Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi Na 41—Mayar da Duniya Kango

    “Gama zunubanta sun kawo har sama, Allah kwa Ya tuna da muguntanta…. Chikin koko wanda ta dama, ku dama mata so biyu. Misalin da ta daukaka kanta duka, ta yi annishuwa kuma, daidai hakanan a ba ta azaba da kewa: gama chikin zuchiyatta tana chewa, Sarauniya ni ke zaune, ba gwamruwa ni ke ba, ba kwa zan ga kewa ba dadai. Domin wannan fa rana daya alobanta za su zo, mutuwa da kewa da yunwa; za a kone ta sarai da wuta; gama Ubangiji Allah Mai-tsarki ne wanda ya shar’anta mata. Sarakunan duniya kwa wadanda suka yi fasikanchi da ita, suka yi zaman annishuwa kuma tare da ita, za su yi kuka da kuwa bisanta,… suna cewa, kaito, kaito, babban birnin, Babila, birni mai-karfi! gama chikin sa’a daya hukumcinki za ya zo.” Ruya 18:5-10.BJ 649.1

    “Dillalan duniya kuma” da “suka wadata bisa ga ikon annishuwanta,” za su tsaya daga nesa domin tsoron azabatta, suna kuka suna bakinzuchiya, suna ta chewa, Kaito, kaito babban birni, ita wadda takan yafa da linen mai-labshi da shunaiya da mulufi,takan yi ado da zinariya da duwatsu masu tamani da lu’u lu’u gama chikin sa’a daya duniya mai-yawa haka ta lalache.” Ruya 18:11,3,15-17. BJ 649.2

    Irin hukumcin da za su fada ma Babila ke nan a ranar fushin Allah. Ita ta cika mudun zunubinta; lokacinta ya zo; ta isa hallakawa daidai.BJ 649.3

    Sa’an da muryan Allah zai juya bautar mutanensa, akwai falkaswa mai-ban tsoro ta wadanda suka yi hasarar komi cikin babban yakin nan na rai. Kafin a rufe gafara, rudin Shaitan ya makantar da su, suka ba da hujja domin halinsu na zunubi. Mawadata sun rika alfahari da fifikonsu kan matalauta, amma sun sami arzikinsu ta wurin ketare dokar Allah ne. Sun ki ciyar da mayunwata, suka ki suturta marasa sutura, su yi adalci su kuma so jin kai. Sun so su daukaka kansu su kuma sami ban girma daga sauran halitu, sai ga shi an raba su da duk ababan da suka yi takama da su, aka bar su a tsiyace ba tsaro kuma. Da razana suna kallo za a hallaka gumakan da suka girmama fiye da Mahalicinsu. Sun rigaya sun sayar da rayukansu domin wadata domin wadata da jin dadi na duniya, basu kuma bidi wadata game da Allah ba. Sakamakon shi ne cewa rayuwarsu ba ta da nasara; jin dadinsu ya zama da daci kamar matsarmama, dukiyarsu ta lalace. Cikin dakika daya za a share abin da suka tara duk tsawon rauwarsu. Mawadata za su yi bakincikin hallakar manyan gidajensu da watsarwar zinariyansu da azurfansu. Amma makokinsu zai tsaya domin tsoron cewa su kansu da gumakansu za su hallaka. Miyagu za su cika da nadama, ba domin rabuwarsu da Allah da yan’uwansu ‘yan Adam ba, amma domin Allah Ya yi nasara. Suna bakincikin yadda sakamakon ya kasance ne, amma ba za su tuba daga muguntarsu ba. Da akwai abin da za su iya yi don samun nasara da za su yi shi. BJ 650.1

    Duniya za ta ga cewa mutane da suka yi masu ba’a, suka rena su, suka kuma so su hallaka su, ga su suna wucewa cikin annoba da guguwa da rawan duniya, ba matsala. Shi wanda wuta ne mai-hallakaswa ga masu ketare dokarsa, rumfar tsaro ne ga mutanensa.BJ 650.2

    Mai-aikin bishara da ya sadakar da gaskiya domin ya sami karbuwar mutane, yanzu zai gane yanayi da tasirin koyaswoyinsa. A bayane yake cewa idon Allah yana bin shi a wurin aikinsa, a titi, yayin da yake ma’amala da mutane cikin fannoni dabam dabam na rayuwa. Kowane yanayi na rayuwarsa, kowane abin da aka rubuta, kowace kalma da aka furta, kowane abin da ya kai mutane ga amincewa da karya, yana shuka iri ne; yanzu kuma zai ga girbin wahalallun batattun rayukan da ke kewaye da shi ne.BJ 650.3

    In ji Ubangiji: “Sun warkar da chiwutar diyar mutanena bisa bisa kadai, sun che Lafiya, lafiya; ba kwa lafiya.” “Tun da kun bata zuchiyar masu adilchi da karya, wadanda ni ban bata masu zuchiya ba; kun karfafa hannuwan mugu, da ba za shi juya ga barin muguntassa ba, shi tsira da ransa.” Irmiya 8:11; Ezekiel 13:22.BJ 651.1

    “Kaiton makiyaya wadanda ke hallaka tumakin makiyayata…ga shi, zan jawo maku muguntar ayukanku, in ji Ubangiji.” “Ku yi ihu, ku makiyaya, ku yi ta kuka; ku yi birgima chikin toka, ku shugabannan garke: gama lokachin kisanku ya yi sarai,… Makiyaya kuma za su rasa hanyar gudu, shugabannan garke kuma za su rasa hanyar tsira.” Irmiya 233:1,2; 25:34,35.BJ 651.2

    Shugabannin addini da sauran mutane za su ga cewa basu rike dangantaka mai-dacewa da Allah ba. Za su ga cewa sun yi tawaye ga Mai-ba da dukan dokokin adalci. Kawar da umurnin Allah ya jawo babban mabulbulan mugunta da rashin jituwa da kiyayya da zunubi, har sai da duniya ta zama babban fili guda na tashin hankali da lalacewa. Abin da wadanda suka ki gaskiya suka kuma rungumi kuskure za su gani ke nan a wannan lokacin. Babu harshen da zai iya bayana irin sha’awan da marasa biyayya za su yi, na rai madawami da suka rasa har abada. Mutanen da duniya ta yi masu sujada sabo da baiwarsu da iya maganarsu, yanzu za su ga ainihin yanayin ababan nan. Za su gane abin da ta wurin zunubi suka rasa, za su kuma fadi a sawayen wadanda suka rena amincinsu, za su kuma furta cewa Allah Ya kaunace su. BJ 651.3

    Mutanen za su ga cewa an yaudare su. Za su zargi juna da cewa sun kai su ga hallaka; amma dukansu za su hada kai su jibga dukan zarginsu kan shugabannin addini. Pastoci marasa aminci sun yi annabcin ababa masu dadi, suka sa masu sauraronsu suka wofinta dokar Allah suka kuma tsananta ma masu son kiyaye ta da tsarki. Yanzu, cikin bakincikinsu, mallaman karyan nan za su furta a gaban duniya cewa sun rudi mutane. Taron jama’a za su cika da fushi. Za su ce: “Mun bata! Kuma ku ne sanadin hallakrmu,” sa’an nan za su koma kan makiyayan karyan. Wadanda suka fi sha’awansu a da, za su furta la’ana mafi-muni a kansu. Hannuwan da suka taba manna masu lambobin girmamawa za a daga domin hallaka su. Za a yi anfani da makaman da aka so a hallaka mutanen Allah da su domin hallaka magabtansu yanzu. Ko ina akwai tashin hankali da zub da jini.BJ 651.4

    “Kara za ta kai har matukar duniya; gama Ubangiji yana shari’a da al’ummai, za ya kai dukan masu rai garin shari’a; don miyagu kwa, za ya bashe su ga takobi.” Irmiya 25:31. Har shekaru dubu shida babban jayayyar tana gudana; Dan Allah da ‘yan sakonsa na sama suna fada da ikon mugun, domin su fadakar, su mayar da kwana, su kuma ceci ‘ya’yan muatane. Yanzu kowa ya dauki matakinsa; miyagu sun hada kai da Shaitan gaba daya cikin yakinsa da Allah. Lokacin ya zo da Allah zai nuna ikon dokarsa da aka tattake. Yanzu jayayyar ba da Shaitan ne kadai ba, amma har da mutane ma. “Ubnagiji yana da jayayya da al’ummai;” “Za ya ba da wadanda ke miyagu ga takobi.” BJ 652.1

    Bayan an ba da shaidar cetaswa ga wadanda ke bakincikin dukan ban kyama da ake yi, yanzu malaikan mutuwa zai fita, wanda a wahayin Ezekiel aka misalta da mutanen da ke rike da makamai na yanka, wadanda aka ba su umurni cewa: “Ku karkashe sarai tsofo, da sarmayi da budurwa, kananan yara da mata; amma kada ku kusanto kowane mutum wanda shaida tana kansa; a sama kuma, a wuri mai-tsarki nawa.” Ezekiel 9:1-6. BJ 652.2

    Aikin hallakan zai fara cikin wadanda suka ce su ne masu kiwon ruhaniyar mutanen ne. Masu tsaro na karyan ne za su fara mutuwa. Ba wanda za a tausaya masa ko a kyale shi. Maza da mata da ‘yan mata da kananan yara duk za su hallaka.BJ 652.3

    “Ubangiji yana fitowa daga wurinsa domin shi yi ma mazamnan duniya hukumci sabada muguntassu: kasa kuma ta bude asirin jininta, ba kwa za ta kara rufe kisassunta ba.” Ishaya 26:21. “Amma aloba ke nan wadda Ubangiji za ya buga dukan al’ummai da ita, wadanda suka yi yaki da Urushalima; namansu za ya rube tun suna tsaye, idanunsu za su rube a chikin kwarinsu, harshensu kuma za shi rube a chikin bakinsu. Za ya zama kwa a chikin ranan nan, fargaba mai-yawa daga wurin Ubangiji za ta kama su; kowane dayansu kuma za ya kama hannun makwabcinsa, hannunsa kuma za ya shiga tasamma hannun makwabchinsa.” Zechariah 14:12,13. Cikin mahaukaciyar tarzumar fushinsu kansu, da kuma zubowar fushin Allah da ba a surka ba, miyagun mazamnan duniya: priestoci da shugabanni da mutane, mawadata da matalauta, manya da kanana za su mutu. “A ranan nan fa za a ga kisassun Ubangiji tun daga wannan iyakan duniya zuwa wannnan iyaka: ba za a yi makokinsu ba, ba za a tattara, ba kwa za a bizne su ba.” Irmiya 25:33.BJ 652.4

    Lokacin zuwan Kristi, za a shafe miyagu daga fuskar duniya, za ya cinye su da lumfashin bakinsa ya hallaka su kuma da hasken darajarsa. Kristi zai dauki mutanensa zuwa Birnin Allah, a dauke mazamnan duniya daga cikinta. “Duba, Ubangiji yana mai da duniya wofi, yana maishe ta kufai, yana kabantadda ita, yana matsadda mazamnanta.” “Kasa za ta wofinta sarai, ta bachi sarai: gama Ubangiji Ya fadi wannan magana.” “Sabada sun ketare dokokin sun sake farilla, suna ta da madawamin alkawali. Domin wannan la’ana ta cinye kasan, mazamna a chikinta kuma an iske su masu laifi ne: domin wannan mazamnan kasa sun kone.” Ishaya 24:1,3,5,6.BJ 653.1

    Dukan duniya ta zama kamar kangon jeji. Kufai na birane da kauyuka, wadanda rawan duniya ya hallaka, itatuwa da aka tumbuke, duwatsun da teku ya jefo, ko kuma aka yaga daga kasa kanta, suna warwatse a fuskar kasa, yayin da manyan koguna suka zama alamun inda aka tumbuke duwatsun daga tushensu.BJ 653.2

    Yanzu al’amarin da hidimar karshe ta ranar kafara takan misalta zai faru. Sa’an da aka gama hidima a cikin wuri mafi-tsarki, aka kuma cire zunuban Israila daga haikalin ta wurin jinin hadaya ta zunubin, sa’an nan akan kawo bunsurun Azazel din da ransa gaban Ubangiji; a gaban taron jama’a kuma babban priest za “shi furta dukan muguntar ‘ya’yan Isarila a bisansa, da dukan laifofinsu, watau zunubansu duka; za a sa su a bisa kan bunsurun.” Leviticus 16:21. Hakanan kuma sa’an da aka kamala aikin kafara a haikalin sama, sa’an nan a gaban Allah da malaikun sama, da rundunan fansassun, za a aza zunuban mutanen Allah a kan Shaitan; za a kuma bayana cewa shi ne mai-laifin dukan muguntan da ya sa suka aikata. Kuma kamar yadda akan kori bunsurun Azazel din zuwa kasan da babu kowa a ciki, hakanan za a kori Shaitan zuwa kangon duniya inda ba kowa, jeji mara ban sha’awa.”BJ 654.1

    Mai-ruyan ya yi annabcin korar Shaitan da yanayin rashin tsari da kango da duniya za ta kasance, ya kuma ce yanayin nan zai kasance har shekara dubu. Bayan ya bayana yadda zuwa Ubangiji na biyu da hallakar miyagu, annabcin ya ci gaba da cewa: “Na ga wani malaika kuma yana sabkowa daga sama, yana rike da makublin rami mara-matuka, yana kwa da babbar sarka a hanunsa. Sai ya damki dragon tsofon maciji, shi ne Ibelis da Shaitan, ya damre shi har zuwa shekara dubu, ya jefas da shi chikin rami mara-matuka, ya rufe bakin, ya sa masa hatimi a bakinsa, domin kada shi kara rudin al’ummmai, har shekara dubu suka chika: bayan wannan sai a kwanche shi domin kankanin lokachi.” Ruya 20:1-3.BJ 654.2

    Batun cewa “rami mara —matuka” yana misalta duniya a yanayin ta na kango da duhu ne, a bayane yake cikin wadansu nassosi dabam. Game da yanayin duniya “a chikin farko,” Littafin ya ce, “Kasa kwa sarari che wofi kuma; a kan fuskar zurfi kuma sai dufu.” Farawa 1:2. Annabci yana koyar da cewa za a sake dawo da duniya wannan yanayin. Sa’an da ya hangi babban ranar Allah, annabi Irmiya y ace: “Na duba kasa, ga kufai, kango che: na duba sammai, ba su da haske, na duba duwatsu, ga su suna rawan jiki, dukan tuddai kuma suna makerketa. Na duba, ga shi, babu mutum; dukan tsuntsayen sama kuma sun tashi sun tafi. Na duba kuma, ga Karmel ta zama jeji, dukan biranen kuma sun rurrushe.” Irmiya 4: 23-26.BJ 654.3

    Nan ne zai zama gidan Shaitan da miyagun malaikunsa har shekara dubu. Iyakar shi duniyan nan, ba zai iya zuwa wadansu duniyoyi ba har da zai jarabci wadanda basu taba faduwa ko kuma ya fitine su ba. Ta yadda za a daure shi kenan: babu sauran wadanda zai gwada ikon shi a kansu. An yanke shi gaba daya daga aikin rudi da hallaka da ya yi daruruwan shekaru yana jin dadin yi.BJ 655.1

    Annabi Ishaya da ya hangi lokacin da za a hambarar da Shaitan, ya ce: “Daga sama ga faduwarka, ya Lucifer, dan asubahi. Duba fa, aka datse ka har kasa, kai mai-kasadda al’ummai! …Chikin zuchiyarka ka che, Har sama zan hau, zan daukaka kursiyi na bisa tamrarin Allah….in mai da kaina kamar Mai-iko duka. Amma dai har lahira za a gangaradda kai, har zuwa iyakar kurewar ramin. Wadanda suka ganka za su zuba maka ido, su yi bimbini a kanka, su che, Ko shi ne mutumin da ya sa duniya ta yi rawa, mai-girgiza mulkoki; wanda ya mayas da duniya kamar jeji, ya kabantadda biranenta; wanda ba yakan saki kamammunsa su koma gidansu ba?” Ishaya 14: 12-17.BJ 655.2

    Shekara dubu shida aikin tawayen Shaitan “ya sa duniya ta yi rawa.” Ya “mayas da duniya kamar jeji, ya kabantadda biranenta;” kuma “ba yakan saki kamammunsa.” Shekara dubu shida kurkukunsa yana tara mutanen Allah, kuma da ya rike su kamammu har abada, amma Kristi Ya yanke sarkokin, Ya saki fursunonin.BJ 655.3

    Ko miyagu ma za su kasance inda ikon Shaitan ba zai kai su ba, sa’an nan zai kasance daga shi sai miyagun malaikunsa domin su gane sakamakon la’anan da zunubi ya jawo. “Dukan sarakunan al’ummai, ai, dukansu, a chikin daraja su ke barchi, kowa chikin gidansa [kabari]. Amma kai an yas da kai chan bayan kushewar kamar reshe abin kyama,….Ba za ka tara zamanka da su chikin kabari ba, gama ka hallaka kasarka, ka kashe talakawanka.” Ishaya 14:18-20.BJ 656.1

    Har shekara dubu, Shaitan zai yi ta yawon banza nan da can cikin kangon duniya domin ya ga sakamakon tawayen sa ga dokar Allah. A wannan lokacin wahalolinsa za su yi tsanani. Tun faduwarsa, rayuwarsa ta aiki ba tsayawa ta hana shi yin bimbini; amma yanzu za a hana shi ikonsa a kuma bar shi ya yi bimbini game da aikin da shi ya yi tun da ya yi tawayensa na farko ga gwamnatin Allah, ya kuma hangi gaba da rawan jiki da razana zuwa ga lokacin da dole zai sha wahala sabo da dukan muguntan da ya yi, a kuma hore shi sabo da zunuban da ya sa aka yi.BJ 656.2

    Ga mutanen allah, daurin Shaitan zai kawo murna da farin ciki. In ji annabi: “Za ya zama kuma a chikin ranan nan da Ubangiji za ya hutadda kai daga bakinchiki naka, da wahalarka, da bauta mai-wuya wadda aka sa maka, sa’an nan za a mai da wannan habaichi bisa sarkin Babila [watau Shaitan kenan], ka che, Ga yanda mai-wulakanchi ya kare!... Ubangij iYa karya sandar miyagu, kandirin masu-mulki; shi wanda ya dinga bugun dangogi chikin fushi, ya mallaki al’ummai da fushi, da tsanani wanda ba mai-hanawa.” Aya 3-6.BJ 656.3

    Cikin shekaru dubu, tsakanin tashin matattu na fari da na biyu din, hukumcin miyagu za ya gudana. Manzo Bulus ya nuna cewa hukuncin nan zai biyo zuwan Kristi na biyu ne. “Kada ka shar’anta komi da garaje, kamin Ubangiji ya zo, wanda za ya tone boyayyun al’amura na dufu, ya bubbude shawarwarin zukata a sarari.” Korinthiyawa I, 4:5. Daniel ya ce sa’anda Mai-zamanin da Ya zo, “aka ba da shari’a chikin hannuwan tsarkaka na Madaukaki.” Daniel 7:22. A wannan lokacin, masu adalci za su yi mulki a matsayin sarakuna da priestoci ga Allah. Yohanna cikin Ruya ya ce: “Na ga kursiyin kuma, akwai mazamna a bisansu kuma, aka ba da shari’a chikin hannunsu.” “Za su zama priests na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi shekara dubu.” Ruya 20:4,6. A wannan lokacin ne kamar yadda Bulus ya ce, “trsarkaka za su yi ma duniya sahri’a.” Korinthiyawa I, 6:2. Tare da Kristi, za su sahr’anta miyagu, suna gwada ayukansu da littafin dokokin, watau Littafi Mai-tsarki, suna hukumta kowane mutum bisa ga ayukan da aka yi cikin jiki. Sa’an nan za a bayana horon da za a ba miyagun, bisa ga gayukansu, sai a kuma rubuta shi daidai sunayensu a cikin littafin mutuwa.BJ 656.4

    Kristi da mutanensa za su kuma shar’anta Shaitan da miyagun malaikunsa. In ji Bulus: “Ba ku sani ba mu za mu yi ma malaiku shari’a?” Aya 3. Yahuda kuma ya bayana cewa: “Malaiku kuma wadanda basu rike matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama, ya tsare su chikin madawaman sarkoki a chikin dufu zuwa hukumchin babban ranar.” Yahuda 6.BJ 657.1

    A karshen shekara dubu din, tashi na biyu din zai gudana. Sa’an nan za a ta da miyagu daga matattu su bayana a gaban Allah domin aiwatar da rubutacen hukumcin. Ta hakanan, mai-ruyan, bayan ya bayana tashin matattu na masu adalci, ya ce: “Sauran matattu basu rayu ba sai shekara dubu din suka chika tukuna.” Ruya 20:5. Ishaya kuma ya bayana, game da miyagu, cewa: “Za a tara su wuri daya kamar yadda ake tara ‘yan sarka a rami, za a kuble su a chikin kurkuku, bayan kwana da yawa kuma za a ziyarche su da hukumchi.” Ishaya 24:22. BJ 657.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents