Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 22—Cikawar Annabci

    Sa’anda lokacin da aka sa tsammani Ubangiji zai zo ya wuce - a bazarar 1844 - wadanda suka yi zaman bangaskiya don bayanuwarsa sun yi zaman shakka da rashin tabbaci. Yayin da duniya ta duaka cewa an ka da su, an kuma nuna cewa an rude su ne, abinda ya share masu hawaye shi ne maganar Allah din dai. Da yawa sun ci gaba suna nazarin Littafin, suna sake bincika shaidun bangaskiyarsu, suna kuma nazarin annabci a hankali don samun Karin haske. Shaidar Littafin da ta goyi bayan matsayinsu ta kasance a sarari, tabbataciya kuma. Allamu tabbatattu sun nuna cewa zuwan Kristi ya kusa. Albarkar Ubangiji, cikin tubar da masu zunubi da falkas da rayuwar ruhaniya cikin Kirista, ta nuna cewa sakon daga sama ne. Kuma ko da shike basu iya gane dalilin yankan burin su ba, sun tabbata cewa Allah ne ya bishe su kafin wannan lokacin.BJ 389.1

    Garwaye da annabce annabcen da suka dauka cewa sun shafi lokacin zuwan Kristi na biyu akwai magana da ya je daidai da yanayin rashin tabbacin su da jiran tsammanin su, wanda kuma ya karfafa su su jira da hakuri cikin bangaskiyar cewa abin da ya shiga masu duhu yanzu za a bayyana shi a daidai lokaci.BJ 389.2

    Cikin annabce annabcen akwai na Habakuk 2:1-4: “Zan tsaya wurin tsaro na, in tsaya a bisa hasumiya, in duba, in ga abinda za ya fada mani, da abinda zan amsa masa a kan karata. Ubangiji ya amsa mani, ya che, ka rubuta, ta fita a fili chikin alluna, domin mai-karantawa shi yi a guje. Gama ruyan har yanzu da ayanannen lokachinta, tana kwa gaggabta zuwa matukan, ba kwa za ta yi karya ba, ko ta jima, dakanta mata, gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba. Duba, ransa ya kumbura, ba daidai yake ba a chikinsa, amma adili ta wurin bangaskiyassa, za ya rayu.”BJ 390.1

    Tun 1842, umurnin da annabcin nan ya bayar, cewa “ka rubuta ru’yan ta fita a fili chikin al’uma, domin mai-karantawa shi yi a guje,” ya nuna ma Charles Fitch zancen shirya wata taswirar annabci da za ta bayana wahyin Daniel da Ruya. An dauka cewa wallafawar taswiran nan cikar annabcin Habakuk ne. Amma kuma ba wanda ya lura cewa annabci dayan ya nuna cewa za a sami jikiri kadan kafin a cika annabcin. Bayan yankan burin, muhimmancin nassin nan ya bayana: “Gama ru’yan har yanzu da ayanannen lokachinta, tana kwa gagabta zuwa matukan, ba kwa za ta yi karya ba, ko ta jima, dakanta mata, gama lallai za ta zo, baza ta yi jinkiri ba,… adali tawurin bangaskiyarsa za ya rayu.”BJ 390.2

    Wani sashin annabcin Ezekiel ma ya kasance abin karfafawa da ta’azantarwa ga masu bi. “Maganar Ubangiji kwa ta zo gareni chewa, Dan mutum, mi ne wannan karin magana da ku ke yi a kasar Israila, kuna chewa, kwanaki sun dade, kowache ru’ya kwa ta kan lalache? Ka fada masu fa, in ji Ubangiji Yahweh,… zan yi magana, magana da na fadi kwa za a chikata, ba za ta sake yin jinkiri ba.” “Mutanen gidan Israila suna cewa, Ru’ya da yake gani zanchen kwanakin gaba ne da nisa tukuna, yana annabcin zamani na nesa. Ka che masu fa, ga abinda Ubangiji Yahweh ya fadi, ba za a kara jinkirtadda maganata ba ko daya, amma magana da na fadi za ta chika, in ji Ubangiji Yahweh.” Ezekiel 12:21-25,27,28.BJ 390.3

    Masu jira suka yi farinciki, da sanin cewa shi wanda Ya san karshe daga farkon ya dubi dukan sararaki, da ya hangi cizon yatsan, sai ya ba su kalmomin na karfafawa da bege. Ba don irin nassosin nan da suka shawarce su su jira cikin hakuri su kuma rike amincewar su ga maganar Allah ba, da bangaskiyarsu ta kasa a lokacin gwajin nan.BJ 391.1

    Misalin budurwai goman nan na Matta 25 ma yana bayana abin da ya faru da ‘yan Adventist din. Cikin Matta 24, cikin amsa tambayar almajiran game da alamar zuwansa da na karshen duniya, Kristi ya bayaan wadansu al’amura mafi hunimmanci cikin tarihin duniya da na ekklesiyarsa, daga zuwan sa na farko har zuwansa na biyu; su ne, hallakawar Urushalima, babban kuncin ekklesiya kalkashin tsanantawan kafirai da na paparuma, duhuntawar rana da wata da kuma faduwar taurari. Bayan wannan, ya yi maganar zuwan mulkinsa, ya kuma ba da misalin bayi iri biyu da ke sauraron bayanuwarsa. Sura 25 ya fara da kalmomin nan: “Sa’an nan za a iske mulkin sama yana kama da budurwai goma.” A nan ana maganar ekklesiyar kwanakin karshe ne, wadda it ace aka ambata a karshen sura 24. A wannan misalin, an kwatanta yanayinsu da al’amuran aure na kasashen Gabas.BJ 391.2

    “Sa’an nan za a iske mulkin sama yana kama da budurwai goma, wadanda suka dauki fitillunsu, suka fita garin su tarbi ango. Biyar daga chikinsu marasa- azachi ne, biyar masu hikima ne. Gama marasa azanchin nan, da suka dauki fitillunsu, basu dauka duk da mai ba: amma masu-hikima suka dauki mai chikin santulansu tare da fitillunsu. Ana nan sa’anda ango ya yi jinkiri, dukansu suka yi rurrumi, suka yi barci. Amma da tsakiyar dare sai aka ji murya, Ga ango! Ku fito, ku tarbe shi.”BJ 391.3

    An gane cewa zuwan angon yana misalta zuwan nan na Kristi da malaika na fari ya sanar ne. Canje canje masu yawa da aka yi a kalkashin shelar kusantowar zuwansa sun je dai dai da tafiyar budurwai din ne. A wannan misalin, kaman na Matta 24, mutane kashi biyu aka misalta. Dukansu sun dauki fitillunsu, Littafin, kuma tawurin haskensa sun tafi domin su tarbi angon. Amma, yayinda “marasa azancbin nan, da suka dauki fitillunsu, basu dauka duk da mai ba,” “masu-hikima suka dauki mai chikin santulansu tare da fitillinsu.” Kashi na biyu din sun karbi alherin Allah, ikon sakewa mai-haskakawa na Ruhu Mai-tsarki, wanda ke mai da maganarsa fitilla ga sawaye, haske kuma ga tafarki. Cikin tsoron Allah sun yi nazarin Littafin domin su san gaskiyar, suka kuma nemi tsabtar ziciya da ta rayuwa. Sun sami dandano dan kansu, bangaskiya ga Allah da maganarsa, wadda yankan buri da jinkiri ba za su iya hambararwa ba. Wadansu suka “dauki fitillinsu, basu dauka duk da mai ba.” Ba cikin hankalinsu suka karbi sakon ba. Nauyin sakon ya ba su tsoro, amma kuma sun dogara ga bangaskiyar yanu-wansu ne, suka gamsu da yadda jikinsu ke ji kawai, ba tare da kwakwarar fahimtar gaskiyar ko ainihin aikin alheri cikin zuciyar ba. Wadannan sun fita domin su tarbi Ubangiji, cike da begen samun lada nan da nan, amma basu shirya domin jinkiri da yankan buri ba. Sa’anda jarabobi suka shigo, bangaskiyarsu ta kasa, haskensu kuma ya ragu.BJ 391.4

    “Sa’anda ango ya yi jinkiri, dukansu suka yi rurrumi, suka yi barci.” Jinkirin angon, yana misalta wucewar lokacin da aka yi tsammanin zuwan Ubangiji ne, da yakan burin da kuma jinkirin zuwan na sa. Cikin wannan lokaci na rashin tabbaci, sha’awar marasa zurfin bangaskiya ta fara kaduwa nan da nan, kokarinsu kuma ya ragu; amma wadanda bangaskiyarsu ta kafu bisa saninsu na Littafin ne suka kasance da kafafunsu a kan dutse wanda iskar yankan kauna ba ta iya kawarwa ba. “Dukansu suka yi rurrumi, suka yi barci,” wani bangare cikin rashin kulawa da kuma rabuwa da bangaskiyarsu, daya bangaren kuma tana jira cikin hakuri, har sai an ba da Karin haske. Duk da haka, cikin daren gwajin, masu hakurin ma kamar sun fara rasa bangaskiyar basu iya dogara ga bangaskiyar ‘yan-uwansu kuma ba. Dole kowa zai tsaya ko kuma ya fadi don kansa.BJ 392.1

    Wajen wannanlokacin, tsananin ra’ayi ya fara bayanuwa. Wadansu da suka ce sun karbi sakon da himma suka ki maganar Allah a matsayin sa na mai-bishewa shi kadai, mara kuskure, kuma da korafin samun bishewar Ruhu, suka mika kansu ga ikon tunanin kansu da ra’ayinsu, da ganin zuciyarsu. Akwai wadanda suka nuna makauniyar himma mara sassauci, suna sokar wadanda basu bi ra’ayin su ba. Babbar kungiyar Advenstist ba ta goyi bayan matsanantan ra’ayoyinsu da ayukansu ba.BJ 393.1

    Shaitan ya so ta wurin wannan hanyar ya ja da aikin Allah ya kuma rushe shi ne. Mutanen sun rigaya sun motsu sosai tawurin aikin koyaswar zuwan Kristi, dubban masu-zunubi sun rigaya sun tuba, amintattun mutane kuma suna ba da kansu ga aikin shelar gaskiyar, ko a lokacin jinkirin ma. Shaitan yana hasarar masu binsa, kuma don kawo reni ga aikin Allah, ya yi kokarin rudin wadansu da suka ce su masu bangaskiya ne ya kuma tura su zuwa makura. Wakilansa kuma suka shirya anfani da kowane kuskure da kowace kasawa, da kowane abin da bai dace ba, su kuma bayana shi a gaban mutane har da karin gishiri, domin a ki jinin Adventist da imaninsu. Ta hakanan idan ya sami karin yawan wadanda zai sa su ce sun ba da gaskiya ga zuwan Kristi na biyu, alhali shi Shaitan ne ke mulki bisa zukatansu, zai sami karin riba ta wurin jan hankula zuwa ga mutanen nasa cewa haka ne dukan masu ba da gaskiya su ke.BJ 393.2

    Shaitan ne “mai-zargin yan’uwan,” kuma ruhunsa ne ke motsa mutane su lura suna jira su ga kurakurai da kasawar mutanen Ubangiji, su kuma bayana su ga jama’a, yayin da ake kin ambaton kyawawan ayukansu. A kullum Shaitan yakan dinga aikin duk lokacin da Allah ke aikin ceton rayuka. Sa’anda ‘ya’yan Allah suka zo domin gabatarda kansu gaban Ubangiji, Shaitan ma yakan zo a tsakaninsu. A kowace falkaswa, yana shirye ne ya kawo wadanda ba a tsarkake zukatan su ba, kuma tunaninsu bai daidaita ba. Sa’anda wadannan suka karbi wadansu fannonin gaskiya, suka kuma karbu ga ainihin masu ba da gaskiyar, yakan yi aki tawurinsu don kawo ra’ayoyi da za su rudi marasa kulawa. Ba a tabbatar da cewa mutum Kirista ne na kwarai wai don ana ganin shi tare da ‘ya’yan Allah, ko a gidan sujada da wajen cin jibin Ubangiji ma. A kullum Shaitan yana wuraren ibada cikin kamanin wadanda zai iya anfani da su a matsayin wakilansa.BJ 393.3

    Sarkin mugunta yana jayayya kowane inci inda mutanen Allah suka ci gaba cikin tafiyarsu zuwa birni na sama. Cikin dukan tarihin ekklesiya ba wani canjin da aka taba gudanarwa ba tare da samun manyan matsaloli ba. Haka ya kasance a zamanin Bulus. Duk inda manzon ya kafa ekklesiya, akwai wadanda suka ce sun karbi gaskiyar, amma suka kawo ridda dabam dabam da in aka karba za su shanye gaskiyar ma a kwana a tashi. Luther ma ya gamu da rikici da wahala a hannun masu tsananin ra’ayi da suka ce wai Allah Ya yi magana kai tsaye tawurinsu, saboda haka kuma suka aza ra’ayoyinsu bisa shaidar Littafin. Da yawa marasa bangaskiya da kwarewa, amma masu gamsuwa da isarsu, kuma masu son ji da kuma fadin sabobin ababa, aka yaudare su tawurin karyar sabobin mallaman, suka kuma hada hannu da wakilan Shaitan cikin aikinsu na rushe abinda Allah ya motsa Luther ya gina. ‘Ya’yan Wesley kuma, da wadansu da suka albarkaci duniya da tasirinsu da bangaskiyarsu kuma, a kowane mataki sun gamu da dabarun Shaitan, inda ya rika tura masu-tsananin himma, marasa daidaituwa, marasa tsarki kuma, zuwa tsananin ra’ayi kowane iri.BJ 394.1

    William Miller bai goyi bayan halayyan da suka kai ga tsananin ra’ayin ba. Kamar Luther, ya ce ya kamata a gwada kowane ruhu da maganar Allah. Miller ya ce: “Iblis yana da iko mai-yawa kan zukatan wadansu yau. Kuma ta yaya za mu san irin ruhun da suke da shi? Littafin ya amsa: ‘Bisa ga ‘ya’yansu za ku sansanche su.’ Akwai ruhohi da yawa da suka shigo duniya, kuma an umurce mu mu gwada ruhohin. Ruhun da ba ya sa mu yin rayuwar natsuwa da adalci da tsoron Allah a duniya ta yanzu ba, ba Ruhun Kristi ba ne. Na kara hakikancewa akwai hannun Shaitan a cikin al’amuran nan na rashin natsuwa. Da yawa cikin masu karyan cewa an tsarkake su gaba daya suna bin al’adun mutane, kuma bisa dukan alamu, basu san gaskiyar ba, daidai da wadanda ba sa ikirarin nan din.” “Ruhun kuskure zai kau da mu daga gaskiya; Ruhun Allah kuma zai kai mu ga gaskiya. Amma, in ji ku, mutum zai iya kasancewa cikin kuskure amma ya ga kaman yana da gaskiya. Don me? Mun amsa: ‘Ruhun da maganar sun je daidai. Idan mutum ya gwada kansa ta wurin maganar Allah, ya kuma sami daidaituwa da dukan maganar, ashe kuwa dole ya ba da gaskiya cewa yana da gaskiyar; amma idan ya tarar cewa ruhun da ke bi da shi bai je daidai da dukan dokar Allah ko kuma Littafinsa ba, to sai shi yi taka-tsantsan ko da tarkon Iblis ya kama shi.” “Sau da yawa ni kan fi samun shaidar ibadata cikin zuciya a wurin masu tsoro da masu kuka da masu magana da kyar, fiye da yawan surutun nan a cikin Kirista.”BJ 394.2

    A kwanakin Canjin, magabta sun zargi ‘yan canjin da suka yi himman jayayya da tsananin ra’ayi da laifin jawo matsalolin matsanantan ra’ayin. Irin abin da masu jayayya da masu shelar zuwan Yesu na biyu suka yi ke nan su ma. Ban da kara gishiri ma kurakuran masu matsanancin ra’ayin, magabtan sun dinga baza rahotanin karya. Son kai da kiyaya ne kowa suka motsa mutanen nan. Shelar kusantowar Kristi ta girgiza salamarsu, sun ji tsoron cewa watakila gaskiya ne, suna kuma begen cewa ba gaskiyan ba ne, wannan ne kuwa asirin yakin da suka yi da Adventist da imaninsu.BJ 395.1

    Kasancewar masu matsanantan ra’ayin nan marasa yawa a cikin Adventist daidai yake da kasancewarsu masu rudu kuma cikin ekklesiya a zamanin Bulus da zamanin Luther, wannan kuma bai zama hujjar kushe aikinsu ba. Bari mutanen Allah su tashi daga barci su fara aikin tuba da canji, bari su bincika nassosin, su kuma koyi gaskiya wadda ke cikin Yesu, bari su kebe kansu dungum ga Allah, za a kuwa ga shaida cewa har yanzu Shaitan yana aiki, ba barci. Da kowane irin rudu, zai nuna ikonsa, yana anfani da dukan malaikunsa.BJ 396.1

    Ba shelar zuwan Yesu na biyu ne ya jawo matsanancin ra’ayi da kuma rabuwa ba. Wadannan sun bayana da daminan 1844 ne, lokacin da Adventist ke cikin yanayi na shakka da rudewa game da ainihin matsayinsu. Wa’azin sakon malaika fari da na kiran nan na tsakar dare ya danne matsanancin ra’ayi da tsatsaguwa. Wadanda suka yi aikin nan mai-saduda sun kasance cikin daidaituwa, zukatansu sun cika da kaunar juna da kuma Yesu, wanda suka yi begen ganinsa ba da jimawa ba. Bangaskiya dayan, bege mai-albarka dayan, sun daga su bisa mulkin kowane tasiri na mutum, suka kuma zama garkuwa daga haren haren Shaitan.BJ 396.2

    “Sa’an da ango ya yi jinkiri, dukansu sun yi rurrumi, suka yi barci. Amma da tsakiyar dare sai aka ji murya, Ga ango! Ku fito, ku tarbe shi. Sa’an nan dukan wadannan budurwai suka tashi, suka yi ta gyartan fitillinsu.” Matta 25:5-7. A daminar 1844 a tsakanin lokacin da aka fara tsammanin cewa kwana 2300 din za su kare, da kakar shekara dayan, lokacin da daga baya aka gane cewa kwana 2300 din sun kare, an yi shelar sakon ainihin kalmomin nassin: “Ga ango!”BJ 396.3

    Abin da ya jawo wannan aikin shi ne ganowar cewa a 457 BC ne umurnin Artaxerxes don maida Urushalima, ya fara aiki, wanda shine farawan kwana 2300 din nan, da kakan 457 BC din, ba a farkon shekaran ba yadda aka zata da farko. Idan aka kirga daga kaka na 457, shekaru 2300 din sun kare a kakan 1844 ne. BJ 396.4

    Ra’ayoyi da ke da tushe daga alamu na Tsohon Alkawali ma sun nuna cewa al’amarin da tsarkakewar haikakin ya misalta zai faru da kaka ne. Wannan ya bayana a sarari sa’anda aka mai da hankali ga yadda alamu game da zuwan Kristi na farko suka cika.BJ 397.1

    Yankan Dan ragon paskan misali ne na mutuwar Kristi. Bulus ya ce: “Gama an yanke paskarmu, watau Kristi.” Korinthiyawa I, 5:7. Damin nunan fari, wanda a lokacin paska akan mika a gaban Ubangiji, alama ce ta tashin Kristi. Bulus ya ce: “Kristi yayan fari; kana su da ken a Kristi, chikin zuwansa.” Korinthiyawa I, 15:23. Kamar damin da ake mikawa, wanda shi ne hatsin da ya fara nuna, wanda akan tara kafin girbi, Kristi ne nunan fari na cikin runbun Allah.BJ 397.2

    An cika alamun nan, ba game da al’amarin kadai ba, har da lokacin ma. Rana ta sha hudu ga watan daya na Yahudawa, daidai rana da watan da aka rika yanka Dan ragon Paskar har karni na goma sha biyar, Kristi, bayan Ya ci Paskar tare da alamajiransa, Ya kafa hidiman nan da zai zama abin tunawa da mutuwarsa, “Dan rago na Allah wanda yana dauke da zunubin duniya!” A wannan daren ne miyagu suka dauke Shi domin a kashe shi ta wurin giciyewa. Kuma kamar cikar misalin damin nan, an ta da Ubangijinmu daga matattu akan rana ta uku, nunan fari na wadanda ke barci, misalin dukan masu nagarta da za a tashe su daga matattu, wadanda za a canja jikunan kaskantarsu “domin ya yi kama da jikin darajassa.” Filibiyawa 3:21.BJ 397.3

    Hakanan kuma dole misalan da suka shafi zuwan Kristi na biyu za su cika daidai lokacin da aka ambata a hidimar misalan. A kalkashin tsarin Musa, tsarkakewar haikalin, ko kuma babban Ranar kafarar yakan faru ne a rana ta goma ga watan bakwai na Yahudawa (Leviticus 16:29-34). Saboda babban priest, bayan ya yi ma Israila kafara, ta haka kuma ya cire zunubansu daga haikalin, yakan fito ya yi ma mutanen albarka. Haka aka ba da gaskiya cewa Kristi, Babban Priest namu, zai bayana domin tsarkake duniya ta wurin hallaka zunubi da masu zunubi, ya kuma albarkaci masu jiransa da rashin mutuwa. Rana ta goma ga watan bakwai, rana mai girma ta kafara, lokacin tsarkakewar haikalin, wanda a 1844 ya fado daidaida ran ashirin da biyu ga Oktoba, aka dauka cewa lokacin zuwan Ubangiji ke nan. Wannan ya je daidai da tabbacin da aka rigaya aka samu cewa kwana 2300 din za su kare lokacin kaka ne.BJ 397.4

    Cikin misalin nan na Matta 25, zuwan angon ya biyo bayan lokacin jira da rurrumin ne. wannan ya je daidai da ra’ayoyin da aka bayana ne, daga annabci da kuma misali. Dubban mutane ne suka yi shelar kiran nan na “tsakiyar dare”.BJ 398.1

    Aikin ya mamaye kasar kamar ambaliya. Daga birni zuwa birni, kauye zuwa kauye, ya shiga kowane lungu har sai da mutanen Allah suka falka duka. Saboda wannan aikin, matsanancin ra’ayi ya watse kamar yadda raban takan watse in rana ta fito. Shakka da rudewar masu bada gaskiya suka kare, bege da karfin zuciya kuma suka cika zukatansu. Aikin ya yantu daga halayyan nan da kan faru sa’anda hankulan mutane sun motsu ba tare da tasirin maganar Allah da Ruhunsa ba. Kamar Israilawan da ne da sukan dawo wurin Ubangiji bayan bayinsa sun kai masu sakonin tsautawa. Aikin bai jawo murna mai-tsanani ba, sai dai zurfin binciken zukata da furta zunubi da rabuwa da duniya. Shiri don saduwa da Ubangiji ne ya dami mutanen. Akwai naciyar addu’a da kebewa dungum ga aikin Ubangiji. BJ 398.2

    Game da aikin, Miller ya ce: “Ba a nuna farinciki sosai ba,” an dakatar da wannan har sai nan gaba, sa’anda dukan sama da kasa za su yi murna da ta wuce misali, cike da daraja kuma. Babu ihu: wannan ma an bar ma ihun nan daga sama. Mawaka sun yi shuru: suna jira su hadu da rundunonin maliku; mawakan sama,… Babu sabanin ra’ayi; duka suna da zuciya daya da tunani daya.”BJ 399.1

    Wani wanda shi ma ya yi aikin ya shaida cewa: “Aikin ya haifar da binciken zuciya da kaskantar da kai a gaban Allah na sama. Ya jawo yayewar sha’awar ababan duniyan nan, da warkaswa daga jayayya da kiyayya, furtawar laifofi, tuba a gaban Allah, da addu’a na tuba da gaske a gabansa domin a sami gafara da karbuwa. Ya jawo kaskantar da kai da durkusawar ruhu, irin da ba mu taba gani ba. Kamar yadda Allah Ya umurta ta wurin Joel, sa’anda babbar rana ta Allah ta kusa, ta haifar da yagewar zukata ba na tufafi ba, da kuma juyawa ga Ubangiji da azumi da kuka da bakinciki kamar yadda Allah ya fada ta bakin Zechariah, an zubo da ruhun alheri da addu’a ma yayansa; suka dube Shi, Shi wanda, suka suke Shi, an yi babban bakinciki a kasar,… kuma wadanda ke neman Ubangiji suka kaskantar da kansu a gaban shi.”BJ 399.2

    Cikin dukan aikace aikacen addini tun zamanin manzanin, ba wanda ya fi na kakan 1844 din nan rashin harbuwa da kumamancin mutuntaka da dabarun Shaitan. Ko yanzu ma bayan shekaru da dama, dukan wadanda suka sa hannu cikin aikin nan suna kuma tsaye kan gaskiya suna jin tasiri mai-tsarki na aikin nan mai-tsarkin, suna kuma shaida cewa daga Allah ne.BJ 399.3

    Sa’anda aka kira: “Ga ango! Ku fito ku tarbe shi.” Masu jira “suka tashi, suka yi ta gyartan fitillunsu;” sun yi nazarin maganar Allah da himman da ba a taba ganin irin sa ba. An aiko maliku daga sama su falkas da wadanda suka fid da zuciya, su kuma shirya su su karbi sakon. Aikin bai dogara ga hikimar mutane ne da iyawar u ba, ya dogara ga ikon Allah ne. Ba mafi baiwa ba, mafi tawli’u da himma ne suka fara ji suka kuma yi biyayya ga kiran. Manoma suka bar hatsinsu a gona, makanikai suka bar kayan aikinsu, da hawaye da farinciki kuma suka fito don ba da gargadin. Wadanda da farko suka shugabanci aikin suna cikin na karshen shiga aikin. Ekklesiyoyin, a kalla, sun hana sakon shiga cikinsu, kuma yawancin wadanda suka karbe shi sun janye daga ekklesiyoyin. Cikin alherin Allah shelan nan ya hadu da sakon malaika na biyu ya kuma karfafa aikin.BJ 400.1

    Sakon nan, “Ango ya zo!” ba abin mahawara ba ne, da shike tabbacin daga Littafin a bayane yake. Ya zo da wani iko mai-karfi da ya motsa ruhu. Ba shakka ba tambaya. Lokacin shigowar Kristi Urushalima, mutanen da suka taru daga dukan sassan kasar don kiyaye bukin sun taru a Dutsen Zaitun, kuma yayin da suka sadu da jama’an da ke rufa ma Yesu baya sun sami motsuwar al’amarin, su ma suka ta da murya suna cewa: “Mai-albarka ne shi wanda ke zuwa chikin sunan Ubangiji!” Matta 21:9. Hakanan ne kuma marasa ba da gaskiya da suka rika halartar taron Adventist - wadansu don neman sanin abin da ke faruwa, ko don ba’a kawai - suka ji ikon da ke cikin sakon nan: “Ga ango!”BJ 400.2

    A lokacin akwai bangaskiya da ta kawo amsar addu’a, kamar yayyafi a kan busashiyar kasa, Ruhun alheri ya sauko bisa masu nema da himma. Wadanda suka yarda su tsaya fuska da fuska da Mai-fansarsu sun ji murna mai-saduda da ya fi gaban bayanawa. Ikon tausawa na Ruhu Mai-tsarki ya narkar da zuciya yayin da ake zubo da albarka a yalwace bisa amintattu.BJ 400.3

    A hankali cikin natsuwa wadanda suka karbi sakon sun kai lokacin da suka yi begen saduwa da Ubangijinsu. Kowace safiya sun dauka cewa aikinsu na farko shi ne neman tabbaci cewa Allah Ya karbe su. Zukatansu sun zama daya, suka rika addu’a tare, suna ma juna addu’a kuma. Sau da yawa sukan sadu don sadarwa da Allah, suna addu’a gare Shi a gona ko daji. Tabbacin karbuwa ga Mai-ceton ya fi masu abincinsu; kuma idan basu fahimci wani abu ba, basu huta ba har sai da suka fahimta. Yayin da suka ji tabbacin gafara, suka yi marmarin ganin Shi wanda suke kauna.BJ 401.1

    Amma yankan buri na jiran su har wayau. Lokacin da suke bege ya wuce. Mai-cetonsu kuma bai bayana ba. Sun yi begen zuwansa da dukan bangaskiya, yanzu kuma suka ji yadda Maryamu ta ji sa’anda bayan ta je kabarin Mai-ceton, ta tarar ba gawansa, ta yi ihu da kuka ta ce: “Sun dauki Ubangiji na, kuma ban san inda sun ajiye shi ba.” Yohanna 20:13BJ 401.2

    Da farko tsoron kada ya zamana cewa gaskiya ce sakon ya sa marasa ba da gaskiya, suka yi hankali. Bayan lokacin ya wuce, tsoron nan bai watse nan da nan ba; da farko basu iya yin murna kan yankan burin da ya sami masu bin ba, amma da shike ba a ga alamun fushin Allah ba, suka farfado daga tsoronsu, suka koma ga reninsu da ba’ansu. Da yawa da suka ce sun gaskata Ubangiji zai zo suka watsar da bangaskiyarsu. Wadansu da suka nuna tabbaci da farko, sun ji kunya sosai da yadda suka ji, kamar su gudu daga duniyar ma. Kamar Yunana suka yi ma Allah gunaguni suka gwammaci mutuwa maimakon rai. Wadanda da suka dangana bangaskiyarsu kan ra’ayin wadansu, ba maganar Allah ba, a yanzu suka so su kuma canja ra’ayinsu. Masu ba’a suka sha kan masu kumamanci da matsorata zuwa gefensu, dukansu kuma suka hada kai wajen shelar cewa ba dalilin tsoro ko bege kuma yanzu. Lokacin ya wuce, Ubangiji bai zo ba. Duniya kuma za ta iya kasancewa yadda take har dubban shakaru.BJ 401.3

    Masu ainihin bangaskiya sun rigaya sun sallamar da komi sabo da Kristi, suka kuma yi shelar kasancewarsa fiye da kowane lokaci. Sun gaskanta cewa sun rigaya sun ba duniya kashedi na karshe, kuma, da begen karbuwa ga Maigidansu da malaikun sama, sun riagaya sun janye daga tarayya da wadanda basu karbi sakon ba. Da murandi mai yawa suka yi addu’a cewa: “Ka zo Ubangiji Yesu, ka zo da sauri.” Amma bai zo ba. Yanzu kuma sun sake daukan nauyin matsalolin duniya da rudewarta, su kuma jimre ba’a da zage zagen marada, babban gwaji ne na bangaskiyarsu da hakurinsu.BJ 402.1

    Duk da haka cizon yatsan nan bai yi girma kaman wanda almajiran suka sha lokacin zuwan Kristi na farko ba. Sa’anda Yesu ya shiga Urushalima da nasara, masu binsa sun dauka cewa zai hau gadon sarautan Dauda ke nan, ya kubutar da Israila daga masu zaluntarta. Da bege mai-yawa suka rika gasar nuna daukaka ga sarkinsu. Da yawa suka shimfida tufafinsu a kan hanyan da yake takawa, ko kuma su baza ganyen dabino a gabansa. Cikin tsananin murnarsu suka ta da murya tare suna cewa: “Hossana ga Dan Dauda.” Sa’anda Farisawa cikin damuwa da haushin jin wannan murnar, suka ce ma Yesu ya tsauta ma almajiransa, Ya amsa Ya ce: “Da a che wadannan za su yi shuru, ko duwatsu za su yi murya.” Luka 19:40. Dole a cika annabci. Almajiran sun cika nufin Allah ne; duk da haka yankan buri yana gabansu. Amma kwanaki kalilan sun wuce bayan sun ga mutuwa mai-zafi na Mai-ceton, suka kuma shimfida Shi a kabarin. Ko burinsu daya bai cika ba, begensu kuma ya mutu tare da Yesu. Sai da Ubangijinsu ya fito daga kabari da nasara kafin suka gane cewa annabci ya rigaya ya ce haka zai faru, kuma “wajibi ne ga Kristi Ya sha wahala, ya tashi kuma daga matattu.” Ayukan 17:3.BJ 402.2

    Shekaru dari biyar kafin nan, Ubangiji ya rigaya ya bayana ta bakin annabi Zechariah cewa; “Ki yi murna sarai, ya diyar Sihiyona: ki yi sowa, ya diyar Urushalima, ga sarkin ki, yana zuwa wurinki; mai-adilchi ne shi, mai-nasara kwa; mai-tawali’u, haye a kan jaki, akan aholakin jaki.” Zechariah 9:9. Da almajiran sun gane cewa Kristi za shi wurin hukumci ne da wurin mutuwa kuma, da basu cika annabcin nan ba.BJ 403.1

    Hakanan ne kuma Miller da abokansa suka cika annabci suka kuma ba da sakon da annabci ya rigaya ya ce za a ba duniya, amma wanda da basu bayar ba, in da sun sami cikakkiyar ganewar annabcin da ya nuna cewa za su yi cizon yatsa, ya kuma ba da wani sakon da za a yi wa’azin sa ga dukan al’ummai kafin zuwan Ubangiji. An ba da sakon malaika na fari da na biyu din daidai lokaci, aka kuma cika aikin da Ubangiji Ya shirya aiwatarwa.BJ 403.2

    Duniya tana kallo, tana begen cewa idan lokacin ya wuce Kristi kuma bai bayana ba, za a yi watsi da dukan tsarin nan na Adventist. Amma yayin da mutane da yawa suka rabu da bangaskiyarsu, akwai wadanda suka tsaya da karfi; sakamakon aikin Adventist din, ruhun tawali’u da bimbini, ruhun rabuwa da duniya da sakewar rayuwa, wadanda aikin ya kunsa, ya nuna cewa aikin na Allah ne. Basu isa su yi musun cewa ikon Ruhu Mai-tsarki ya shaida wa’azin zuwan Kristi na biyu din ba, kuma basu iya ganin wani kuskure game da lissafin annabce anabacen wokatai ba. Manyan masu jayayya da su basu yi nasaran hambarar da tsarin su na fassara annabci ba. Basu yarda su rabu da ra’ayiyoyin da masanan da Ruhu ya motsa suka amince da su tawurin binciken Littafin cikin himma da addu’a ba, ra’ayoyin da suka jimre soke soken sanannun mallaman addini da masu hikima irin ta duniya, ra’ayoyin da kuma suka tsaya daram, duk da jayayyar masana da masu-iya magana, da kuma ba’a da zage zagen masu martaba da talakawa.BJ 403.3

    Gaskiya kam al’amarin da aka yi begensa bai faru ba, amma ko wannan ma bai jijjiga bangaskiyarsu ga maganar Allah ba. Lokacin da Yunana ya yi shela a titunan Nineveh cewa cikin kwana arba’in za a hallaka birnin, Ubangiji ya karbi kaskantar zuciyar mutanen Nineveh, ya kara masu lokacin gwaji, duk da haka Allah ne ya aika ma Yunana sakon, kuma bisa ga nufin Allah ne aka gwada Nineveh. Adventist sun gaskata cewa hakanan ne ma Allah ya kai su ga ba da gargadin hukumcin, suka ce: “sakon ya gwada zukatan dukan wadanda suka ji shi, ya kuma ta da sha’awar bayanuwar Ubangiji; ko kuma ya jawo kiyayya ga zuwan Ubangiji. Ya ja layi,… ta yadda wadanda ke so su gwada zukatan su su san ko da sun kasance a wane bangare ne, in da Ubangiji ya zo a lakacin, ko da sun yi ihu cewa: “Ga shi wannan Allahnmu ne; mun jirache shi, za ya cheche mu?”, ko kuma da sun kira duwatsu su fadi a kansu, su boye su daga fuskar Shi wanda ke zaune bisa kursiyin, daga fushin Dan ragon kuma? Ta hakanan Allah ya gwada mutanensa, Ya gwada bangaskiyarsu, ya gwada su, ya kuma ga ko za su janye a lokacin gwaji daga wurin da ya so ya ajiye su; ko kuma za su sallamar da duniyan nan, su kuma dogara ga maganar Allah kadai.”BJ 404.1

    William Miller ya bayana tunanin wadanda suka ba da gaskiya cewa Allah ne ya bi da su cikin abin da ya faru da su. Ya ce: “In da zan sake maimaita rayuwa ta kuma, da shaida dayan da na samu a lokacin tsakani na da Allah dole zanyi yadda na yi a lokacin can.” “Ina fata na tsarkake tufafi na daga jinin mutane. Ina ji kamar na yi iyakacin kokarina dai na wanke kaina daga duk wani alhakin laifinsu.” “Ko da shike an yanke mani buri sau biyu, ni ban karai ba, ban kuma yi sanyin gwiwa ba,… Bege na game da zuwan Kristi yana da karfi kamar kowane lokaci. Ni dai na yi abin da, bayan shakaru ina bimbini, na ga cewa ya zama wajibi ne gare ni in yi. Idan na yi kuskure, saboda kauna ne, kaunar yan’uwa na mutane da sanin cewa aikin Allah ni ke yi.” Abu daya da na sani shi ne cewa ban yi wa’azin komi ba sai na abin da na gaskata, Allah kuma yana tare da ni, ikonsa ya bayana a cikin aikin, an kuma sami anfani sosai.” “Ga ganin mutum, an sa dubbai sun yi nazarin Littafin ta wurin wa’azin lokacin; kuma ta hakanan, ta wurin bangaskiya da yayyafawar jinin Kristi, an sasanta su da Allah.” “Ban taba yi ma masu girman kai fadanci ba, ko kuma in ji tsoron fushin duniya ba. Yanzu kuma ba zan sayi soyayyarsu ba, ba kuwa zan bata lokaci na ina neman kiyayarsu ba. Ba zan taba neman rai na a hannunsu ba, ko kuma in ji shakkar rasa raina idan Allah cikin kaddararsa ya umurta hakan.”BJ 404.2

    Allah bai rabu da mutanensa ba; Ruhunsa ya ci gaba da kasancewa da wadanda basu ki hasken da sun rigaya sun samu suka kuma kushe aikin maganar zuwan Kristi din ba. Cikin wasika zuwa ga Ibraniyawa akwai kalmomi na karfafawa da fadaka ga masu jira da aka jarabace su a lokacin hargitsin nan. “Kada fa ku yasda gaba gadin ku, abin da ke da sakamako mai-girma. Gama kuna da bukatar hankuri, domin, bayan da kun aika nufin Allah, ku karbi alkawalin. Gama da sauran jimawa kadan, wanda ke zuwa za shi zo, ba kwa za shi yi jinkiri ba. Amma adilina da bangaskiya za shi rayu: idan kwa ya noke, raina ba shi jin dadinsa ba. Amma mu ba mu chikin masu-nokewa zuwa hallaka ba; amma chikin wadanda su ke da bangaskiya zuwa cheton rai.” Ibraniyawa 10:35-39.BJ 405.1

    Kalmomin da sun nuna kusatowar zuwan Ubangiji sun tabbatar da cewa ana ma ekklesiyar kwanakin karshe ne fadakan nan. Ya ce: “Gama da sauran jimawa kadan wanda ke zuwa za shi zo, ba kwa za shi yi jinkiri ba.” Ya kuma nuna a sarari cewa za a sami kamanin dakatawa, kuma za a ga kamar Ubangiji Ya yi jinkiri ne. Umurnin da aka bayar a nan ya je daidai da abin da ya faru da Adventist a wannan lokacin. Mutanen da ake magana da su a nan suna fuskantar yiwuwar rushe bangaskiyarsu. Sun bi nufin Allah tawurin bin bishewar Ruhu Mai-tsarki da maganarsa; duk da haka basu iya gane nufinsa a abin da ya faru da su ba, basu kuma gane hanyar da ke gabansu ba, suka so su yi shakka ma ko Allah ne yake bishe su. A lokacin nan kalmomin na cewa, “Amma adili na da bangaskiya ne za shi rayu.” Sun je daidai. Da shike hasken kiran tsakiyar daren nan ya haskaka hanyarsu, suka kuma ga an bayana annabcin, kuma alamun da ke cika da wuri wuri suna nuna cewa zuwan Kristi Ya yi kusa, sun yi tafiya bisa ga ganin ido ne a lokacin. Amma yanzu, da shike begensu bai cika ba, za su tsaya tawurin bangaskiya ga Allah da maganarsa ne kadai. Masu ba’a sun rika cewa: “An rude ku.” Amma maganar Allah ta ce: “Idan kwa ya noke, raina ba shi jin dadinsa ba.” Idan suka shika bangaskiyarsu yanzu, suka kuma musunci ikon Ruhu Ma-tsarki wanda Ya kasance tare da sakon, wannan zai zama ja da baya ne zuwa hallaka. Kalmomin Bulus, sun karfafa su, cewa: “Kada fa ku yas da gaba gadin ku.” “Kuna da bukatar hankuri,” “Gama da sauran jimawa kadan, wanda ke zuwa za shi zo, ba kwa za shi yi jinkiri ba.” Abin da ya fi anfani gare su shi ne su kaunaci hasken da sun rigaya sun karba daga wurin Allah, su rike alkawuransa, su kuma ci gaba da nazarin Littafin, su kuma yi hakuri su jira, suna tsaro don karban Karin haske.BJ 406.1

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents