Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 39—Kwanakin Wahala

    “A wannan lokacin fa Micahel za ya tashi tsaye, shi babban sarki mai-kariyar jama’arka; za a yi kwanakin wahala irin da ba a taba yi ba tun da aka yi al’umma har loton nan; a loton nan kwa za a chechi mutanenka, kowane daya wanda aka iske shi a rubuche chikin litafin.” Daniel 12:1.BJ 609.1

    Sa’anda sakon malaika na ukun ya rufe, babu sauran alheri kuma domin mazamnan duniya. Mutanen Allah sun kamala aikinsu. Sun rigaya sun karbi ruwan karshe, “wartsakewa daga wurin Ubangiji,” kuma su na shirye domin lokacin gwaji da ke gabansu. Malaiku su na kai da kawowa da hanzari a cikin sama. Wani malaika da ya dawo daga duniya ya sanar da cewa aikin sa ya kare; an rigaya an yi ma duniya gwaji na karshe, kuma dukan wadanda suka nuna cewa su na biyayya ga dokokin Allah sun rigaya sun karbi hatimin Allah Mai-rai. Sa’an nan Yesu zai dena tsakancin Sa a haikali na sama. Za ya daga hannuwansa, da babban murya kuma zai ce: “An gama,” dukan rundunan malaiku kuma za su ajiye rawaninsu yayin da zai yi sanarwan nan mai-nauyi cewa: “Wanda shi ke mara-adilchi, bari shi yi ta rashin adiklchi: wanda shi ke mai-kazanta kuma, a kara kazamtadda shi: wanda shi ke mai-adilchi kuma, bari shi yi ta adilchi: wanda shi ke mara tsarki kuma, a kara tsarkake shi.” Ruya 22: 11. An rigaya an yanka hukuncin rai ko mutuwa game da kowane mai-rai. Kristi Ya rigaya Ya yi kafara domin mutanensa, Ya kuma shafe zunubansu. Adadin talakawansa ya cika; mulkin da ikon da girman mulkin kalkashin dukan sama an kusa a ba da shi ga magadan ceto, Yesu kuma zai yi mulki a matsayin Shi na Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayen giji.BJ 609.2

    Sa’an da Ya bar haikalin, duhu zai rufe mazamnan duniya. A wannan lokaci na ban tsoro, dole masu adalci su kasance a idon Alah Mai-tsaarki, babu matsakanci. An cire hanin da ke kan miyagu, Shaitan kuma ya na da cikaken iko kan wadanda a karshe dai sun zama marasa tuba. Tsawon jimrewan Allah ya kare. Duniya ta ki jinkansa, ta rena kaunarsa, ta kuma tattake dokarsa. Miyagu sun zarce kadadar gafararsu; a karshe an janye Ruhun Allah da suka dinga ki. Da shike ba su da kariyar alherin Allah, ba su da tsaro ke nan daga mugun. Sa’annan Shaitan zai jefa mazamnan duniya cikin wata wahala babba ta karshe. Sa’an da malaikun Allah sun dena tsayar da ikokin fushi mai-tsanani, za a sake dukan fannonin tashin hankali. Dukan duniya za ta shiga cikin hallaka da ta fi wadda ta fada ma Urushalima ta da muni. BJ 610.1

    Malaika daya ne ya hallaka dukan ‘ya’yan farin Masarawa ya kuma cika kasar da makoki. Lokacin da Dawuda ya yi ma Allah laifi ta wurin lissafta jama’a, malaika daya ne ya kawo hallakan da aka hori Dawudan da ita. Ikon hallakan nan da malaiku masu tsarki suka yi anfani da shi sa’an da Allah Ya umurce su, shi ne miyagu za su yi anfani da shi idan Allah Ya yarda masu. Akwai ikoki da ke shirye yanzu, su na jiran izinin Allah ne kawai, su mai da ko ina kango.BJ 610.2

    An zargi masu girmama dokar Allah da jawo ma duniya matsaloli, za a kuma zarge su da cewa su ne sanadin masifu da za su abko ma halitta da tashin hankali da zub da jini da ke cika duniya da kaito. Ikon da ke tattare da gargadi na karshen ya fusata miyagu: suna fushi da dukan wadanda suka karbi sakon, Shaitan kuma zai kara zuga ruhun kiyayya da zalunci.BJ 610.3

    Sa’an da a karshe dai aka janye kasancewar Allah daga al’aummar Yahudawa, prietoci da mutane basu sani ba. Ko da shike suna kalkashin mulkin Shaitan, kuma cikin zafin fushi mai-munin gaske, duk da haka sun dauka cewa su zababbu na Allah ne. Hidima ta ci gaba a cikin haikalin; an ci gaba da mika hadayu a kan kazamtattun bagadinta, kowace rana kuma an dinga rokon albarkar Allah kan mutanen nan da ke da laifin jinin Dan Allah a kansu, suna kuma so su kashe ‘yan hidimansa da manzaninsa. Sabo da haka, sa’an da aka bayana hukumcin da ke kan haikalin, kuma kadadar duniya ta tabbata har abada, mazamnan duniya ba za su sani ba. Mutanen da an rigaya an janye Ruhun Allah daga wurinsu a karshe, za su ci gaba da surar addini, kuma himmar mugunta da sarkin muguntan zai motsa su da ita don cim ma miyagun kulle kullensa, za su dauki kamanin himma domin Allah.BJ 611.1

    Da shike Assabbat ya zama muhimmin batun jayayya tsakanin Kirista ko ina, kuma hukumomin addini da na kasa sun hada kai domin kiyaye Lahadi, naciyar wata karamar kungiya ta marasa rinjaye wajen kin amincewa da masu rinjayen zai mai da su abin zagin dukan duniya. Za a koyar da cewa marasa yawan nan da ke jayayya da abin da ekklesiya ta kafa da kuma dokar kasa, bai kamata a yi hakuri da su ba; ya fi kyau su din su wahala da a jefa al’ummomi dungum cikin rikici da rashin bin doka. Shekaru dubu da dari takwas da suka gabata, shugabannin sun yi irin maganan nan game da Kristi. Kayafa ya ce: “Yana da anfani a gare ku mutum daya shi mutu saba da jama’a, kada al’umma duka ta lalace.” Yohanna 11:50. Za a amince da wannan maganar, daga baya kuma za a kafa doka game da masu tsarkake Assabbat na doka ta hudu, a zarge su da cewa sun cancanci horo mafi tsanani, a kuma ba mutane dama bayan wani lokaci, su kashe su. Romanci a Tsohuwar Duniya da ridda cikin Kin ikon paparuma a Sabuwar Duniya za su dauki mataki dayan game da masu girmama dukan dokokin Allah.BJ 611.2

    Sa’an nan za a jefa mutanen Allah cikin al’amuran nan na fitina da wahala da annabi ya kira lokacin wahalar Yakub. “Gama haka Ubangiji Ya fadi: mun ji murya ta rawan jiki, ta tsoro ba ta lafiya ba che.... Dukan fuskoki fa sun komo fari. Kaito! gama wannan rana mai-girma che, har babu kamatta: lokachin wahalar Yakub ke nan; amma za a cheche shi daga chiki.” Irmiya 30:5-7.BJ 612.1

    Daren azabar Yakub, sa’an da ya yi kokuawa cikin addu’a domin kubuta daga hannun Isuwa (Farawa 32:24-30) ya na misalta abin da zai faru da mutanen Allah a lokacin wahala ne. Sabo da yaudaran da ya yi domin samun albakar ubansa, wadda kuwa ta Isuwa ce, Yakub ya gudu domin ransa, barazanar dan’uwansa ta razana shi. Bayan shekaru da dama na zaman korarre, ya kama hanya, bisa umurnin Allah, domin shi dawo tare da matansa da ‘ya’yansa, da garkunan dabbobinsa, zuwa kasarsa ta gado. Daga isowa kasar, ya cika da tsoro sabo da zuwan Isuwa da mayaka domin daukan fansa. Da alama Yakub da jama’ar a za su fuskanci gwada karfi da kuma kisa ke nan. Ban da taraddadi da tsoro, ga kuma zargin kansa, (tsarguwa) da shike zunubin shi ne ya jawo wannan hatsarin. Begen shi kadai jin kan Allah ne; dole addu’a ce kadai tsaronsa. Duk da haka ya yi iyakar kokarinsa don yin kafara domin laifin da ya yi ma dan-uwansa, ya kuma kawar da barazanar. Haka ya kamata masu bin Kristi su yi iyakar kokari su sa kansu cikin hasken da ya dace a gaban mutane domin su kawar da kiyayya da hatsarin da ke barazana ga ‘yancin lamiri.BJ 612.2

    Bayan ya tara iyalin sa, domin kada su ga wahalarsa, yakub ya kasance shi kadai domin ya roki Allah. Ya furta zunubinsa, ya kuma yi godiya sabo da jin kan Allah gare shi yayin da cikin tawali’u mai-zurfi ya ambaci alkawalin da aka yi da ubaninsa da alkawuran da aka yi masa cikin wahayinsa a Babel da kuma cikin kasa hijirarsa. Lokacin matukar tarzomar rayuwarsa ta zo. Cikin duhu da kadaici, ya ci gaba da addu’a da kaskantar da kansa a gaban Allah. Faraf daya, wani hannu ya dafe kafadarsa. Ya dauka wani magabci ne ke neman ransa, kuma da dukan karfinsa ya yi kokuwa da wanda ya dafe shi. Sa’an da gari ya fara wayewa, bakon ya fito da ikonsa da ya fi na mutum, kuma da ya taba shi, sai Yakub mai-karfin nan kamar ya gurgunce, sai kuma ya fadi, babu taimako, yana kuka da roko a wuyar mai kokuwa da shi. Yanzu Yakub ya gane cewa malaikan alkawalin ne ya ke kokuwa da shi. Ko da shike ya gurgunce, ya na kuma fama da matukar azaba, bai rabu da aniyarsa ba, ya dade yana jimre rudami da nadama da wahala sabo da zunubinsa; yanzu dole a tabbatar masa cewa an gafarta masa. Bakon nan daga wurin Allah Ya kusa ya tafi; amma Yakub ya manne masa yana rokon albarka. Malaikan ya ce: “Ka bar ni in tafi, gama gari yana wayewa;” amma Yakub ya ce: “Ba zan bar ka ba, sai ka yi mani albarka.” Wannan shi ne rashin tsoro da naciya da jimrewa. Da Yakub ya yi fahariya ne ko tsageranci, da nan da nan an hallaka shi; amma nashi tabbaci ne na wanda ya furta kumamancinsa da rashin cancantarsa, amma don haka ya amince da jin kan Allah Mai-cika alkawali.BJ 612.3

    “Ya yi iko bisa malaikan, ya rinjaye shi.” Hosea 12:4. Ta wurin kaskantarwa da tuba da mika kai, mai-zunubin nan, mai-kuskure, mai-mutuwa, ya rinjaya da Sarkin sama. Ya rigaya ya manna begensa ga alkawuran Allah, kuma zuciyar Kauna Mara-iyaka ba ta iya koran rokon mai-zunubin ba. Domin shaidar nasararsa da karfafawa ga wadansu, domin su bi kwatancinsa, a ka sake sunansa daga wanda ke tunurwa da zunubinsa zuwa wanda ya kan sa a tuna da nasararsa. Kuma rinjayar da Yakub ya yi da Allah tabbaci ne cewa zai rinjaya da mutane. Bai sake jin tsoron saduwa da fushin dan-uwansa ba, da shike Ubangiji ne tsaronsa.BJ 613.1

    Da Shaitan ya rigaya ya zargi Yakub a gaban malaikun Allah, yana cewa yana da ‘yanci ya hallaka shi sabo da zunubinsa; ya motsa Isuwa ya kai masa hari; kuma a daren kokowar Yakub din nan, Shaitan ya yi kokarin danne shi da tunanin laifinsa domin shi sanyaya masa gwiwa, shi karya masa dogararsa ga Allah. Yakub ya kusan fid da zuciya; amma ya san cewa idan babu taimako daga sama, zai hallaka. Ya rigaya ya tuba da gaske daga zunubinsa, ya kuma roki jinkan Allah. Bai bar manufarsa ba, amma ya manne ma Malaikan, ya kuma dinga add’uarsa da naciya, tare da kuka mai-zafi har sai da ya yi nasara.BJ 614.1

    Kamar yadda Shaitan ya zuga Isuwa ya kai ma Yakub hari, hakanan zai zuga miyagu su hallaka mutanen Allaha lokacin wahala. Kuma yadda ya zargi Yakub, haka ne zai zargi mutanen Allah. Yana gani kamar dukan duniya talakawansa ne, amma karamar kungiyan nan da ke kiyaye dokokin Allah suna kin mulkinsa. Da zai shafe su daga duniya da nasararsa za ta cika. Ya ga cewa malaiku masu-tsarki suna tsaronsu, ya kuma gane cewa an gafarta zunubbansu; amma bai san cewa an rigaya an kamala sahri’ar su a haikali na sama ba. Yana da cikakken sanin zunuban da ya jarabce su suka aikata, kuma yana gabatar da su a gaban Allah da karin gishiri ainun, ya na cewa su ma sun cancaci a hana su alherin Allah daidai da yadda aka hana shi. Yana cewa bisa adalci Ubangiji ba zai iya gafara zunubansu, sa’an nan Ya hallaka shi da malaikunsa ba. Yana kuma cewa su nasa ne, kuma ya kamata a ba shi su ya hallaka su.BJ 614.2

    Yayin da Shaitan ke zagin mutanen Allah sabo da zunubansu, Ubangiji yana barin shi Ya jarabce su matuka. Za a gwada amincewarsu ga Allah da bangaskiyarsu da naciyarsu kuma. Yayin da suke tuna baya, zukatansu su kan yi sanyi, domin a dukan rayuwarsu, ba nagarta da yawa. Suna da cikakken sanin rashin cancantarsu da kumamancinsu. Shaitan zai yi kokarin razana su da cewa wai ba su da bege, kuma ba za a taba wanke abin kazantarsu ba. Ta wurin wannan ya na begen lalata bangaskiyarsu domin su yarda da jarabobinsa, su kuma juya daga biyayyarsu ga Allah.BJ 614.3

    Ko da shike magabta masu son hallaka mutanen Allah za su kewaye su, duk da haka tsoron zalunci sabo da gaskiya ba shi ne ukuban da za su sha ba; suna tsoro ne cewa ba a tuba daga kowane zunubi ba, kuma cewa ta wurin wani laifinsu, za su kasa samun cikawar alkawalin Mai-ceton, cewa: “Ni ma zan kiyaye ka daga sa’ar jaraba, wannan da ke zuwa bisa dukan duniya.” Ruya 3:10. Da za su sami tabbacin gafara, da ba za su ji tsoron azaba ko mutuwa ba; amma idan basu cancanta ba, har suka rasa rayukansu sabo da aibin halayensu, wannan zai jawo reni ga sunan Allah.BJ 615.1

    A kowane gefe suna jin shirye shiryen tawaye da tashin hankali; kuma a cikin zukatansu akwai bege da buri sosai na cewa riddan nan ta kare, muguntar miyagu kuma ta kare. Amma yayin da suke rokon Allah Ya tsayar da tawaye, suna zargin kansu kwarai cewa su kansu ba su da ikon tsayayya da mugunta da kuma rage karuwarta. Suna ji kamar da kullum sun dinga anfani da dukan iyawarsu don hidimar Kristi, su na ci gaba da kokarinsu, da mayakan Shaitan ba su da iko sosai da za su dawama a kansu. BJ 615.2

    Za su azabtar da kansu a gaban Allah, suna nuna tubarsu daga zunubansu, suna kuma rokon alkawalin Mai-ceton cewa: “Bari shi kama karfi na, domin shi yi amana da ni.” Ishaya 27:5. Bangaskiyarsu ba ta da fadi ba wai don ba a amsa addu’o’insu nan da nan ba. Ko da shike su na fama da masananan taraddadi da razana da wahala ba za su dena addu’o’insu ba. Za su rike karfin Allah yadda Yakub ya rike Malaikan, kuma maganar rayukansu ita ce: “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka yi mani albarka.” BJ 615.3

    Da Yakub bai rigaya ya tuba daga zunuubinsa na samun gado ta wurin yaudara ba, da Allah bai ji addu’arsa Ya kuma kiyaye ransa ta wurin jinkai ba. Hakanan a lokacin wahala, idan mutanen Allah sun tuna da zunuban da basu furta ba, yayin da suke fama da tsoro da ukuba, da za a fi karfinsu; rashin bege zai yanke bangaskiyarsu, kuma ba za su sami karfin zuciya da za su roki Allah Ya kubutar da su ba. Amma yayin da suke da kyakyawar sanin rashin isarsu, ba su da boyayyun zunubai da za su bayana. Zunubansu sun rigaya sun fuskanci hukumci an kuma shafe su, kuma ba za su iya kawo su a tuna da su ba. BJ 616.1

    Shaitan yana sa mutane da yawa su gaskata cewa Allah zai manta da rashin amincinsu game da kananan al’amuran rayuwa; amma Ubangiji yana nunawa cikin huldarsa da Yakub cewa ba zai taba amincewa ko kuma ya kyale mugunta ba. Dukan wadanda sun yi kokarin boye zunubansu ko kuma ba da hujja dominsu, suka kuma bar zunuban sun kasance a littattafan sama, ba su furta ba, ba a kuma gafarta su ba, Shaitan zai yi nasara bisan su. Yawan furcin bangaskiyansu da yawan darajar matsayin da su ke rike daidai yake da yawan fushin Allah game da laifinsu, da yawan farin cikin Shaitan babban magabcinsu. Masu jinkirta shiryawa don ranar Allah ba za su iya samun shirin a ranar wahala ba ko kuma wata rana daga baya. Dukan irin wadannan ba su da bege.BJ 616.2

    Kiristan da za su shiga ba shiri cikin yakin karshen nan mai-ban tsoro, cikin rashin bege za su furta zunubansu cikin kalmomi na azaba, yayin da miyagu za su yi murna game da wahalarsu. Furcin zunuban nan irin na Isuwa da Yahuda ne. Masu fadin zunuban suna bakincikin sakamakon zunuban su ne, amma ba laifin kansa ba. Ba sa jin tuba ta gaskiya, basa kyamar mugunta, suna amincewa da zunuban su, ta wurin tsoron horo; amma kamar Fir’auna na da, za su koma tumbensu ga Allah da zaran an kawar da horon.BJ 616.3

    Tarihin Yakub tabbaci ne kuma cewa Allah ba zai jefar da wadanda aka rude su, aka jarabce su, aka kuma yashe su zuwa cikin zunubi ba, idan sun dawo wurinsa da tuba ta gaskiya. Yayin da Shaitan ke kokarin hallaka wadannan, Allah zai aiko da malaikunsa, su tsare su, su ta’azanar da su a lokacin hadari. Hare haren Shaitan masu tsanani ne da himma kuma, rudinsa mumuna ne; amma idon Ubangiji yana kan mutanensa, kunnensa kuma yana sauraron kukarsu. Azabarsu mai-yawa ce, wutar tanderun kuma ta kusa ta cinye su; amma mai-tsarkakewan zai fito da su kamar zinariya da aka tsarkake da wuta; dole a cinye son duniyansu, domin a nuna halin Kristi cikakke.BJ 617.1

    Lokacin wahala da ukuba da ke gabanmu zai bukaci bangaskiya da za ta jimre gajiya da jinkiri da yunwa, bangaskiya da ba za ta kare ba ko da an jarabce ta sosai. An ba kowa lokacin gwajin hali domin a shirya don wancan lokacin. Yakub ya dawama domin ya yi naciya da himma ne. Nasararsa shaida ce ta ikon addu’a da naciya, dukan wadanda za su kama alkawuran Allah yadda shi ya yi, su kuma yi himma da naciya yadda ya yi, za su yi nasara ma yadda shi ya yi. Wadanda ba sa so su yi musun kai, su yi kuka a Allah, su dade suna addu’a da naciya don albarkarsa, baza su same ta ba. Wadanda suka san kokowa da Allah ba su da yawa! Nawa suka taba sa rayukansu sun bi Allah da himmar bukata har sai an mika kowace gabar jikin? Sa’anda rashin bege ya yi yawa ta yadda harshe ba zai iya ambatawa ba game da mai-addu’ar, mutum nawa ne sukan nace da bangaskiya ga alkawuran Allah?BJ 617.2

    Masu kankantar bangaskiya yanzu, suna kalkashin babban hatsarin faduwa kalkashin ikon rudin Shaitan da dokan da za ta tilasta lamiri. Ko da sun jimre gwajin ma, za su kara nutsewa cikin wahala da ukuba ne lokacin wahala, da shike basu taba sabawa da dogara ga Allah ba. Zai zama masu dole su koya cikin matsi da sanyin gwiwa, darussan nan na bangaskiya da suka kyale.BJ 618.1

    Ya kamata mu fahimci Allah yanzu ta wurin gwada alkawuransa. Malaiku suna rubuta kowace addu’a ta naciya da gaskiya. Gara mu rabu da muradun kanmu da mu manta sadarwa da Allah. Talauci mafi zurfi, musun kai mafi girma, tare da yardar Allah, ya fi arziki da girmamawa da holewa da abota ba tare da yardar Allah ba. Dole mu sami lokaci mu yi addu’a. Idan mun bar zukatanmu sun shaku da ababan duniya, Ubangiji zai iya ba mu lokaci ta wurin cire mana gumakanmu na zinariya da gidaje da gonaki masu anfani. BJ 618.2

    Matasa ba za su jarabtu da zunubi ba idan sun ki shi ta duk wata hanya, sai dai wadda a ciki za su iya rokon albarkar Allah. Idan ‘yan sakon da ke kai sakon gargadi na karshe ga duniya za su roki albarkar Allah, ba yamusai cikin kiwuya da rashin kuzari ba, amma da himma, cikin bangaskiya yadda Yakub ya yi, za su sami wurare da yawa inda zasu iya cewa: “Na ga Allah ido da ido, rai na kuma ya wanzu.” Farawa 32: 30. Sama za ta lissafta su a matsayin ‘ya’yan sarakuna, masu ikon yin nasara da Allah da kuma mutane. BJ 618.3

    Lokacin wahala “irin da ba a taba yi ba,” ba da jimawa ba zai zo mana; kuma za mu bukaci kwarewan da ba mu da shi yanzu, wanda kuma da yawa sabo da yawan kiwuya ba za su samu ba. Sau da yawa wahala takan yi yawa a zato, fiye da zahiri; amma ba haka yake game da hargitsin da ke gabanmu ba. Komi yawan bayani ba za a iya nuna girman matsalar ba. A wancan lokacin gwajin, ole kowane mai-rai ya tsaya ma kan sa a gaban Allah. “Ko da a ce Nuhu, Daniel, da Ayuba suna cikinta [kasar], na rantse da raina, in ji Ubangiji Yahweh, ba za su chechi ko da ko daya ba, ransu kadai za su cheta ta wurin adilchinsu.” Ezekiel 14:20. BJ 618.4

    Yanzu, yayin da Babban Priest na mu yake yin kafara domin mu, ya kamata mu bidi zama cikakku cikin Kristi. Ko ta wurin tunani ma ba a iya sa Mai-ceton ya amince da ikon jaraba ba. Shaitan yakan sami wani wuri da zai rike ne a cikin zukatan mutane inda zai sa kafa; ko ana sha’awar wani zunubi wanda ta wurinsa jarabobinsa za su nuna ikon su. Amma Kristi Ya ce: “Sarkin duniya yana zuwa, ba shi da komi a chikina.” Yohanna 14:30. Shaitan bai iya samun wani abu a cikin Dan Allah ba da zai ba shi dammar yin nasara. Ya kiyaye dokokin Ubansa, kuma ba zunubi a cikinsa da Shaitan zai yi anfani da shi ya cuce Shi. Yanayin da dole a iske ga wadanda za su tsaya a kwanakin wahala ke nan.BJ 619.1

    A rayuwan nan ne za mu rabu da zunuubi, ta wurin bagaskiya cikin jinin kafara na Kristi. Mai-cetonmu yana gayyatar mu, mu hada kanmu da shi, mu hada kumamancinmu da karfinsa, jahilcinmu da hikimarsa, rashin isanmu da isarsa. Kadarar Allah ce makaranta, inda zamu koyi tawali’u da kaskantar da kai irin an Yesu. Ubangiji kullum yana nuna mana ainihin manufofin rayuwa ne, ba hanyar da muka zaba da ta fi kamar sauki da dadi gare mu ba. Ya rage namu mu hada kai da hanyoyin da Allah ke anfani da su cikin aikin sifanta haalayenmu daidai da gurbin sama. Ba wanda zai kyale aikin nan ko kuma ya dakatar da shi, ba tare da fuskantar hatsari mafi ban tsoro ga ransa ba.BJ 619.2

    Manzo Yohanna cikin ruya ya ji babbar murya a sama tana cewa: “Kaiton duniya da teku: domin Shaitan ya sabko wajenku, hasala mai-girma kwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kadan ne.” Ruya 12:12. Al’amuran da suka jawo wannan magana daga sama suna da ban tsoro. Fushin Shaita zai karu sa’an da ya ga lokacinsa yana karewa, kuma aikinsa na rudi da hallaka zai kai makuransa a kwanakin wahala ne.BJ 619.3

    Ba da jimawa ba za a bayana ababa masu ban tsoro a sammai, alamar ikon aljannu na aikata al’ajibai. Ruhohin aljannu za su shiga zukatan sarakunan duniya da cikin dukan duniya kuma, domin a rike su cikin rudi, a kuma zuga su su hada kai da Shaitan cikin fadan shi na karshe da gwamnatin sama. Ta wurin wadannan wakilan, za a rudi shugabanni da talakawa. Mutane za su taso suna karyan cewa su ne Kristi kansa, su kuma bidi suna, da sujada wadanda duka ‘yanci ne an Mai-fansarmu. Za su aikata al’ajibai na warkarwa, za su kuma ce suna da ruyai daga sama da ke sabani da shaidar Littafin.BJ 620.1

    A matsayin rudi mafi-girma, Shaitan kan shi zai ce shi ne Kristi. Ekklesiya ta dade tana cewa tana sauraron zuwan Mai-ceton a matsayin babban begenta. Yanzu babban mai-rudin zai sa a ga kamar Kristi Ya zo. A bangarorin duniya dabam dabam, Shaitan zai nuna kansa ga mutane kamar halitta mai-martaba da walkiya, kamar da Dan Allah yadda Yohanna ya bayana Shi cikin Ruya 1:13-15. Darajar da ta kewaye shi ta fi duk wadda idon dan Adam ya taba gani. Kuwwar nasara za ta cika wuri cewa: “Kristi Ya zo! Kristi Ya zo!” mutane za su durkusa a gabansa cikin bangirma, shi kuma zai daga hannuwansa, ya furta albarka a kansu, yadda Kristi Ya albarkaci almajiransa lokacin da yana duniya. Muryarsa tana da taushi, mai-dadin ji kuwa. Cikin amo cike da ladabi da tausayi zai gabatar da wadansu gaskiyan nan na sama da Mai-ceton ya furta; zai warkar da cututtuka, sa’an nan da kamanin halin Kristi, zai ce ya canja Assabbat zuwa Lahadi, ya kuma umurci kowa ya tsarkake ranan da shi ya yi mata albarka. Zai bayana cewa masu naciyar kiyaye rana ta bakwai da tsarki su na sabon sunansa ne ta wurin kin jin malaikunsa da ya aika da haske da gaskiya kuma. Rudi mai-karfi, maikusan tilastawa ke nan. Kamar Samriyawan da Simon Magus ya rude su, jama’a, daga mafi-kankanta zuwa mafi-girma, za su saurari bokancin nan, su na cewa: “Wannan shi ne ikon Allah.” Ayukan 8:10.BJ 620.2

    Amma ba za a yaudari mutanen Allah ba, koyaswoyin jabun Kristin nan basu je daidai da Littafin ba. Zai sa albarkarsa kan masu sujada ga bisan da gumkinsa ne, ainihin wadanda Littafin ya ce za a zuba fushin Allah wanda ba a surka ba a kansu. BJ 621.1

    Bugu da kari kuma, ba a yarda ma Shaitan ya yi kwaikwayon irin zuwan da Kristi zai yi ba. Mai-ceton Ya rigaya Ya gargadi mutanensa kan rudi game da wannan batun, Ya kuma bayana yadda zuwansa na biyu zai kasance. “Gama masu karyan Kristi za su tashi, da masu karyan annabchi, za su gwada alamu masu-girma da al’ajibai kuma; har su badda ko zababbu da kansu, da ya yiwu.... Idan fa sun che maku, Ga shi yana chikin jeji; kada ku fita: ko kwa, Ga shi yana chikin lolokai; kada ku gaskanta. Gama kamar yadda walkiya takan fito daga gabas, ana kwa ganinta har yamma; hakanan bayyanuwar Dan mutum za ta zama.” Matta 24:24-27,31; Ruya 1:7; Tassalunikawa I, 4:16, 17. Ba za a iya yin jabun wannan zuwan ba. Ko ina za a sani, dukan duniya za ta shaida shi.BJ 621.2

    Wadanda da ma suna nazarin Littafin a natse, suka kuma karbi kaunar gaskiya ne kadai za a kare su daga kakarfan rudin da zai kama duniya. Ta wurin shaidar Littafin, masu binciken za su gane mai-rudin cikin sojan gonan na shi. Lokacin gwajin zai zo ma kowa. Ta wurin rairayar jarabobi za a bayana ainihin Kirista. Ko mutanen Allah yanzu sun kafu sosai cikin maganarsa ta yadda ba za su bi tunanin kansu ba ne? Ko a cikin wannan tashin hankalin za su manne ma Littafin da Littafin kadai ne? Shaitan, in ya yiwu, zai hana su shiryawa domin su tsaya a wannan ranar. Zai tsara al’amura ta yadda zai yi masu shinge, ya dabaibaye su da dukiyar duniya, ya sa su dauki kaya mai-nauyi da gajiyarwa, domin zukatansu su cika da damuwoyin rayuwan nan, har ranar gwaji ta zo masu kamar barawo. BJ 621.3

    Sa’an da dokan da shugabannin kashen Kirista dabam dabam za su bayar sabanin masu kiyaye dokokin Allah za ta janye tsaron gwamnati, ta bar su da wadanda ke so su hallaka su, mutanen Allah za su gudu daga birane da kauyuka, su hada kai a kungiyoyi, su na zama a wuraren da suka fi kadaici da kasancewa kango. Da yawa za su sami mafaka a kogunan duwatsu ne. Kamar Kiristan Kwarin Piedmont, za su mai da madaukakan wurare na duniya mafakansu, za su kuma gode ma Allah sabo da karfafan wurare na duwatsun, Ishaya 33: 16. Amma da yawa daga dukan al’ummai da dukan sassa, manya da kanana, mawadata da matalauta, bakake da farare, za a jefa su cikin muguwar bauta mafi rashin adalci. Kaunatattu na Allah za su yi kwanakin wahala, a daure da sarkoki, a kulle cikin kurkuku, da hukumcin kisa a kansu, wadansu kuma an bar su su mutu da yunwa cikin kurkuku masu duhu da ban kyama. Ba wanda ke jin kukansu; ba mutumin da ke shirye ya taimake su. BJ 622.1

    Ko Ubangiji zai manta da mutanensa a wannan lokacin jaraba? Ko Ya manta da Nuhu lokacin da aka hori duniyar zamaninsa? Ko Ya manta da Lot lokacin da wuta ta sauko daga sama ta cinye biranen Sodom da Gomorrah? Ko Ya manta da Yusufu a tsakiyar masu bautar gumaka a Masar? Ko Ya manta da Iliya lokacin da rantsuwar Jezebel ta yi masa barazana da abin da ya faru da annabawan Baal? Ko Ya manta da Irmiya a cikin kurukun sa na ramin nan mai-ban kyama? Ko Ya manta da jarumawan nan uku a cikin tanderun wuta? Ko kuma Daniel a cikin ramin zakuna?BJ 622.2

    “Sihiyona ta che, Ubangiji Ya yashe ni, Ubangiji Ya manta da ni kuma. Ya yiwu mache ta manta da danta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin dan chikinta ba? I, ya yiwu wadannan su manta amma ni ba ni manta da ke ba. Ga shi na zana ki a tafin hannu na” isahya 49:14-16. “Shi wanda ya taba ku, ya taba kwayar idonsa.” Zechariah 2:8. BJ 622.3

    Ko da shike magabta za su jefa su cikin kurkuku, duk da haka wannan ba zai yanke sadarwa tsakaninsu da Kristi ba. Wani wanda ke ganin kowane kumamancinsu, wanda Ya san kowane gwaji, Ya fi dukan ikokin duniya; malaiku kuma za su zo wurinsu cikin kurkukun, su ba su haske da salama daga sama. Kurkukun zai zama kamar fadar sarki, gama masu arzikin bnagaskiya su na zama a wurin, kuma za a haskaka wurin da hasken sama, yadda aka yi sa’anda Bulus da Sila su ka yi addu’a da wakokin yabo da tsakar dare cikin kurkukun Filibbi. BJ 623.1

    Hukumcin Allah zai abka kan masu neman danne mutanen Allah da hallaka su kuma. Tsawon hakurinsa da miyagu yana kara karfafa su cikin zunubansu, amma duk da haka horonsu tabbatace ne mai-tsanani kuma da shike ya yi jinkiri da yawa. “Gama Ubangiji za ya tashi kamar chikin dutsen Perazim, za ya hasala kamar yadda Ya yi chikin kwarin Gibeon; domin Shi yi aikinsa; aikinsa mai-ban al’ajibi, ya tabbatasda al’ajibinsa mai-ban al’ajibi.” Ga Allahnmu Mai-jinkai, horo abin al’ajibi ne. “In ji Ubangiji Yahweh, Na rantse da raina, ba ni da wani jin dadi chikin mutuwar mugu ba.” Ezekiel 33: 11. “Ubangiji yana chike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jin kai da gaskiya;... yana gafarta laifi da sabo da zunubi.” Duk da haka, “ba shi kubutadda mai-laifi ko kadan.” “Ubangiji mai-jinkirin fushi ne, mai-girma ne chikin iko, ba kwa za shi kubutadda masu laifi ba ko kadan.” Fitowa 34:6,7; Nahum 1:3. Ta wurin manyan al’amura, cikin adalci zai kunita ikon dokarsa da aka tattake. Zafin horon da ke jiran mai-laifi zai bayana ta wurin jinkirin Ubangiji wajen aiwatar da hukumcin. Al’amman da ya dade yana yi mata hakuri, wadda kuma ba zai buga ta ba har sai ta cika ma’aunin zunubinta a lissafin Allah, a karshe za ta sha kokon fushin da ba a surka da jinkai ba.BJ 623.2

    Sa’an da Kristi Ya dena tsakancinsa a haikalin, za a zubo fushin nan da ba a surka bad a za azuba ma wadanda suke sujada ga bisan da gumkinsa suka kuma karbi lambansa (Ruya 14:9, 10). Annoban Masar, a lokacin da Allah Ya kusa kubutar da Israila, sun yi kama da wadannan annoba mafi-muni da fadi da za su fado ma duniya gaf da kubutarwar mutanen Allah. In ji mai-ruyan, game da annoban nan, ya ce: “Sai ya zama mugun gyambo mai-azaba bisa mutane wadanda su ke da shaidar bisan, masu sujada ga gumkinsa kuma.” Teku ya zama jini irin na matachen mutum: kowane abu mai-rai “ya mutu kwa, watau abin da ke chikin teku.” Kuma “koguna da mabulbulan ruwaye ...ya zama jini kuma.” Duk da munin annoban nan, adalcin Allah ya kunita. Malaikan Allah ya ce: “Mai-adilchi ne kai, .... domin ka hukumta hakanan: gama su suka zubasda jinin tsarkaka da annabawa, jini kuma ka ba su su sha: wannan ya dache da su.” Ruya 16:2-6. Ta wurin hukumta mutanen Allah zuwa mutuwa, da gaske sun ja ma kansu laifin jinin na su kamar da hannunsu ne suka zubar da jinin. Hakanan ne kuma Kristi Ya ce Yahudawan zamaninsa ke da alhakin dukan jinin tsarkaka da aka zubar tun kwanakin Habila, da shike suna da ruhu iri dayan, sun kuma so su yi aiki iri dayan da masu kisan annabawan nan.BJ 623.3

    Cikin annoban da ke biye an ba rana iko “ta babbake mutane da wuta. Har mutane suka babbake domin tsananin zafi.” Aya 8, 9. Annabawan sun bayana yanayin duniya a wannan lokaci na bantsoro kamar haka: “Kasa tana makoki, gama an banzantadda hatsi.... Dukan itatuwan gona sun bushe: gama farinchiki ya yi yaushi a zuchiyar yan Adam.” “Iri ya ruba a kalkashin hoggan; an lalatadda rumbuna.... Ji dai nishin dabbobi! Garkunan shanu sun damu, domin babu wurin kiwo. Rafufukan ruwa sun kafe, wuta kwa ta chinye makiyaya na jeji.” “Raira wakoki na haikali kuma za su zama kururuwa a chikin ranan nan, in ji Ubangiji Yahweh: gawaye za su yi yawa; a kowane wuri kwa za a zubas da su a shuru.” Joel 1:10-12, 17-20; Amos 8:3.BJ 624.1

    Annoban nan ba za su mamaye duniya ko ina ba, in ba haka ba da mazamnan duniya za su hallaka gaba daya. Duk da haka za su zama annoba mafi-muni da ‘yan Adam suka taba gani. Dukan annoban da mutane suka fuskanta kafin rufewar gafara akan surka su da jin kai. Jinin Kristi yakan tsare mai-zunubi daga karban cikakken mudun laifinsa, amma a hukumci na karshe, za a zubo fushi da ba a surka da jin kai ba.BJ 624.2

    A wancan ranar, jama’a da yawa za su yi marmarin mafakar jin kan Allah wanda sun dade suna ki. “Ga shi, in ji Ubangiji Yahweh, kwanaki suna zuwa inda zan aike yunwa a chikin kasan, ba yunwan gurasa ko kishin ruwa ba, amma na jin magnar Ubangiji. Za su kama yawo daga teku zuwa teku, daga arewa zuwa gabas; za su yi gudu nan da can garin neman magnar Ubangiji amma ba za su samu ba.” Amos 8:11, 12.BJ 625.1

    Mutanen Allah ba za su rasa shan wahala ba; amma yayin da ake tsananta masu, ana wahal da su, yayin da suke jimre rashi, suna wahalar abinci kuma, ba za a bar su su hallaka ba. Allahn nan da Ya lura da Iliya ba zai kyale daya daga ‘ya’yansa masu sadakar da kai ba. Shi wanda yake lissafta suman kansu zai lura da su, kuma a lokacin yunwa za a kosar da su. Yayin da miyagu ke mutuwa da yunwa da annoba, malaiku za su tsare masu adalci, su biya bukatunsu kuma. Alkawalin shi ne, “Shi wanda ke tafiya bisa adilchi” “za a rika ba shi abinchinsa; ruwansa na sha tabbatache ne...” “Fakirai da masu-mayata suka nemi ruwa, amma babu, harshen su kwa ya kasa domin kishin ruwa; ni Ubangiji, ni amsa masu, ni Allah na Israila ba ni yashe su ba.” Ishaya 33:15, 16; 41:17.BJ 625.2

    “Gama ko da shike itachen baure ba za ya yi fure ba, ba kwa yaya a chikin kuringar anab ba; wahalar zaitun ta zama banza, gonaki basu ba da abinchi ba: ko da za a raba tumaki da wurin zamansu, ba a iske shanu a dangwalinsu ba;” duk da haka wadanda ke tsoronsa za su “yi murna chikin Ubangiji,” su yi farin ciki kuma cikin Allahn ceton su. Habakuk 3:17, 18.BJ 625.3

    “Ubangiji mai-tsaronka: Ubangiji Shi ne inuwarka ga hannun damanka. Rana ba za ta buge ka chikin yini ba, ko wuta da dare. Ubangiji za ya tsare ka daga dukan mugunta za ya kiyaye ranka.” “Gama za ya fishe ka daga tarkon mai-farauta, daga aloba mai-kawo mutuwa kuma. Za shi rufe ka da jawarkinsa, a kalkashin fukafukansa za ka sami kariya: gaskiyarsa garkuwa ne da kutufani. Ba za ka ji tsoron razanar dare ba; ko kwa kibiya wadda ke tashi da rana; ko aloban da ke yawo a chikin dufu, ko hallaka wadda ke lalataswa da tsakar rana. Mutum dubu za su fadi daura da kai, zambar goma kuma a hannun ka na dama; amma ba za su kusanche ka ba. Da idanun ka kadai za ka duba ka ga sakamakon miyagun mutane. Gama kai ne mafakata ya Ubangiji! Ka mai da Madaukaki wurin zamanka; babu mugunta da za ta same ka, babu wata aloba da za ta kusanchi tent naka.” Zabura 121:5-7; 91:3-10. BJ 625.4

    Duk da haka, ga ganin mutum, zai zama kaman ba da jimawa ba dole mutanen Allah za su hatimce shaidarsu da jinin su yadda jarumawan da aka kashe kafinsu suka yi. Su kansu sun fara tsoro cewa Ubangiji Ya bar su su fada hannun magabtansu. Lokaci ne na wahala mai-ban tsoro. Dare da rana su na kuka ga Allah domin kubutarwa. Miyagun za su yi takama, za a kuma ji ihun gorin cewa: “Yanzu ina bangaskiyar ta ku? Don me Allah bai kubutar da ku daga hannunmu, ba idan da gaske kumutanensa ne?” Amma masu jiran za su tuna Yesu yayin da yake mutuwa a giciyen Kalfari, da manyan priestoci da shugabanni da ke ihu suna ba’a cewa: “Ya ceci wadansu, ya kasa ceton kansa. Sarkin Israila ne shi; shi sabko yanzu daga gichiye, mu kwa mu ba da gaskiya gare shi.” Matta 27:42. Kamar Yakub, kowa yana kokowa da Allah. Fuskokinsu suna nuna faman da su ke yi a ciki. Kowace fuska ta nuna damuwa. Duk da haka basu dena addu’ar naciyarsu ba.BJ 626.1

    Da mutane sun iya gani da idon sama, da za su ga garkunan malaiku masu cikakken karfi kewaye da wadanda suka kiyaye Kalmar hakurin Kristi. Da tausayi mai-taushi sun shaida wahalarsu, suka kuma ji addu’o’insu. Su na jiran umurnin Kwamandan su ne domin su kubutar da su daga matsalarsu. Amma dole su kara jira kadan. Dole mutanen Allah su sha daga kokon, a kuma yi masu baptisma da baptismar. Jinkirin kansa da ke damun su, shi ne amsa mafi kyau ga addu’o’insu, yayin da suke jira da aminci dominUbangiji Ya yi aiki, wannan yana sa su yin bangaskiya da bege da hakuri da basu yi sosai ba lokacin rayuwarsu ta addini. Duk da haka sabo da zababbu za a takaita lokacin wahalar. “Allah fa ba za ya rama ma zababaunsa ba, da suke yi masa kuka dare da rana?... ina che maku, da samri za ya rama masu.” Luka 15:7-8. Karshen zai zo da sauri fiye da yadda mutane ke zato. Za a tattara alkamar domin rumbun Allah; za a daure zawan kamar yayi domin wutar hallaka.BJ 626.2

    Masu gadin sama, cikin amincinsu, suna ci gaba da tsaro. Ko da shike wata doka ta bai daya ta ayana lokacin da za a karkashe masu kiyaye doka, magabtansu wasu lokuta kafin lokacin da aka aiyana, za su yi kokarin dauke rayukansu. Amma ba wanda zai iya wuce manyan masu tsaron da aka ajiye kewaye da kowane amintace. Za a abka ma wadansu lokacin da suke gudu daga birane da kauyuka ne; amma makamai da aka daga domin a kashe su da su za su karye su fadi kamar kara. Malaiku cikin kamanin mayaka za su kare wadansu.BJ 627.1

    Cikin dukan sararraki Allah Yakan yi aiki ta wurin malaiku masu tsarki domin taimako da kubutarwar mutanensa. Masu rai daga sama sukan sa hannu dumu dumu cikin harkokin ‘yan Adam. Sukan bayyana cikin tufafi masu kamar walkiya; su kan zo kamar mutane cikin tufafin matafiya. Malaiku sun sha bayanuwa cikin kamanin mutane ga mutanen Allah. Sukan huta kaman sun gaji, a gindin bishiyoyi da rana. Sun sha karban liyafa a gidajen mutane. Sukan zama masu bishewa ga matafiya cikin dare. Da hannunsu sun kunna wutar bagadi. Sun bude kofofin kurkuku suka ‘yantar da bayin Ubangiji. Yafe da makamai na sama sun sauko suka ture dutse daga kabarin Mai-ceton.BJ 627.2

    Cikin kamanin mutane malaiku su kan kasance cikin masu-adalci; sukan kuma ziyarci taron miyagu, yadda suka je Sodom, domin su rubuta ayukansu, domin a san ko sun wuce kadadar hakurin Allah. Ubangiji yana jin dadin jinkai; kuma sabo da kalilan da ke ainihin bauta masa, yakan hana bala’i, ya tsawaita salamar jama’a masu yawa. Da kadan masu zunubi zuka san cewa suna raye sabo da amintattu kalilan da suke wulakantawa suna kuma yi masu ba’a ne.BJ 627.3

    Ko da shike shugabannin duniyan nan basu sani ba, duk da haka cikin majalisunsu malaiku sukan yi magana a madadin wadansu. Idanun mutane sukan gan su, kunnuwan mutane sukan ji rokonsu, lebunan mutane sun sha hamayya da shawarwarinsu, suka kuma yi ba’a gare su, hannayen mutane sun sha zagin su, suka ci mutuncinsu. Cikin zauren majalisa da kotun shari’a ‘yan sakon nan na sama sun nuna sanin tarihin ‘yan Adam kwarai; sun nuna cewa sun fi kwararrun masu kare wulakantattun nan iya kare mutanen. Sun sha canja manufofi, suka hana mugunta da kan iya kawo cikas sosai ga aikin Allah, ya kuma jawo wahala mai-yawa ga mutanensa. A sa’ar hatsari da wahala, “Malaikan Ubangiji yana kafa sansani kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.” Zabura 34:7.BJ 628.1

    Da bege mai-yawa, mutanen Allah suna jiran alamun Sarkinsu da ke zuwa. Sa’an da aka tambayi masu tsaron cewa, “Ina labarin daren?,” akan ba da amsa ba shakka cewa, “Safiya tana zuwa, dare kuma yana zuwa.” Ishaya 21:11,12. Haske yana haskakawa kan gizagizai da ke kan duwatsun. Ba da jimawa ba za a bayana darajarsa. Ranan adalci ya kusa haskakawa. Safiya da dare duk sun kusa budewar rana mara karshe ga masu adalci, tabbatar dare mara matuka ga miyagu.”BJ 628.2

    Yayin da masu kokowa suke addu’o’insu a gaban Allah, an kusan janye labulen da ya raba su da Shi. Sammai suna haskakawa da wayewar yini na har abada, kuma kamar dadin wakokin malaiku, kalmomin suna shiga kunne cewa: “Tsaya da karfi wurin biyayyarka. Taimako yana zuwa.” Kristi babban Mai-nasara yana mika ma gajiyayyun mayakansa rawanin daraja mara mutuwa; muryarsa kuma tana fitowa daga budaddun kofofi cewa: “Ga shi ina tare da ku. Kada ku ji tsoro. Na san dukan bakincikinku; na dauki bakincikinku. Ba da magabtan da basu gogu ku ke yaki ba. Na rigaya na yi yakin a madadinku, kuma cikin sunana kun fi masu nasara ma.” BJ 628.3

    Mai-ceton zai aiko taimako daidai sa’an da muke bukata ne. Hanyar sama tsarkakakkiya ce da tafin sawun kafafunsa. Kowace kaya da ke huda kafafunmu ta huda nasa. Kowane giciye da aka ce mu dauka Shi Ya rigaya Ya dauka kafin mu. Ubangiji yana barin rashin jituwa domin Ya shirya mai-rai don salama ne. Lokacin wahala ce mai-ban tsoro ga mutanen Allah; amma lokaci ne da kowane mai-ba da gaskiya na kwarai zai zabi sama, kuma ta wurin bangaskiya zai ga bakan gizon alkawalin kewaye da shi.BJ 629.1

    “Pansassu na Ubangiji kuma za su komo, da rairawa za su iso Sihiyona, farinchiki madawami za ya kasanche a bisa kansu; za su sami murna da farinchiki; bakinchiki da ajiyar zuchiya za su gudu. Ni dai ni ne mai-yi maku ta’aziya: Kai wane ne da kake jin tsoron mutum mai-mutuwa, dan mutum kuma da za a maishe shi kamar chiyawa; har ma ka manta da Ubangiji mahalichinka,.... kana jin tsoron hasalar azalumi tuttur sa’an da yana shirin hallakaswa? Ina take fa hasalar azalumi, da samri za a sake takurarre, ba za ya mutu chikin rami ba, abinchinsa kuma ba za ya sare ba. Gama ni ne Ubangiji Allahnka, wanda yakan dama teku, har da ambaliyunta su yi ruri: Ubangiji mai-runduna shi ne sunansa. Na kuma sa zantattukana a chikin bakinka, na boye ka kuma a chikin inuwar tafin hannuna.” Ishaya 51:11-16.BJ 629.2

    “Domin wannan ki ji ya ke kuntachiya, ke mai-maye amma ba da ruwan anab ba: hakanan Ubangijinki Yahweh Ya fadi, allahnki kuma wanda ya ke taimakon da’awar mutanensa, Ga shi na amshe kokon tangadinki, kwariyar hasalata ke nan: ba za ki kara shanta ba; amma zan sa ta a chikin hannun wdanda ke kuntata ki, su wadanda sun che ma ranki, Ki duka domin mu taka mu wuche: har ma kin maid a bayanki kamar kasa, kamar hanya kuma, ga wanda ke bi ta kai.” Aya 21-23.BJ 629.3

    Idon Allah, sa’anda ya dubi sararrakin da ke zuwa, ya kafu kan tashin hankalin da mutanensa za su fuskanta, sa’anda mulkokin duniya za su ja daga da su. Kamar kamamme a wata kasa, za su kasance cikin tsoron mutuwa ta wurin yunwa ko ta wurin anfani da karfi a kansu. Amma Mai-tsarkin nan da ya raba Jan Teku a gaban Israila, za ya nuna ikonsa Ya juya bautarsu. “Za su zama nawa, in ji Ubangiji Mai-runduna, a chikin wannan rana da ni ke yin ajiya mai-daraja ke nan; zan kwa kebe su, kamar yadda mutum yakan kebe dansa da ke bauta masa.” Malachi 3:17. Da za a zubar da jinin amintattun shaidun Kristi a lokacin nan ne, da ba zai zama kamar iri da aka shuka domin ya kawo ma Allah girbi ba. Amincinsu ba zai zama shaida da zai sa wadansu su amince da gaskiyar ba, gama zuciyar da ta taurara ta rigaya ta tutture rakuman ruwan jin kai ta yadda ba za su sake komawa ba. Da yanzu za a bar masu adalci a hannun magabtansu, da sarkin duhu zai yi nasara. In ji mai-zabura: “Gama a chikin ranar wahala za shi boye ni a chikin maboyar tent nasa za ya suturche ni.” Zabura 27:5. Kristi Ya rigaya Ya yi magana, ya ce: “Ku zo, mutanena, ku shiga chikin dakunanku, ku rufe ma kanku kofofi: ku buya kadan, har fushin ya wuche. Gama ga shi Ubangiji yana fitowa daga wurinsa domin Shi yi ma mazamnan duniya hukmchi sabada muguntassu.” Ishaya 26:26, 21. Mai-daraja ce cetaswar wadanda suka yi hakuri suka jira zuwansa, wadanda kuma sunayensu suna rubuce cikin Littafi na rai.BJ 630.1

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents