu binsu ‘yan kin yarda su mori ‘yancin addini ba?” I kam, amma a matsayin lheri, bisa ga shirin kawai, amma ba ‘yanci ba. Sauran wadanda ba a ambata cikin shirin ba, ikon nan dai zai ci gaba da mulki kansu; babu zancen lamiri a kotu; Rum ce mai-sharia mara kuskure, kuma dole a yi mata biyayya. Da an amince da shirin, da ya zama an amince kenan cewa ‘yancin addini zai kasance a Saxony ne kadai; ga sauran Kirista kuma ‘yancin bincike da amincewa da sabuwar bangaskiya, da sun zama laifuka kenan, hukumcinsu kuwa kurkuku da kisa. Su za su yarda a kange yancin addini a wuri daya? a yi shela cewa kada wani ya sake amincewa da Canjin? cewa duk inda Rum ke iko yanzu ya zama nata har abada? Da ‘yan Canjin za su iya cewa ba su da laifi akan jinin dubban mutane wadanda sabo da wannan shirin da sun rasa rayukansu a hannun paparuma? Wannan da ya zama cin amanar aikin bishara da ‘yancin Kirista a wannan lokaci na musamman. Maimakon wannan suka gwammaci “sadakar da komi har jihohinsu ma, da rawaninsu, da rayukansu.” BJ 198.1

Yayan sarkin suka ce: “Mun ki wannan dokar. A sha’anin lamiri, masu rinjaye ba su da iko.” Wakilai suka ce: “Sabo da dokar 1526 ne kasar take morar zaman salama: soke shi zai cika Jamus da wahaloli da tsatsaguwa. Majalisar ba za ta iya yin komi ba sai dai ta kiyaye yancin addini, har sai babban majalisa ta yi zama.” Tsaron yancin addini aikin gwamanti ne, kuma iyakan ikon ta kenan game da sha’anin addini. Duk wani gwamnati da ya yi kokarin takurawa ko tabbatar da kiyaye addini ta wurin ikon ta, yana sadakar da kaidar da Krista masu baza bishara suka yi fama akai ke nan. BJ 199.1

‘Yan paparuman sun shirya danne abin da suka kira “Karin hali na taurin kai.” Sun fara da kokarin ta da rarrabuwa tsakanin magoya bayan Canjin ne, su kuma razana dukan wadanda suka goyi bayansu a fili. Wakilan yantattun jihohin suka gurbana a gaban Majalisar domin su amsa ko za su amince da sharuddan abin da ake niyyar yi. Suka nemi a ba su lokaci, amma a banza. Sa’anda aka gana da su, kusan rabinsu suka goyi bayan ‘yan Canjin. Wadanda suka ki sadakar da ‘yancin addini da ‘yancin zabi sun san wannan matakin ware su kenan don zargi da hukumci da zalunci nan gaba. Wani wakili ya ce: “Dole mu ki maganar Allah ko kuma a kone mu.” BJ 199.2

Sarki Ferdinand, wakilin babban sarkin kenan a Majalisar, ya ga cewa dokar za ta kawo rarrabbuwa soai, sai dai in sun lallashi ‘ya’yan sarkin suka amince da shi. Sabo da haka, ya gwada lallashi, ganin cewa gwada ma irin mutanen nan karfi zai kara taurara su ne kakwai. Ya “roki ‘ya’yan sarkin su amince da dokar, yana tabbatar masu cewa baban sarkin zai ji dadinsu sosai.” Amma amintattun nan sun yarda da ikon da ya fi na shugabannin duniya, suka kuma amsa a natse cewa: “Za mu yi biyayya da babban sarkin cikin komi da zai kara kawo salama da daukakar Allah.” BJ 199.3

A gaban majalisar, sarkin a karshe ya sanar ma mai-zaben da abokansa cewa dokar, “ba da jimawa ba za a zana ta a matsayin dokar babban sarki,” kuma cewa “abin da ya rage masu kawai shi ne su goyi bayan masu rinjaye.” Bayan wannan magnar sai ya fita daga wurin taron, bai ba ‘yan Canjin dammar shawara ko ba da amsa ba. “A banza suka aika a roki sarkin ya dawo.” Amsar da ya bayar it ace: “An gama da zancen nan; amincewa kadai ya rage.” BJ 200.1

Mutanen babban sarkin sun tabbatar cewa ‘ya’yan sarkin, Kiristan nan, za su manne ma Littafin, cewa ya fi koyaswoyin mutane da dokokinsu; kuma sun san cewa duk inda aka yarda da wannan kaidar, a karshe za a hambarar da tsarin paparuma. Amma kamar dubbai tun zamaninsu, “suka dubi ababan da ake gani kadai,” suka rudi kansu cewa manufar babban sarki da paparuma tana da karfi, na ‘yan Canji kuma ba ta da karfi. Da ‘yan Canjin sun dogara ga taimakon mutane ne kadai fa da sun zama marasa karfi, kamar yadda ‘yan paparuma suka dauka. Amma ko da shike ba su da yawa, kuma suna sabani da paparuma, sun kasance da karfinsu. Suka daukaka kara “daga rahotun Majalisar zuwa ga maganar Allah, kuma daga babban sarki Charles zuwa wurin Yesu Kristi, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayen giji.” BJ 200.2

Da shike Ferdinand ya ki kula abababn da lamirinsu ya amince da su, ‘ya’yan sarkin suka ki kulawa da tayinsa, amma suka kai kin amincewarsu gaban Majalisar kasa baki daya ba tare da jinkiri ba. Sabo da haka aka zana wani bayani aka gabatar ma Majalisar, cewa: BJ 200.3

“Mun nuna kin yarda, ta wurin rubutun nan, gaban Allah, Mahalicinmu, Makadaici, Mai-kiyayewa, Mai-ceto kuma, wanda kuma wata rana zai zama Mai-sahr’anta mu, da kuma gaban dukan mutane da dukan halita, cewa mu, domin mu kan mu da domin mutanenmu, bamu yarda ba, ba ma kuma kiyaye ta kowace hanya, dokar da ake so a kafa ba, cikin duk wani abin da ya saba ma Allah da maganarsa mai-tsarki, da lamirinmu da ceton rayukanmu.” BJ 200.4

“Mene! Mu amince da dokar! Muna furta cewa Allah Madaukakai yana kira ga mutum ya san Shi, duk da haka kuma mutumin nan ba zai iya sanin Allah ba!” “Ba wata tabbataciyar koyaswa sai wadda ta je daidai da maganar Allah.... Ubangiji Ya hana koyar da wata koyaswa dabam.... Wani nassi na Littafi ne yakan fassara wani.... Wannan littafin, game da duk abin da Kirista ke bukata, yana da saukin ganewa, kuma an shirya shi domin watsar da duhu. Mu mun kudurta, da alherin Allah, za mu ci gaba da wa’azin maganarsa mai-tsarki kamar yadda take a cikin littattafai na Tsoho da Sabon Alkawali, ba tare da kara wani abu akai da zai saba masa ba. Wannan maganar ce gaskiya kadai, it ace tabbataciyar magwajin dukan koyaswa da na dukan rayuwa, kuma ba za ta taba kasawa ko kuma ta rude mu ba. Wanda ya yi gini a kan wannan harsashe zai tsaya ya yi tsayayya da dukan ikokin lahira, yayin da dukan ababan banza na mutumyaka da aka shirya masa za su fadi a gaban fuskar Allah.” BJ 201.1

“Sabo da haka, mun ki karkiyar da aka tilasta a kanmu.” “A lokaci dayan kuma muna da tsammanin cewa mai-martaba babban sarki zai bi da mu, kamar yariman Kirista wanda ke kaunar Allah fiye da kowane abu, mun kuma bayana kanmu a shirye mu yi masa, da ya ku iyayengiji ma duka, soyayya da biyayya da suka cancanta.” BJ 201.2

Majalisar ta sami ganewa sosai. Yawancinsu suka cika da mamaki game da karfin halin masu kin dokar. Gaba ya zama masu da kamanin hargitsi da rashin tabbaci. Suka ga kamar dole kawai tsatsaguwa da hargitsi da zub da jini za su faru. Amma ‘yan Canjin, da shike sun tabbatar cewa suna da gaskiya, sun kuma dogara ga Mai-cikakken iko, suka “cika da karfin hali da naciya.” BJ 201.3

“Kaidodin da wannan kin yarda ya kunsa... su ne ainihin Kin yarda da ikon paparuma. Kin yardan nan yana jayayya da cin mutunci kashi biyu ne, game da sha’anin addini: na farko shi ne shisshigin majistare, na biyu kuma shi ne mulkin kama-karya na ekklesiya. Maimakon wadannan cin mutuncin, Kin yarda ya aza ikon lamiri bisa majistare, ikon maganar Allah kuma bisa ekklesiyar da ake gani. Da farko ma yana kin ikon kasa a cikin ababan ruhaniya, kuma kamar manzani da annabawa, yana cewa: ‘Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.’ A gaban renin Charles V, Kin yardan yana daukaka rawanin Yesu Kristi. Amma ya ci gaba: ya tsara kaidar cewa dole kowace koyaswar mutane ta kasance kalkashin hikimar Allah.” Masu Kin yardan sun kuma nanata ‘yancin su na furta abin da suka gaskata. Ba gaskatawa da aikatawa kadai za su yi ba, amma za su koyar da abin da maganar Allah ke koyarwa ma, suka kuma ki ‘yancin preist ko majistare ya sa baki. Kin yardan nan na Spires babbar sahida ce sabanin rashin hakuri na addini, da kuma bayana ra’ayin dukan mutane su yi sujada ga Allah bisa ga lamirinsu. BJ 201.4

An rigaya an yi furcin. Aka rubuta shi cikin tunanin dubbai, aka kuma yi rajistansa cikin littattafai na sama, inda duk kokarin mutum ba zai iya share shi ba. Dukan yan bisharan Jamus suka rungumi Kin yardar a matsayin bayyanawar bangaskiyar Jamus. Ko ina mutane suka ga yiwuwar sabon zamani mafi-kyau a cikin wannan furcin. Wani dan sarki ya ce ma masu Kin yarda na Spires: “Bari Madaukaki, wanda Ya ba ka alheri har ka furta da karfi ba takura, kuma ba tsoro, ya kiyaye ka cikin wannan karfin Kiristan, har rana ta har abada.” BJ 202.1

Da a ce Canjin, bayan ya fara cin nasara, ya yarda da hada kai da duniya don samun tagomashi a duniya, da ya yi ma Allah da shi canjin kan shi ma rashin aminci, ta haka kuma da ya tabbatar da rushewar shi. Abin da ya faru da ‘yan Canjin nan yana da darasi don dukan sararakin baya. Dabarar Shaitan don aiki sabanin Allah da maganarsa ba ta sake ba; har yanzu ba ya so a Littafi mai-bishewar rayuwa, kamar yadda bai so hakan ba a karni na sha shida. A zamaninmu, an rabu da koyaswoyin Littafin, kuma akwai bukatar komawa ga babban kaidan nan- Littafin da Littafin kadai, a matsayin kaidar imani da kaidar aiki kuma. Shaitan dai yana kan aiki ta kowace hanya don hallaka ‘yancin addini. Ikon antichrist da masu Kin kaidodin paparuma suka ki yana kokari kwarai yanzu don mayar da fifikon sa da ya rasa. Mannewa da aka yi ga maganar Allah shi ne kadai begen Canjin a yau. BJ 202.2

Alamun hatsari suka bayana ga masu aikin gyaran; an kuma ga alamu, cewa Allah Ya mika hannunsa domin Ya ceci amintattu. Wajen wannan lokacin ne “Melanchthon cikin gaggawa ya bi da abokin sa Simon Ggrynaeus ta titunan Spires zuwa kogin Rhine, ya matsa mashi ya ketare tekun. Abokin ya yi mamakin wannan gaggawar. ‘Tsohon mutum natsatse, ni kuma ban san shi ba,’” in ji Melanchthon, ‘ya bayana gare ni ya ce, Cikin minti daya Ferdinand zai aiki hafsoshin shari’a su zo su kama Grynaeus.’” Grynaeus, a karshe kuma ya yi masa fada wai don ya kare “wadansu kurakurai masu ban kyama.” “Faber ya boye fushinsa, amma jima kadan bayan wannan ya je wurin sarkin, wanda ya rigaya ya ba shi oda sabanin shehun mallamin nan na Heideberg, mai-taurin kai. Melanchthon bai yi sahkka ba cewa Allah ne Ya ceci abokinsa ta wurin aiko wani malaika mai-tsarki ya gargade shi. BJ 203.1

“Ya tsaya a gabar kogin Rhine, ba motsi har sai da ruwayen kogin suka ceci Grynaeus daga masu tsananta masa. Da ya gan shi a ketaren kogin, Melanchthon ya ce: ‘A karshe dai an fizge shi daga mukamukan wadanda ke kishin jinin mara laifi.’ Sa’anda ya koma gidansa aka fada ma Melanchthon cewa hafsoshi masu neman Grynaeus sun bincika gidan, sama da kasa.” An kudurta habaka Canjin a gaban shugabannin duniya ma. Sarki Ferdinand ya rigaya ya ki sauraron yayan sarki masu bishara; amma za a ba su zarafi su gabatar da maganarsu a gaban babban sarkin tare da manyan kasa da na ekklesiya. Don kwantar da fadace fadacen da suka addabi kasar, Charles V, shekara ta biye, bayan kin yarda na Spires, ya kira taron majalisa a Augsburg, inda ya sanar da niyyarsa ta shugabantar taron da kansa. Can aka kira shugabannin kin yardar. BJ 203.2

Manyan hadaruka sun yi ma Canjin barazana; amma magoya bayansa suka bar komi a hannun Allah, suka kuwa yi alkawalin yin aminci ga bisharar. Yan majalisar mai-zaben Saxony suka roke shi kada ya je Majalisar. Suka ce babban sarkin ya so yayan sarkin su je domin ya dana masu tarko ne. “Ko ba sa komi cikin kasada ne mutum ya je ya kulle kansa cikin ganuwar birni tare da magabci mai-iko ba?” Amma wadansu suka ce, “Bari ‘ya’yan sarkin su kame kansu cikin karfin zuciya, aikin Allah kuwa ya kubuta ke nan. Allah Mai-aminci ne, ba zai rabu da mu ba,” in ji Luther. Mai-zaben ya kama hanya, tare da masu rufe masa baya, zuwa Augsburg. Kowa ya san hatsarukan da ke fuskantarsa, da yawa kuma suka rika tafiya da duhun fuska da damuwar zuciya kuma. Amma Luther wanda ya bi su har Coburg, ya falkas da bangaskiyarsu ta wurin raira wakar da ya rubuta lokacin wannan tafiyar, wadda ke cewa, “Allahn mu Babban Hasumiya ne.” Tsoro mai-yawa ya waste, zukata da yawa masu nauyi suka warware sa’anda suka ji wakan nan. BJ 204.1

‘Ya’yan sarki, ‘yan canjin sun rigaya sun kudurta cewa za su shirya ra’ayoyinsu a jere a jere, tare da shaida daga Litafin, domin su gabatar ma Majalisar; aka kuma ba Luther aikin shirya ra’ayoyin, shi da Melanchthon, da abokansu. ‘Yan Kin yardan suka karbi furcin nan a matsayin bayanin bangaskiyarsu, suka kuma taru domin rattaba sunayen su kan takardar. Wannan mawuyacin lokaci ne. ‘Yan Canjin sun so kada a rikitar da maganarsu da zancen siyasa; sun so canjin ya yi tasirin da ya fito daga maganar Allah ne kawai. Sa’an da ‘ya’yan sarki Kirista din suka hallara don sa hannu kan Furcin nasu, Melanchthon ya ce: “Musamman tauhidi, da ya kamata ma’aikatan bishara ne su gabataar da ababan nan; mu kebe manyan kasa tukuna domin sauran al’amuran.” John na Saxony kuwa ya amsa cewa: “Allah Ya kiyaye ka hana ni. Na rigaya na kudurta yin abin da ke daidai, ba tare da damun kai na game da rawani na ba. Ina so in bayana Ubangiji. Hular sarauta ta, da matsayi, ba su da muhumminci gare ni kamr giciyen Yesu Kristi.” Bayan ya yi maganan nan sai ya rubuta sunansa. Wani dan sarkin kuma, sa’an da ya dauki alkalamin, ya ce: “Idan girman Ubangiji na Yesu Kristi yana bukataar wannan, ni ina shirye ... in bar dukiya ta da rai na a baya.” Ya ci gaba da cewa: “gwamma in sallamar da talakawa na da jihohi na, in bar kasar iyayena da sanda a hannu na, da in karbi wata koyaswa dabam da wannan takardar kuduri ta kunsa.” Irin bangaskiya da karfin mutanen Allahn nan kenan. BJ 204.2

Lokacin bayanuwa gaban babban sarkin ya zo, Charles V kan kujerar sarautarsa, ga masu zabe da ‘ya’yan sarki sun kewaye shi, ya saurari yan Canji masu kin yarda da paparuman. Aka karanta Kudurinsu. A wannan babbar taron aka bayana gaskiyar bishara sarai sarai, aka kuma bayana kurakuran ekklesiyar paparuma. “Shi ya sa aka kira wannan ranar, rana mafi-girma ta Canjin, kuma daya daga ranaku mafi-daraja a tarihin Kiristanci da na yan Adam.” BJ 205.1

Amma shekaru kalilan ne sun wuce, bayan Luther ya tsaya shi kadai a Worms a gaban majalisar kasa. Yanzu a madadin sa ga manyan yaran sarki na kasar, masu tarin iko. An hana Luther zuwa Augsburg, amma ya kasance a wurin, ta wurin maganar sa da addu’arsa. Ya rubuta cewa: “Ina cike da murna ganin cewa na rayu har wannan sa’a, inda aka daukaka Kristi a gaban jama’a ta bakin shahararru, masu shaida, kuma a gaban wannan taro mai daraja.” Ta haka aka cika abin da Littafin ya ce: “Ina kuwa furta shaidunka a gaban sarakuna.” Zabura 119:46. BJ 205.2

A zamanin Bulus hakanan ne aka kawo bisharan nan da aka kulle shi sabo da ita a gaban ‘ya’yan sarakuna, da fadawan babban birnin kasar. Sabo da haka a wannan lokaci, wannan abin da babban sarki ya hana wa’azi daga bagadi, an yi shelarsa daga fadar sarkin; abin da mutane da yawa sun ce bai cancanta ko bayi masu ji ba, iyayen kasar suka ji shi. Sarakuna da manyan mutane ne masu sauraro, ‘ya’yan sarakuna masu rawani kuma suka zama masu wa’azin, kuma wa’azin shi ne gaskiya na Allah. “Tun zamanin manzani ba a taba yin wani aikin da ya fi wannan ban girma, ko kudurin bangaskiya da ya fi wannan ban sha’awa ba,” in ji wani marubucin. BJ 206.1

Wani bishop, dan tsarin paparuma ya ce: “Duk abin da Luthawan suka fada gaskiya ce; ba za mu iya musunsu ba.” Wani kuma ya tambayi Dr. Eck, “Za ka iya karyata kudurin da mai-zabe da abokansa suka ambata?” Shi kuwa ya amsa: “Da rubuce rubucen manzani da annabawa kam, babu!, amma da rubuce rubucen ubani da na majalisu kuwa, i !” Mai-tambayan ya ce: “Na gane. Lutherawa a ganin ka suna cikin Littafin, mu kuma muna waje.” BJ 206.2

Wadansu yayan sarakunan Jamus suka karbi sabuwar gaskiyar. Babban sarkin kan sa ya furta cewa ababan da masu kin paparuman suka rubuta gaskiya ne. Aka juya kudurin zuwa harsuna da yawa, aka kuma baza su ko ina a Turai, kuma miliyoyi cikin sararakin baya sun karbe shi a matsayin shaidan bangaskiyarsu. BJ 206.3

Amintattun bayin Allah basu yi aikinsa ne kadai ba. Yayin da mulkoki da ikoki da masu ruhaniya na mugunta suka taru masu, Ubangiji bai kyale mutanensa ba. Da an bude idanunsu da sun ga shaidar kasancewar Allah da taimakonsa kamar yadda aka yi ma wani annabi na da. Sa’an da bawan Elisha ya nuna masa dakarun magabta da suka kewaye su, suka tare duk wata hanyar tsira, annabin ya yi addu’a cewa: “Ya Ubangiji, ina rokonka, ka Bude idanunsa domin shi gani.” Sarakuna II, 6:17. Sai ga shi, dutsen ya cika da karusai da dawakin wuta, dakarun sama ke nan da aka aiko domin su tsare mutumin Allah. Hakanan ne malaikun Allah suka tsare masu aikin Canjin nan. BJ 206.4

Wata kaidar da Luther ya rike ita ce cewa ba zai dogara ga ikon mutane don taimaka ma Canjin ba, kuma ba za a yi anfani da makamai don kare ta ba. Ya yi murna cewa ‘ya’yan sarakunan kasar sun karbi bisharar; amma sa’an da suka shawarta hada kai domin tsaro, ya ce: “Koyaswar bishara, Allah ne kadai zai kare ta.... Allah zai fi sa hannu a madadin aikin idan mutane basu yi ma aikin karambani ba. Kowace shawara da ta hada da siyasa, a ganinsa sanadin tsoro ne ba dalili, da rashin dangana kuma.” BJ 207.1

Sa’an da manyan magabta ke hada kai don hambarar da sabuwar bangaskiyar, aka kuma fito da dubban makamai domin yin fada da ita, Luther ya rubuta cewa: “Shaitan yana sa fushinsa; shugabannin ekklesiya marasa tsoron Allah suna hada kai; mu kuma ana mana barazanar yaki. A karfafa mutane su yi hamayya sosai a gaban Ubangiji, ta wurin bangaskiya da addu’a, domin magabtanmu, sa’an da Ruhun Allah Ya yi nasara kansu, su nemi salama. Babban bukatar mu addu’a ce; bari mutanen su san cewa yanzu suna bakin kaifin takobi da fushin Shaitan, su kuma yi addu’a.” BJ 207.2

Kuma bayan lokacin nan, game da zancen hadin bakin nan da ‘ya’yan sarakuna suka so a yi, Luther ya ce makamin kadai da za a yi anfani da shi a yakin nan shi ne “takobin Ruhu.” Ya rubuta ma mai-zaben Saxony cewa: “Bisa lamirinmu, ba za mu iya amincewa da hadin kai da ake tunanin yi ba. Za mu gwammaci mutuwa sau goma da mu ga bisharar mu ta jawo zubar da digo daya na jini.” Namu shi ne mu zama kamar ‘ya’yan raguna da ake kaiwa mayanka. Dole a dauki giciyen Kristi. Mai-girma, ka kasance da rashin tsoro. Ta wurin addu’o’inmu za mu yi ababan da suka fi abin da dukan magabtanmu za su yi ta wurin faharyar su. Kada dai hannunka ya zub da jinin yan-uwanka. Idan babban sarkin yana so a kai mu gaban shari’arsa, muna shirye mu bayana. Kai ba za ka iya kare bangaskiyarmu ba: ya kamata kowa ya ba da gaskiya amma ya san cewa kasada yake dauka.” BJ 207.3

Daga wurin addu’a a boye karfi ya zo wanda ya jijjiga duniya ta wurin babban Canji. Can fa bayin Allah a natse suka aza sawayensu bisa dutsen alkawuransa. Lokacin jayayyan nan a Augsburg, Luther “bai taba tsallaka rana guda ba, yana addu’a a kalla sa’a guda, kuma sa’o’in da suka fi dadin yin nazari kenan.” Daga dakinsa akan ji shi yana bude ma Allah zuciyarsa cikin kalmomi “cike da daukaka, da tsoro da bege kamar yadda mutum yakan yi magana da aboki.” Yakan ce: “Na san Kai ne Ubanmu, kuma za ka watsar da masu zaluntar ‘ya’yan ka, gama kai kanka ma kana cikin hatsari tare da mu. Dukan al’amarin nan naka ne, kuma bisa ga umurninka ne kadai muka sa hannu a ciki. Don haka, ka tsare mu ya Uba.” BJ 208.1

Zuwa ga Melanchthon, wanda nauyin taraddadi da tsoro ya danne shi, ya rubuta cewa: “Alheri da salama cikin Kristi - na ce cikin Kristi, kuma ba cikin duniya ba. Amin. Na ki jinin matsanantan damuwa da ke cinye ka. Idan abin da muke yi ba nagari ba ne, ka bar shi; idan nagari ne, don me za mu karyata alkawuran Shi wanda Ya umurce mu mu yi barci ba tsoro?... Kristi ba zai rabu da aikin adalci da gaskiya ba. Yana raye, yana mulki; tsoron me kuwa za mu ji?” BJ 208.2

Allah Ya saurari kukan bayinsa. Ya ba ‘ya’yan sarakuna alheri da karfin zuciya don rike gaskiyar, sabanin shugabannin duhu na duniyan nan. Ubangiji Ya ce: “Ga shi, ina sanya dutse magabaci na kusurwa zababe, mai-daraja, a cikin Sihiyona: wanda ya ba da gaskiya gare shi kuma ba za ya kumyata ba.” Bitrus I, 2:6. Yan Canji masu kin mulkin paparuma sun yi gini a kan Kristi, kuma kofofin lahira basu yi nasara kansu ba. BJ 208.3