Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    Babi na 12—Canjin Faransa

    Shekarun fada da duhu ne suka biyo bayan Kin yardan nan na Spires da Kudurin nan na Augsburg da suka jawo nasarar Canjin a Jamus. Da shike tsatsaguwa tsakanin magoya bayanta ya raunana ta, magabata kuma suka rika cakunarta, Kin yardar ta fuskanci yiwuwar rushewa kwata kwata. dubbai suka hatimce shaidarsu da jininsu. Yakin basasa ya barke; daya daga cikin shugabannin Kin yardan ne kuwa ya bashe ta; mafiya martaba cikin ‘ya’yan sarakuna yan canji sun fada cikin hannun babban sarkin, aka rika jan su daga gari zuwa gari kamar kamammu. Amma lokacin da babban sarkin ya ga kamar ya yi nasara ne aka ka da shi. Yana gani aka kwace kamammunsa daga hannunsa, aka tilasta shi a karshe dai ya ba da yanci ga koyaswoyin da ya dade yana so ya rushe. Ya rigaya ya kashe kasarsa da rayuwarsa da dukiyarsa ma a kan rushewar ridda. Yanzu kuma ya ga mayakansa suna mutuwa a cikin yaki, dukiyarsa tana karewa, kasashensa da yawa suna fama da tawaye, yayin da ko ina bangaskiyan da ya kasa dannewa tana yaduwa ne. Charles V ya yi ta yaki da Mai-cikakken iko ne. Allah Ya ce: “Bari haske shi kasance,” amma babban sarkin ya so ya sa duhu ya dawama. Shirin shi ya rushe; cikin saurin tsufa kuwa, ga gajiyar yaki mai-tsawo, ya sauka daga sarautar, ya boye kansa cikin gidan masu zaman zuhudu.BJ 209.1

    A Switzerlaand, kamar Jamus, kwanakin duhu suka abko ma Canjin, yayin da jihohi da yawa suka karbi sabuwar bangaskiyar, wadansu suka manne ma koyaswar Rum. Zaluncin da suka yi ma masu so su karbi gaskiyar ya kawo yakin basasa a karshe. Zwingli da magoya bayansa cikin canji suka mutu a filin Cappel. Oecolampaedius, sa’an da masifun nan suka fi karfinsa, ya mutu nan da nan. Rum ta yi nasara, kuma a wurare da yawa ta kusa ta dawo da dukan ababan da ta yi hasarar su. Amma Shi wanda shawarin Sa tun fil azal ne, bai kyale aikinsa ko mutanensa ba. Hannun shi ya kawo masu kubuta. A wadansu kasashe Ya ta da ma’aikata da za su ci gaba da Canjin. BJ 209.2

    A Faransa, kafin a ji sunan Luther a matsayin dan Canji, gari ya fara wayewa. Daya daga cikin na farkon kama hasken shi ne tsohon nan Lefevre, mai tarin ilimi sosai, shehun mallami a Jami’ar Paris, amintacen da tsarin paparuma, mai-kwazo kuma. Cikin bincikensa na littattafai na da, hankalin sa ya kai ga Littafin, ya kuwa gabatar da nazarin sa ga dalibansa.BJ 210.1

    Lefevre mai-yawan sha’awar tsarkaka ne, ya kuma kudurta zai shirya tarihin tsarkaka da masu mutuwa sabo da addininsu, yadda yake cikin labaru na ekklesiya. Aikin nan ya kunshi fama mai-yawa; amma ya rigaya ya yi nisa da shi sosai, sa’an da, ganin cewa zai sami Karin taimako daga Littafi, ya shiga nazarin shi. Nan kuwa ya ga labarum tsarkaka, amma ba irin yadda ake nunawa cikin tsarin Rum ba. Ambaliyar hasken Allah ta kwararo ma tunaninsa. Cikin mamaki da kyama ya juya daga aikin da ya ba kan shi, ya dukufa ga maganar Allah. Nan da nan ya fara koyar da muhimman gaskiyan da ya gano a wurin.BJ 210.2

    A 1512, kafin Luther ko Zwingli su fara aikin canji, Lefevre ya rubuta cewa: “Allah ne yake ba mu ta wurin bangaskiya, adalcin nan da ke barataswa zuwa rai madawami.” Cikin bimbinin al’ajibin fansa, ya ce: “Dubi girman musayan nan, - an hukumta Mara-laifin, shi mai-laifin kuma an sallame shi; Mai-albarkan Ya dauki la’anar, mai-la’anar kuma ya sami albarka, Rai Ya mutu, matacen kuma ya rayu; Darajan ya nannadu cikin duhu, shi kuma wanda da bai san komi ba sai rudami an suturta shi da daraja.”BJ 210.3

    Kuma yayin da yake koyar da darajar ceto ta Allah ce Shi kadai, ya kuma ce aikin mutum biyayya ne. Ya ce: “Idan kai memban ekklesiyar Krisri ne, kai memban jikinsa ne; idan kai na jikinsa ne, to kana cike da yanayi na Allahntaka .... Da dai mutane za su gane zarafin nan, da za su yi rayuwar tsabta da tsarki, su kuma ga munin darajar duniyan nan idan aka gwada da darajan nan da ido ba zai iya gani ba.”BJ 211.1

    Akwai wadansu cikin daliban Lefevre da suka ji kalmominsa da marmari, wadanda kuma da dadewa bayan mutuwarsa suka ci gaba da shelar gaskiyar. William Farel yana daga cikinsu. Iyayensa masu ibada ne, an kuma koya ma shi ya yarda da koyaswoyin ekklesiya da bangaskiya, har ma kamar manzo Bulus, zai iya fadi game da shi kansa cewa: “Bisa ga tarika mafi kunci ta addininmu na yi zaman Ba-farisi.” Ayukan 16:5. Da shike tsayayyen dan ekklesiyar Rum ne, ya rika himmar hallaka dukan masu jayayya da ekklesiyar. “Ni kan rika cizon hakora kamar kerkeci idan na ji wani yana magana sabanin paparuma,” in ji shi. Ba ya gajiya da girmama tsarkaka, tare da Lefevre sukan bi majami’un Paris, suna sujada a haikalin, suna kuma barin kyautuka a bagadin. Amma ayukan nan basu ba shi salama ba. Laifin zunubin shi ya dame shi, kuma dukan ayukansa na neman gafara basu kau da alhakin laifin ba. Ya saurari kalmomin dan Canjin kamar murya daga sama, cewa: “Ceto daga alheri ne.” “An hukumta Mara-laifin, aka sallami mai-laifin.” “Giciyen Kristi ne kadai yake bude kofofin sama, yana kuma rufe kofofin lahira.”BJ 211.2

    Farel ya karbi gaskiyar da farinciki. Da irin tuban Bulus, ya juya daga bautar al’ada zuwa yancin yayan Allah. “Maimakon zuciyar kisa irin ta mugun kerkeci,” ya ce, na dawo “shuru kamar dan rago mai-tawali’u, mara cetaswa, da zuciya da aka bayas ga Yesu Kristi.” BJ 212.1

    Yayin da Lefevre ya ci gaba da watsa hasken a cikin dalibansa, Farel, da himma cikin aikin Kristi irin wanda ya nuna cikin aikin paparuma, ya ci gaba da bayana ma jama’a gaskiyar. Ba da jimawa ba, wani babban memban ekklesiyar Rum, bishop na Meaux, ya hada kai da su. Wadansu mallamia, shahararrun masana, suka hada hannu cikin shelar bisharan, ta kuwa sami magoya baya daga dukan bangarori, daga gidajen masu aikin hannu da fakirai, har fadar sarkin. Yar’uwar Francis I, wanda ke sarauta a lokacin, ta karbi sabuwar gaskiyar. Sarki kansa da uwarsa, sun nuna alamar goyon baya, da bege sosai kuma yan Canjin suka dinga begen ranan da Faransa za ta karbi bisharar. BJ 212.2

    Amma begensu bai cika ba. Kunci da zalunci sun abka ma almajiran nan na Kristi, amma cikin alheri aka boye wannan daga idanunsu. Lokacin salama ya shiga tsakani, domin su sami karfi su fuskanci guguwar; canji kuma ya ci gaba sosai. Bishop na Meaux ya yi aikii tukuru a diocese dinsa don koya ma limamai da sauran mutane. Aka sauke jahilan priestoci da fasikan cikinsu, aka kuma sauya su da masu illimi da ibada. Bishop din ya so mutanensa su sami maganar Allah don kansu, hakan kuwa ya samu nan da nan. Lefevre ya shiga juya Sabon Alkawali zuwa Farasanci a Meaux. Bishop din bai yi kiwuya ba , ya kuma kashe kurdi don baza shi cikin kowane parish dinsa, jima kadan kuwa talakawan Meaux suka mallaki Littafin. BJ 212.3

    Kamar yadda matafiya da ke mutuwa da kishirwa sukan marabci mabulbular ruwa da murna, hakanan mutanen nan suka karbi sakon sama. Leburori da masu aikin hannu suka rika rage gajiyar aiki ta wurin tattaunawa game da gaskiyar Littafin. Da yamma, maimakon komawa wurin aiki, sukan taru a gidajen juna don karanta maganar Allah da kuma addu’a da yabo. Nan da nan aka ga babban canji cikin mutanen nan. Ko da shike talakawa ne su, marasa ilimi, masu zafin aiki , ikon alherin Allah mai-kawo canji da girmamawa ya bayana a rayuwarsu. Cikin tawali’u da kauna da tsarki, suka kasance shaidun abin da bishara za ta yi ma wadanda suka karbe ta da gaske. BJ 213.1

    Hasken da aka kunna a Meaux ya kai tsirkiyoyin sa da nisa. Kowace rana yawan masu tuba ya dinga karuwa. Sarkin ya dakatar da fushin ekklesiyar, ya rena rashin sassaucin masu zaman zuhudun; amma daga baya shugabannin yan paparuman suka yi nasara. Sai aka kafa wurin kisan. Bishop na Meaux da aka tilasata masa zabi tsakanin wuta da janyewa, sai ya zabi hanyar saukin; amma duk da faduwar shugaban, garkensa suka tsaya da karfi. Da yawa suka shaida gaskiyar a cikin wutan. Ta wurin karfin zuciyarsu da amincinsu, har mutuwa Kiristan nan suka yi ma dubbai magana, wadanda kuwa a lokacin salama basu taba jin shaidarsu ba.BJ 213.2

    Ba masu tawali’u da matalauta ne kadai suka shaida Kristi cikin wahala da reni ba. A dakunan taro na manyan gidaje da na fada, akwai masu sarauta da suka san anfanin gaskiya fiye da wadata ko matsayi ko rai kansa ma. Sulken sarauta ya boye ruhu mafi daraja fiye da yadda rigar priest da hularsa suka yi. Louis de Berquin haifaffen dan sarauta ne. Ba-fade ne mai-karfin zuciya da ya dukufa cikin nazari, mai halayyan kirki ne kuma mara kazanta ko halin fasikanci. Wani marubuci ya ce: “Shi babban mai-bin kundin tsarin dokokin paparuma ne, babban mai sauraron mass da wa’azu;... ya kuma kalmasa dukan halayyansa ta wurin kiyayya ta musamman da yake yi ma tsarin Luthanci.” Amma kamar wadansu da yawa kuma, Allah Ya bishe shi zuwa Littafin, ya yi mamaki da ya ga a ciki, ba koyaswoyin Rum ba, amma koyaswoyin Luther.” Daga nan sai ya mika kan sa da cikakkiyar dukufa ga aikin bishara.BJ 213.3

    Babban masani cikin fadawan Faransa, hikimarsa, da kaifin harshensa, karfin zuciyarsa da himar jaruntakansa, da kuma tasirinsa a fada — gama yana da farin jini a gaban sarkin — sun sa mutane da yawa suka dauka cewa shi ne zai zama dan Canjin kasarsa. Beza ya ce: “Da Berquin ya zama Luther na biyu, in da Francis I ya zama masa mai-zabe na biyu.” Yan paparuma suka ce: “Ya fi Luther muni.” Masu bin Rum a Faransa sun fi jin tsoron sa kam. Suka jefa shi a kurkuku cewa shi mai ridda ne, amma sarkin ya fitar da shi. An yi shekaru ana ci gaba da jayayyar. Francis, da ya rika canjawa tsakanin Rum da Canjin, wani lokaci yakan kyale zazzafan ra’ayin masu zaman zuhudu, wani lokaci kuma ya hana. Sau uku mahukuntan ‘yan paparuma suka sa Berquin a kurkuku, sarkin kuma yana cire shi, kuma domin yana sha’awar hikimarsa, ya ki ya sadakar da shi ga kiyayyar ekklesiya.BJ 214.1

    An dinga yi ma Berquin kashedi akai akai game da hatsarin da ke kansa a Faransa, aka kuma shawarce shi ya bi sawun wadanda suka yi gudun hijira don kansu. Matsoracin nan Erasmus, wanda duk da yawan ilimin sa, ya kasa samun kyaun halin nan da kan daukaka gaskiya fiye da rai, da girma, ya rubuta ma Berquin cewa: “Ka roka a sa ka zama jakada a wata kasar waje; je ka yi tafiya a Jamus. Ka san Beda da irinsa, dodo ne shi mai kawuna dubu, yana fesa dafi kowane gefe. Sunan magabtan ka tuli. Ko aikin ka ya fi na Yesu Kristi, ba za su bari ka tafi ba, har sai sun hallaka ka a wulakance. Kada ka dogara sosai ga tsaron sarkin. Duk yadda aka yi, kada ka raunana ni da tunani na tauhidi.”BJ 214.2

    Amma sa’an da hatsaruka suka karu, himmar Berquin ta kara karfi ne. Maimakon yarda da shawarar Erasmus, ya shirya matakai mafi karfi ne. Ba kare gaskiya kadai zai yi ba, zai kuma tinkari kuskure. Zargin ridda da ‘yan Rum suka so su manna masa, shi ne zai juya a kansu. Abokan hamayyansa mafi kwazo da daci su ne likitocin nan da ‘yan zuhudu na sashen tauhidi a jami’ar Paris, daya daga shugabanni mafi girma na elkklesiya a birnin da kuma kasar. Daga rubuce rubucen likitocin nan Berquin ya samo ababa goma sha biyu da ya shaida a fili cewa sun “saba ma Littafin, kuma ridda ne;” ya kuma roki sari ya zama mai yanka hukmcin. BJ 214.3

    Sarkin da shike bai so ya nuna bamabncin karfin jarumawa biyu din ba, kuma yana murnar samun zarafin kaskantar da girman ran masu zaman zuhudun nan, ya bukaci Rum din su kare kansu ta wurin Littafin. Sun san sarai cewa wannan makamin ba zai haifar da komi ba; fursuna da zalunci da konewa ne makaman da suka iya anfani da su. Yanzu ga shi an juya kaidar, suka ga kansu gaf da faduwa cikin ramin da suka so su tura Berquin ciki. Cikin rudewa suka dinga neman mafita. BJ 215.1

    “Daidai wannan lokacin aka guguntule siffar Budurwa Maryamu a lungun wani titi.” Hankula suka tashi sosai a birnin. Jama’a suka yi ta tururuwa zuwa wurin, suna nuna bakin ciki da fushi. Sarkin ma ya damu sosai. Wannan al’amari ne da yan zuhudun za su iya mai da shi abin anfani, suka kuwa yi hakanan. Suka ce: “Sakamakon koyaswoyin kenan. Yanzu za a hambarar da komi — addini, dokoki, gadon sarauta kansa — ta wurin wanan hadin baki na Luthawa.”BJ 215.2

    Aka sake kama Berquin kuma. Sarkin ya janye daga Paris, aka kuwa bar masu zuhudun su yi abin da suka ga dama. Aka shar’anta dan Canjin, aka kuma hukunta cewa za a kashe shi, kuma domin kada Francis ya shiga tsakani ya cece shi, aka aiwatar da hukumcin kisan ranan da aka sanar da shi. Da tsakar rana aka kai Berquin wurin mutuwarsa. Jama’a da yawa suka taru domin su kalli al’amarin, da yawa kuwa suka kalla cikin mamaki da tsoro, ganin cewa mutumin nan daga iyalai mafi nagarta, mafi karfin zuciya na Faransa, aka zabe shi. Mamaki da haushi da reni da kiyayya mai-daci suka cika fuskokin jama’an nan; amma fuska guda daya ba ta nuna damuwa ba. Tunanin Berquin ba ya wurin wannan hayaniyar; ya san da kasancewar Ubangijinsa ne kawai.BJ 215.3

    Bai damu da akwalar karusar da aka dauke shi ciki ba, ko fuskokin azalumansa, ko mumunan mutuwar da zai yi; shi wanda ke raye, kuma Ya mutu, kuma yana raye har abada, kuma yana da mabudai na mutuwa da na lahira, yana tare da shi. Fuskar Berquin ta haskaka da haske da salamar sama. Ya rigaya ya sa sutura masu kyau sosai. Zai shaida bangaskiyarsa a gaban Sarkin sarakuna da shaidu daga dukan halitta, kuma bai kamata wata alamar bakin ciki ta bata farin cikinsa ba.BJ 216.1

    Yayin da ake tafiya da shi ta titunan garin, mutane sun yi mamaki, ganin salama da murnan nasara da ke fuskarsa. Suka ce: “Ya yi kama da wanda ke zaune a haikali, yana tsakanci game da ababa masu tsarki.” BJ 216.2

    A wurin kisan nasa, Berquuin ya yi kokarin yi ma mutane jawabi; amma masu zuhudun, sabo da tsoron sakamakon, suka fara ihu, sojoji kuma suna tafa makamansu, har surutunsu ya rufe muryar Berquin. Ta haka, a 1529, babban jigo, na ekklesiya da kuma littattafai na Paris, “ya kafa kwatanci ma mutanen 1793 na murkushe maganar wadanda ke bakin mutuwa a dakali.”BJ 216.3

    An murde wuyan Berquin ne, sa’an nan aka kona gawarsa. Labarin mutuwarsa ya jawo bakin ciki ga abokan Canjin ko ina a Faransa. Amma kwatancinsa bai bata ba. Shaidun gaskiyan suka ce: “Mu ma muna shirye mu gamu da mutuwa cikin farin ciki, muna kafa idanunmu kan rai da ke zuwa.”BJ 216.4

    Lokacin zaluncin Meaux, an hana mallaman sabuwar bangaskiyar lasin na yin wa’azi, suka kuwa koma wadansu wurare. Daga baya Lefever ya je Jamus. Farel ya koma kasarsa a gabashin Faransa don baza hasken a kasan da ya girma. Lokacin an rigaya an sami labarin abin da ke faruwa a Meaux, kuma gaskiyan da ya koyar da himma, ba tsoro, ta sami masu sauraro. Nan da nan shugabanni suka taso za su rufe masa baki, aka kore shi daga birnin. Ko da shike bai iya ci gaba da aikin a fili ba, ya shiga kauyuka yana koyarwa a gidajen mutane da filaye na gonaki, yana kwana kuma a dazuka ko kogunan duwatsu inda ya rika zuwa lokacin kuruciyarsa. Allah yan shirya shi don manyan jarabobi ne. Ya ce: “Giciye ad zalunci da kullekullen Shaitan da aka gargade ni akai sun faru; suna da zafi ma fiye da yadda ni kai na zan iya jimrewa; amma Allah Uba na ne; Ya tanada, kuma kullum zai rika tanada mani karfin da ni ke bukata.”BJ 217.1

    Kamar zamanin manzanin, zalunci “ya kara ci gaban bishara ne.” Filibbiyawa 1:12. Da aka kore su daga Paris da Meaux, “Su fa da suka waste suka yi tafiya ko ina, suna wa’azin Kalmar.” Ayukan 8:4. Haka ne kuma hasken ya shiga laarduna da dama na Faransa. BJ 217.2

    Allah Yana kan shirya ma’aikata dai don fadada aikinsa. A wata makaranta a Paris, an yi wani saurayi mai basira da ladabi, wanda ke da alamar zama mai-zurfin tunani, ga kuma halin kirki da ilimi da ibada. Madaukakiyar iyawarsa da aikinsa sun ba shi farin jini a kolejin, aka kuma kau da shakka cewa John Calvin zai zama daya daga cikin mafi kwarewa da daukaka na masu kare ekklesiya. Amma tsirkiyar hasken Allah ta huda yawan ilimi da camfi da aka kange Calvin a ciki. Ya ji labarin sabuwar koyaswar da fargaba, ba tare da shakkar cewa wutar da aka ba masu riddar ta cancance su ba. Duk da haka, babu shiri aka kawo shi fuska da fuska da riddar, aka kuma tilasta shi ya gwada karfin tauhidin Rum don karawa da koyaswar masu Kin ikon paparuma.BJ 217.3

    Wani dan-uwan Calvin da ya zama dan Canjin, yana Paris. Shi da Calvin sukan rika tattauna al’amuran da ke damun addinin Kirista. Olivetan dan Canjin ya ce: “Akwai addinai biyu a duniya. Kashi na daya shi ne wadanda mutane suka kirkiro, kuma cikinsu duka, mutum ne yakan ceci kan sa ta wurin al’adu da kyawawan ayuka; na biyu din shi ne addinin nan daya da Littafi ya bayana, wanda ke koya ma mutum ya nemi ceto ta wurin alherin Allah kadai kyauta.”BJ 218.1

    Calvin ya amsa: “Ba na son sabobin koyaswoyin nan naka; kana tsammani duk rayuwa ta ina kuskure ne? Amma an ba shi tunani a zuciyarsa wanda bai iya watsarwa da sauki ba. A dakinsa, ya yi bimbini game da kalmomin dan-uwan nasa. Jin laifin zunubinsa ya rike shi sosai, ya ji kan shi, ba shi da matsakanci, a gaban Mai-shar’ia Mai-tsarki. Tsakanin tsarkaka da ayukan nagarta da al’adun ekklesiya duka ba su da ikon yin kafara don zunubi. Bai ga komi a gabansa ba sai duhun yakan kauna. A banza masanan ekklesiya suka yi kokarin magance damuwarsa. Furta zunubi da wahal da kai don samun gafara, duk basu biya bukata ba; basu sasanta mutum da Allah ba.”BJ 218.2

    Yayin da yake ci gaba da famar banzan nan, ya ziyarci wani dandali, sai ya tarar ana kone wani mai ridda. Ya cika da mamakin salamar day a gani a fuskar mutumin. Cikin azabar mumunan mutuwan nan, kuma kalkashin hukumcin eklesiya, mutumin ya nuna bangaskiya da karfin zuciya da dalibin nan Clavin ya bambanta da nashi fid da zuciya da kuma duhun nan, alhali yana rayuwar cikakkiyar biyayya ga ekklesiya. Ya san cewa masu riddan nan sun kafa bangaskiya kan Littafin ne. Ya kudurta zai yi nazarinsa don gano asirin farin cikinsu. BJ 218.3

    Cikin Littafi, ya sami Kristi. Ya ce: “Ya Uba, hadayarsa ta gamsar da fushin Ka; jininsa ya wanke dauda ta; Giciyensa ya dauki la’ana ta; mutuwarsa ta yi kafara domi na. Mun shirya ma kanmu wauta da yawa marasa anfani, amma kai ka sa maganar aka a gaba na kamar fitilla, kai kuma ka taba zuciya ta, domin in yi kyamar kowane abu, sai dai cancantar Yesu.”BJ 219.1

    Ilimin da Calvin ya samu na zama priest ne. Yana dan shekara goma sha biyu kadai aka sa ya zama mai lura da wata karamar ekklesiya, kuma bishop ya aske kansa bisa ga kaidar ekklesiya. Ba a shafe shi ba, kuma bai rigaya ya cika sharuddan priestanci ba, amma ya zama limami shi ma, ana kiransa da sunan aikinsa, yana kuma karban alawas don aikin.BJ 219.2

    Yanzu, da shike ya ga cewa ba zai taba zama priest ba, sai ya shiga makarantar aikin lauya, amma ya watsar kuma, ya kallafa ransa ga bishara. Amma kuma bai so ya zama mai koyar ma jama’a ba. Shi asalinsa mai kunya ne, ya kuma damu da nauyin aikin, ya so ya dukufa ga nazari. Rokon abokansa daga bisani dai ya sa shi ya yarda. Ya ce: “Abin mamaki ne a girmama dan talaka haka da irin wannan martabar.”BJ 219.3

    Calvin ya shiga aikinsa shuru, kalmominsa kuma kamar raba ce mai fadowa don mayar ma kasa da karfinta. Ya bar Paris, sai ya koma wani gari a wani lardi da ke kalkashin gimbiya Margaret, wadda sabo da kaunar bishara ta fadada tsaron ta zuwa ga almajiran bisharar. Calvin dai matashi ne a lokacin, mai ladabi da gaskiya kuma. Ya fara aikin sa da mutanen a gidajensu ne. Sa’an da mutanen gidan suka kewaye shi, yakan karanta masu Littafi ya bude masu gaskiyar ceto. Wadanda suka ji sakon sukan kai ma wadansu kyakyawar labarin, ba da jimawaba kuwa mai koyaswar ya zarce birnin, ya kai kauyuka da garuruwan da ke kewaye. Ya shiga manyan gidaje da kanana, ya kuma ci gaba yana kafa harsashen ekklesiyoyi da za su haifar da shaidun gaskiyar. BJ 219.4

    Bayan watanni kadan, ya sake zuwa Paris. An rika samun damuwa tsakanin masana. Nazarin harsuna na dai ya kai mutane ga Littafin, kuma da yawa wadanda gaskiyar ta ba ta taba su ba, yanzu kuwa suka fara tattauna su, har ma suna mahawara da jarumawan tsarin Rum. Ko da shike Calvin kwararren mai mahawara ne a fagen tauhidi, yana da manufar da ta fi mallaman makarantan nan masu surutu. An rigaya an motsa zukatan mutane, yanzu kuma lokaci ya yi da za a bude masu gaskiyar. Yayin da manyan dakunan taruwar jami’o’in su ke cika da hayanniyar mahawarar tauhidi, Calvin yana zuwa gida gida yana koya ma mutane Littafin, yana kuma yi masu magana game da Kristi giciyayye. BJ 220.1

    Cikin alherin Allah, Paris ta sake samun bishara. An rigaya an ki sakon Lefevre da Farel, amma dukan sassan mutanen babban birnin sun sake jin sakon. Sarkin, sabo da dalilai na siyasa, bai rigaya ya goyi bayan Rum gaba daya sabanin Canjin ba. Margaret ta ci gaba da begen cewa Kin ikon paparuma zai sami ci gaba a Faransa. Ta kudurta cewa za a yi wa’azin sabuwar bangaskiyar a Paris. Lokacin da sarkin ba ya gari, ta umurci wani limami mai-kin ikon paparuma ya yi wa’azi a birnin. Da shike shugabannin ‘yan paparuma sun hana yin hakan, gimbiyar ta bude fada domin yin wa’azin. Aka shirya wani gefe ya zama wurin karantarwar, aka kuma sanar da cewa kowace rana, daidai wani lokaaci, za a yi wa’azi, kuma an gayyaci dukan mutane su hallarta. Ba dakin karantarwar kadai ba, har da sauran dakunan kewaye suka rika cika. Kowace rana dubbai sun rika taruwa: fadawa da manyan kasa, da lauyoyi da attajirai, da masu aikin hannu. Maimakon sarkin ya hana taruwar, sai ya umurta aka bude majami’u biyu na Paris. Birnin bai taba motsuwa da maganar Allah hakanan ba. Kamar ruhun rai daga sama ne aka hura ma mutanen. Kamewa, tsabta, oda da kokari ga aiki suka sauya shaye shaye da nishadi da fada da zaman banza.BJ 220.2

    Amma shugabannin ekklesiyar basu zauna kawai ba. Duk da haka sarkin ya ki hana wa’azin, sai suka koma ga jama’a. Sun yi iyakar kokarinsu don motsa tsoro da kiyayya da tsanancin ra’ayin jahilan nan masu camfi. Sa’an da ta yarda da mallamanta na karya, Paris, kamar Urushalima ta da, ba ta san lokacin ziyartarta ba, ko kuma al’amuran salamarta. Shekara biyu ana wa’azin maganar Allah a babban birnin; amma yayin da akwai da yawa da suka karbi bisharar, yawancin mutane suka ki ta. Francis ya nuna ba da yanci don cika burin kansa ne, ‘yan paparuma kuma suka yi nasarar samun ci gaba. Aka sake rufe masujadu, aka kuma kafa wurin kashe masu laifi.BJ 221.1

    Calvin dai yana Paris, yana shirya kansa ta wurin nazari da bimbini da addu’a don aikin da ke gabansa, yana kuma ci gaba da baza hasken. Mahukumta suka kudurta kone shi. Yayin da ya dauka cewa inda ya boye kansa babu hatsari, sai ga abokansa a gurguje da labarin cewa hafsoshi suna hanyar zuwa su kama shi. Daidai lokacin aka ji an buga kofar waje da karfi sosai. Babu lokacin jinkiri. Wadansu abokansa suka tare hafsoshin a kofa yayin da wadansu suka taimake shi ya fita ta taga, nan da nan ya gudu zuwa bayan birnin. Daga masaukin da ya samu a gidan wani lebura abokin Canjin, ya canja kamaninsa da tufafin leburan, ya rataya garma a kafadarsa, ya kama hanya. Da ya nufi Kudu, sai ya sake samun mafaka a wata kasa da ke kalkashin ikon Magaret kuma.BJ 221.2

    A nan ya yi ‘yan watanni kalkashin tsaron abokai masu iko, yana kuma ci gaba da nazari. Amma zuciyarsa tana wajen kai bishara Faransa dai, kuma dole ya fara aiki nan da nan. Da zaran guguwar ta huce, ya koma Poitiers da aikinsa, inda akwai jami’a, kuma inda aka rigaya aka karbi sabuwar koyaswar. Mutane daga kowane gefe suka saurari bishara da murna. Ba a yi wa’azin a fili ba, amma a gidan babban majistare, da masaukin shi Calvin, wani lokaci kuma a wurin hutawa na jama’a, Calvin yakan bude kalmomin rai madawami ga masu ji. Bayan wani lokaci, yayin da yawan masu sauraro ya karu, aka ga zai fi kyau a rika taruwa a bayan birnin. Sai aka zabi wani kogo a gefen wani kwazazzabo, inda itatuwa da duwatsu suka kara inganta mabuyar. Kananan kungiyoyin jama’a sukan bi ta hanyoyi dabam dabam zuwa wurin. A wannan wurin, a kan karanta Littafin ga jin mutane a kuma fassara shi. Nan ne masu Kin ikon paparuma a Faransa suka ci jibin su na farko. Daga wannan karamar majami’a aka aika da amintattun masu wa’azi zuwa wadansu wurare.BJ 222.1

    Calvin ya sake komawa Paris. Bai bar begensa cewa al’ummar Faransa baki daya za ta karbi Canjin ba har yanzu. Amma ya tarar da kowace kofar aiki a rufe. Koyar da bishara hakika kam hanya ne kai tsaye zuwa mutuwa. A karshe dai ya kudurta zai je Jamus. Yana barin Faransa kuwa, guguwa ta abko ma masu Kin ikon paparuma, ta yadda, da yana wurin, da lallai ya hallaka.BJ 222.2

    ‘Yan Canjin a Faransa, da kosawar ganin kasarsu tana tafiya daidai da Jamus da Switzerland, suka kudurta kai ma camfe camfen Rum babban bugu da zai falkas da dukan al’ummar. Don haka takardun sanarwa masu sokar mass suka bazu cikin dare daya, aka manna su ko ina a Faransa. Maimakon kawo ci gaban Canjin, wannan mataki na himma, amma bisa kuskure, ya jawo hasara ne kawai, ba kan masu aikata shi kadai ba, amma kan magoya bayan sabuwar koyaswar, ko ina a Faransa. Ya ba ‘yan Rum din abin da suka dade suna nema, watau dalilin bidar hallakawar masu ridda kwata kwata a matsayin masu tashin hankali, mumunan hatsari kuma ga gadon sarauta da zaman lafiyan al’ummar.BJ 222.3

    Wani wanda ba a san ko aboki ne ko makiyi ba, ya manna takardar sanarwan nan daya a kofar sarki. Sarkin kuwa ya fusata matuka. A wannan takardar aka yi ta sokar camfe camfen da aka kwashe sararraki da dama ana daukakawa. Kuma karfin halin kutsawa fadar sarki da kalaman nan ma ya ta da fushin sarkin. Cikin mamakinsa, sarkin ya tsaya shuru na dan lokaci, yana rawan jiki. Sa’an nan ya ce: “Bari a kama dukan wadanda ake zato ‘yan Luthanci ne. Zan hallaka su duka.” Sarki ya kudurta goyon bayan Rum gaba daya ke nan.BJ 223.1

    Nan da nan aka dauki matakan kama kowane mai ra’ayin Luther a Paris. Aka kama wani dan taliki mai aikin hannu, wanda ya saba kiran masu bangaskiya zuwa wuraren taronsu, aka tilasta shi nuna ma ‘yan sakon ‘yan paparuman gidan kowane mai Kin ikon paparuma a birnin. Jikin shi ya yi sanyi da wannan, amma daga baya tsoron mutuwa ta wurin wuta ya sha kansa, sai ya yarda ya zama mai bashewar ‘yan-uwansa. Morin, dansandan ciki na sarkin, tare da priestoci da masu rikon turaren hayaki, da masu zuhudu da sojoji, tare de mai bashewan, suka bi titunan birnin. An yi jerin nan don girmama mass mai-tsarkin nan ne, domin a nemi gafara sabo da wulakancin da aka yi ma mass din. Amma jerin gwanon nan tana da muguwar manufa a boye kuwa. Sa’an da aka kai gidan mai bin ra’ayin Luther, mai bashewan yakan yi wata alama, amma ba magana, sai a tsayar da jerin gwanon, a shiga gidan, a ja iyalin zuwa waje, a kuma daure su da sarka, sa’an nan sai a ci gaba da nema sauran su kuma. “Basu bar wani gida babba ko karami ba, ko kolejojin Jami’ar Paris.... Morin ya sa dukan birnin ya girgiza.... Aka shiga lokaci na ban razana kwarai.” BJ 223.2

    An kashe mutanen da azabar mugunta ne, aka umrta cewa a rage wutar domin a tsawaita azabarsu. Amma sun mutu masu nasara ne. Amincinsu bai raunana ba. Salamarsu kuma ba ta ragu ba. Masu tsananta masu da suka kasa raunana su suka ji kawai an ka da su. “An baza dakalin kisan ko ina a Paris, kuma aka rika kisa kowace rana, bi da bi, don tsawaita fallasa munin ridda. Amma a karshe dai, bishara ce ta yi riba. Abin da aka yi ya sa dukan Paris ta ga irin mutanen da sabobin koyaswoyin za su iya haifarwa. Babu bagadin da ya kai tudun gawayen da aka tara kasancewa dandalin wa’azi. Murna da salaman da suka haskaka fuskokin mutanen nan lokacin wucewarsu zuwa wurin mutuwarsu, da jaruntakarsu yayin da suke tsaye a tsakiyar wutar, tawali’un gafararsu, sun canja fushin wadansu zuwa tausayi, kiyayya kuma zuwa kauna, wanda kuma da babban murya ya jawo hankula zuwa fifikon bishara.”BJ 224.1

    Priestocin, don kara fusata mutane, suka yi ta baza zarge zarge mafi muni game da masu Kin ikon paparuma. Aka zarge su cewa sun shirya kashe dukan yan katolika, su hambarar da gwamnati, su kuma kashe sarki. Ko alamar shaidar zargin nan babu. Duk da haka, annabce annabcen muguntan nan sun cika, amma ta hanyoyi dabam. Zaluncin da ‘yan Katolika suka yi ma masu Kin ikon paparuma sun tattaru don lokacin ramuwa, kuma daruruwan shekaru daga baya suka haifar da hallakan da suka ce an shirya ma sarki da gwamnatinsa da talakawansa kuma, amma kafirai ne suka kawo shi tare da ‘yan paparuma kansu. Ba kafawar Kin ikon papruma ba, amma danne shi ne ya jawo ma Faransa masifun nan, shekaru dari uku daga baya.BJ 224.2

    Zato, rashin yarda, da tsoro mai yawa suka mamaye dukan mutane. Cikin wannan yanayi aka ga yawan tasirin da koyaswar Luther ta yi ga zukatan mutane shahararru ta fanin ilimi da masu martaba da halin kirki. Jima kadan sai aka iske ma’aikata masu rike manyan matsayi sun bar aiki. Masu aikin hannu, masu buga littattafai, ‘yan makaranta, mawallafa, shehunan mallamai a jami’o’i, har da fadawa ma, suka salwanta. Daruruwa suka gudu daga Paris, suka zama yan gudun hijira daga kasarsu ta gado, ta haka kuma yawancinsu suka nuna goyon bayansu ga sabuwar bangaskiyar. ‘Yan paparuman suka duba kewaye da su, da mamaki, suka gane mutane da yawa masu ridda da suka dade suna zama tare da su. Fushinsu ya huce kan jama’a da yawa marasa galihu masu ridda da ke kalkashin ikonsu har wannan lokacin. Gidajen kaso suka cika, iska kanata kuma ta duhunta da hayakin wutar da aka kunna kan masu goyon bayan bishara. BJ 225.1

    Da Francis I ya daukaka kansa don kasancewa shugaba cikin babban aikin falkas da ilimi a farkon karni na goma sha shida. Yakan ji dadin tara masana a fadarsa, daga kowace kasa. Son iliminsa da kyamar jahilci da camfin masu zaman zuhudun nan ne ya jawo irin zarafin da aka ba Canjin. Amma sabo da himmar batar da ridda, wannan shugaban ya yi dokar da ta hana buga littattafai ko takardu ko ina a Faransa! Francis I daya, daga misalai da yawa ne na cewa ilimi bai hana rashin sassauci da zalunci game da addini ba.BJ 225.2

    Faransa ta shirya za ta yi bukin shigar ta dungum cikin murkushe Kin ikon papapruma. Priestocin suka bidi cewa harin da aka kai ma Allah ta wurin sokar mass za a wanke shi da jini, kuma wai sarkin, a mdadin mutanensa, zai ba da goyon bayan sa ga aikin nan a gaban jama’a. BJ 225.3

    An zabi ran 21 ga watan Janairu, 1535 ne don bukin. An rigaya an motsa tsoron camfi da kiyayyar mutanen. Paris ta cika da jama’a da suka cika tituna daga kauyukan kewaye. An shirya fara ranar da babban jerin gwano ne mai ban sha’awa. “Gidajen gefen hanyan da za a bi suka cika da ado na ban mamaki, aka kuma kafa bagadi nan da can.” A gaban kowace kofa akwai tocilan da ke haskakawa don girmama mass din. Kafin wayewan gari, masu jerin gwanon sun taru a fadar sarki. “Da farko akwai tuta da giciye na kowane parish; bayansu sai ‘yan kasar, suna tafiya su biyu biyu, suna rike kuma da tocilan, kowane dayansu.” Kungiyoyi hudu na ma’aikatan ekklesiyar suka biyo, kowace daya da irin tufafinta. Sa’an nan babban tarin sifofi ya biyo baya. Biye da wadannan manyan shugabannin ekklesiya cikin tufafinsu masu launi iri iri da kayan ado, masu haskakawa, abin kallo. BJ 226.1

    “Bishop din Paris ne ya rike jibin a kalkashin wata babbar laima mai gwafa hudu da ‘ya’yan sarki su hudu suka rike.... bayan jibin, sarki ya biyo ... Ranan, Fancis I bai daura rawani ba, bai kuma sa kayan sarauta ba.” Da kai a bude, idanunsa suna kallon kasa, cikin hannunsa kuma ga kyendur da haskensa, sarkin Farnsa ya bayana “cikin yanayin mai tuba.” A kowane bagadi, yakan sunkuya don ban girma, ba don zunuban da sun kazanar da ransa ba, ko kuma jinin marasa laifi da ya zubar ba, amma wai don mumunan zunubin talakawan sa da suka soki mass. Bayansa sarauniya ta biyo da manyan jami’an kasa, suna tafiya biyu biyu su ma; kowa da tocilan da aka akunna. BJ 226.2

    Cikin hidimomin ranan, sarkin ya yi ma manyan ma’aikatan kasar jawabi a babban dakin taro na fadar bishop. Da bakinciki a fuskarsa ya bayana a gaban su, kuma da kalmomi na kaifin baki ya yi bakin cikin “laifi da sabo, da ranar bakin ciki da ban kunya” da ta abko ma al’ummar. Ya kuma kira ga kowne talaka mai-biyayya ya taimaka wajen murkushe annobar riddan nan da ke barazanar rushe Faransa. Ya ce: “Kamar yadda, da gaske ni ne sarkinku, idan na sa wata gaba ta ta harbu da wannan mumunar rubewar, zan ba ku ita ku yanke.... Biye da haka, in na g a daya daga yara na ya kazamtu da shi, ba zan bar shi ba, ... Ni da kai na zan mika shi, zan kuma mika shi hadaya ga Allah.” Hawaye sun bi maganarsa, dukan taron kuwa suka yi kuka, suna cewa da murya daya: “Za mu rayu mu mutu don addinin Katolika!”BJ 226.3

    Duhun al’ummar ya yi muni sosai, domin taka hasken gaskiya. Alherin da ke kawo ceto ya bayana, amma Faransa, bayan ta ga ikon sa da tsarkinsa, bayan kyaunsa na samaniya ya jawo dubbai, bayan birane da kauyuka sun haskaka da kyallinsa, ta juya ta zabi duhu maimakon haske. Sun kawar da kyautar sama din bayan an ba su ita. Suka kira nagarta mugunta, mugunta kuma nagarta, har sai da suka sami sakamakon rudin kansu da suka yi. Yanzu, ko da shike suna iya gani da gaske kamar suna yi ma Allah ne hidima ta wurin tsananta ma mutanensa, duk da haka, gaskiyan zatonsu bai mai da su marasa laifi ba. Hasken da da zai cece su daga yaudara, daga kazanta da laifn jini, sun ki shi da yardar ransu.BJ 227.1

    An dauki rantsuwar murkushe ridda a cikin majami’an nan ne da, kusan shekara dari uku daga baya, al’umman nan da ta ki Allah Mai-rai, ta daukaka Allahan Tunani a ciki. An sake yin jerin gwanon, wakilan Faransa kuma suka fito don fara aikin da suka rantse za su yi. “An kafa dakali na katako kusa kusa da juna, inda za a kone wadansu masu Kin ikon paparuma da ransu, aka kuma shirya cewa za a sa wuta a kiraren, da zaran sarki ya iso, kuma cewa jerin gwanon jama’a za su tsaya su kalli kisar.” Zaluncin da shaidun nan na Kristi suka sha ba shi da dadin fadi, sabo da yawan muninsa; amma wadanda aka kona din basu nuna rashin karfin hali ba. Da aka matsa ma wani ya janye, ya ce: “Na gaskata abin da annabawa da manzani suka yi wa’azinsa ne kawai da abin da dukan tsarkaka suka gaskata. Bangaskiya ta tana da dangana ga Allah, kuma za ta jimre dukan ikokin lahira.”BJ 227.2

    Akai akai, jerin gwanon suka tsaya a wuraren zaluncin. Da suka kai inda aka fara tafiyar, a fadar sarki, jama’a ta waste, sarki da ‘yan ekkledsiya kuma suka tafi, da gamsuwa game da yadda al’amura suka gudana a ranan, suka kuma gode ma kansu cewa aikin da suka fara yanzu zai ci gaba har sai an hallaka ridda gaba daya. BJ 228.1

    Bisharar salama da Faransa ta ki, hakika za a rushe ta, kuma sakamakon hakan mumuna ne. Ran 21 ga Janairu, 1793, shekara dari biyu da hamsin da takwas daga ranan da Faransa ta kudurta tsananta ma ‘yan Canji, wani jerin gwano da wata manufa dabam ya bi titunan Paris kuma, “Sarkin ne kan gaba kuma; akwai kuma hayanniya da surutu; an kuma ji kukan mutane marasa laifi; akwai kuma dakali na katako, aka kuma rufa al’amuran wannan ranar da kashe kashe; Loius XVI ne, yana gardama da masu kulle shi a kurkuku da masu kisasa, suka kawo shi wurin akwatin, aka kuma danne shi a wurin aka rike har sai da gatarin ya fado, yankakken kan sa kuma ya gungura kan dakalin katakon.” Kuma ba sarkin ne kadai ba, kusa da wurin ma mutum dubu biyu da dari takwas aka hallaka hakanan a zamanin Mulkin Ta’addanci.BJ 228.2

    Canjin ya mika ma duniya budadden Littafi, ya bayana kaidodin dokar Allah, ya kuma nuna muhimmancin ta ga lamirin mutane. Allah Ya bayana ma mutane dokoki da kaidodin sama. Allah fa Ya ce: “Ku kiyaye su fa ku aikata; gama hikimarku da azancinku kenan a idanun al’ummai wadanda za su ji dukan wadannan farillai, za su kwa che. Hakika wannan babbar al’umma mai-hikima che mai-azanchi.” Kubawa 4:6. Sa’an da Faransa ta ki kyautar sama, ta shuka irin rudami da rushewa ne; dole kuwa sanadi da sakamako su haifar da Babban Tawaye da Mulkin Ta’addanci.BJ 228.3

    Da dadewa kafin zaluncin da takardun sanarwan da aka yi ta likawa a bango suka jawo, mai karfin zuciyan nan Farel mai-kwazo, ya gudu daga kasar sa ta haihuwa tilas. Sai ya je Switzerland. Ta wurin aikinsa da ya goyi bayan Zwingli, ya taimaka wajen goyon bayan Canjin. Nan ya karasa shekarunsa na karshe, duk da haka ya ci gaba da tasiri sosai ga Canjin a Faransa. Cikin shekarun farko na hijirarsa, kokarinsa na baza bishara a kasar sa ta gado ne. Ya ci lokaci mai yawa yana wa’azi ga yan kasarsa, kusa da kan iyaka, inda a natse, ya kalli jayayyar, ya kuma taimaka ta wurin kalmominsa na karfafawa da shawara kuma. Da taimakon wadansu ‘yan gudun hijiran aka juya rubuce rubucen ‘yan Canjin Jamus zuwa harshen Faransa. An rika ba masu sayarwa takardun, kan kurdi mara yawa, ta haka anfanin aikin ya taimaka masu suka ci gaba da aikin.BJ 229.1

    Farel ya shiga aikinsa a Switzerland da sunan cewa shi mallamin makaranta ne. Sa’anda ya koma wani parish na kauye, sai ya dukufa ga karantar da yara. Ban da ababan da aka saba koyarwa, ya rika koyar da gaskiya na Littafi da dabara, da begen cewa ta wurin yaran zai sami iyayen. Akwai wadanda suka gaskata, amma priestoci suka shigo domin su tsayar da aikin, aka kuwa zuga kauyawa masu camfi suka yi jayayya da aikin. Priestocin suka ce: “Wannan ai ba bisharar Kristi ba ce, ganin cewa w’azin ta ba ya kawo salama sai yaki.” Kamar almajiran farko, sa’anda aka tsananta masa a wani birni, yakan gudu zuwa wani. Daga kauye zuwa kauye, daga birni zuwa birni, ya yi ta tafiya a kasa, yana jimre yunwa da sanyi da gajiya, kuma ko ina ya je dai, a bakin ransa. Ya yi wa’azi a kasuwanni da majami’u, wani lokaci ma a manyan majami’un. Wadansu lokuta, a majami’un ba ma wadanda za su ji wa’azin; wadansu lokuta a kan bata wa’azin da ihu da holo; kuma akan fizge shi da karfi daga bagadin. Fiye da sau daya yan iska suka tare shi suka yi masa duka har kusan mutuwa. Duk da haka dai ya ci gaba. Ko da shike an dinga koran sa akai akai, da naciya dai ya dinga komawa inda aka kore shi; daya bayan daya kuwa ya yi ta ganin birane da garuruwan da suka taba zama cibiyoyin ‘yan paparuma suna karban bishara. Karamar parish inda ya fara aiki ta karbi sabuwar bangaskiyar. Biranen Morat da Neuchatel ma suka yi watsi da al’adun Rum, suka kuma cire gumaka daga majami’unsu.BJ 229.2

    Farel ya dade yana so ya kafa tutar Kin ikon paparuma a Geneva. Idan aka sami wannan birnin, zai zama cibiyar Canjin a Faransa, da Switzerland, da Italiya. Da wannan manufa a gabansa ya ci gaba da aikinsa har sai da, da yawa cikin garuruwa da kauyuka kewaye suka karbi sakon. Sa’an nan, tare da wani abokinsa, ya shiga Geneva. Amma wa’azi biyu kadai aka yarda mashi ya yi sa’an da prietocin suka kasa sa mahukuntan kasar su hukumta shi, suka kira shi gaban majalisar ekklesiya, inda suka je da makamai a boye cikin rigunansu, da niyyar dauke ransa. A waje, yan iska cike da fushi suka taru da takubba da kulake domin tabbatar da kutuwarsa, ko da ya tsere ma majalisar. Amma kasancewar majistarori da dakaru dauke da makamai ya cece shi. Washegari da sassafe, aka raka shi da abokinsa har ketaren korama zuwa inda babu hatsari. Karshen yunkurin sa na farko na kai bishara Geneva kenan.BJ 230.1

    Don gwaji na biye an zabi wani matashi ne wanda ganin tawali’un sa ma ya sa har masu cewa suna goyon bayan Canjin ma suka dinga rena shi. Amma me wannan zai iya yi inda aka ki Farel? Ta yaya mai kankantar karfin zuciya da kwarewa zai jimre guguwar da ta tilasta mafi karfi da karfin zuciya ya gudu? “Ba ta wurin karfi ba, ba kuwa ta wurin iko ba, amma ta wurin ruhuna, in ji Ubangiji mai-runduna.” Zechariah 4:6. “Amma Allah Ya zabi kuma raunana na duniya, domin shi kunyatadda masu karfi.” “Domin wautar Allah ta fi mutane hikima; rashi karfin Allah kuma ya fi mutane karfi.” Korinthiyawa I, 1:27, 25.BJ 230.2

    Froment ya fara aikin sa kamar mallamin makaranta ne. Gaskiyan da ya koya ma yaran a makaranta sukan maimaita su a gidajensu. Ba da jimawa ba, iyaye suka fara zuwa sauraron fassarar Littafin, har ajin makarantar ya cika da masu sauraro. Akan rarraba Sabon Alkawali da majallu kyauta, suka kuwa kai wurin mutane da yawa da basu isa su zo jin sabobin koyaswoyin a fili ba. Bayan wani lokaci, wannan ma’aikacin ma an tilasta shi ya gudu, amma gaskiyar da ya koyar ta rigaya ta mallaki zukatan mutane. BJ 230.3

    An dai shuka Canjin, ya kuma ci gaba yana kara karfi da fadi kuma. Masu wa’azin suka dawo, kuma ta wurin aikinsu, sujadar masu Kin ikon paparuma ta kafu a Geneva. BJ 230.4

    Birnin ya rigaya ya rungumi Canjin lokacin da Calvin, bayan kai da komowa dabam dabam da canje canje iri iri, ya shigo birnin. Da ya dawo daga ziyarar wurin da aka haife shi, yana kan hanyarsa zuwa Basel, sai ya lura cewa hanya mikakkiya ta cika da dakarun Charles V, wannan kuwa ya tilasta shi bin doguwar hanya mai kwane kwane zuwa Geneva. BJ 231.1

    A wannan ziyarar Favel ya gano hannun Allah. Ko da shike Geneva ta rigaya ta karbi sabuwar bangaskiyar, duk da haka akwai babban aiki da ya rage a yi a wurin. Ba kungiyoyi ake tubarwa zuwa wurin Allah ba, mutane daya daya ake tubarwa zuwa wurin Allah; dole a aiwatar da aikin Canjin a cikin zuciya da lamiri ta wurin ikon Ruhu Mai-tsarki, ba ta wurin dokokin majalisu ba. Yayin da mutanen Geneva suka rigaya suka yi watsi da ikon Rum, basu shirya ta hakanan su rabu da miyagun halayyan da suka yawaita a zamanin mulkinta ba. Tabbatar da kaidodin bishara a nan, a kuma shirya mutanen nan su cika matsayin da Allah ke bidarsu su dauka, ba kananan al’amura ba ne. BJ 231.2

    Farel ya tabbata cewa Calvin mutum ne wanda zai iya hada kai da shi cikin aikin nan. Cikin sunan Allah ya umurci saurayin ya yi aiki a nan. Calvin ya ja baya sabo da mamaki. Ga shi mai- yawan tsoro ne da son salama, ya yi dari dari da zancen saduwa da mutanen Geneva din nan masu karfin zuciya da ‘yancin kai, har ma da son gwada karfi. Karancin lafiyarsa, hade da halayyan sa na yawan nazari, suka sa shi ya bidi yin ritaya. Da shike ya gaskata cewa da alkalaminsa zai fi yin aikin canjin, ya yi marmarin samun wurin da babu surutu domin yin nazarin, ta wurin wallafa littattafai da kasidu da dai sauran su kuma zai rika koyarwa ya kuma gina ekklesiyoyin. Amma umurnin Farel ya zo masa kamar kira ce daga sama, kuma bai isa ya ki ba. Ya ce ya ga kamar “hannun Allah ya mike sama, ya kama shi, ya kuma kafa shi babu kawuwa a wurin da ya kosa ya bari.”BJ 231.3

    A wannan lokacin, manyan hadaruka sun kewaye aikin Kin ikon paparuman. Haramce haramcen paparuma sun rika taruwa kan Geneva, kuma manyan kasashe suka yi masa barazanar hallaka shi. Ta yaya wannan karamin birnin zai nuna tsayayya ga mulkin nan mai yawan iko da yakan tilasta sarakuna su yi biyayya? Ta yaya za ta yi tsayayya da dakarun manyan kasahen duniya? BJ 232.1

    Ko ina cikin Kirista, Kin yarda da ikon paparuma ya gamu da kiyayya daga manyan magabta. Bayan nasarorin farko na Canjin sun wuce, Rum ta tara sabobin dabaru da begen hallaka Canjin. A wannan lokacin aka kafa kungiyar Jesuits, kungiya mafi mugunta da zalunci da karfi daga cikin jarumawan paparuma. Da shike sun yanke daga danantaka na duniya da ababan burin na mutumtaka, sun mutu ga marmari irin na mutumtaka, an kuma kashe tunani da lamiri kwata kwata, basu san wata kaida ko dangantaka ba, sai ta kungiyarsu, aikin su kadai kuma shi ne fadada ikon kungiyar. Bisharar Kristi ta sa masu bin ta suka iya jimre hadari da wahala, ba tare da damuwa game da sanyi ko yunwa ko aiki ko talauci ba, domin daga tutar gaskiya ko ana horo da kurkuku da kisa. Don yin fada da ‘yan Canjin nan, Jesuits suka motsa mabiyansu da matsanancin ra’ayin da ya sa suka iya jimre irin matsaloli dayan, su kuma yi jayayya da ikokin gaskiya, da kowane irin rudu. Babu laifin da ya fi karfin aikatawarsu, ba rudin da ba za su iya yi ba, ba sake kaman da ba za su iya yi ba kuma. Da shike sun ranatse suka rungumi talauci da kaskantarwa har abada, nufinsu ne su tara dukiya da iko don anfani wajen hambarar da Kin ikon paparuma, da sake kafawar daukakar paparuma din.BJ 232.2

    Sa’an da suka fita a matsayin su na ‘yan kungiyar, sukan yafa kamanin tsarki, suna ziyartar kurkuku da asibitoci, suna taimakon marasa lafiya da matalauta, suna cewa sun rabu da duniya, suna kuma amsa sunan Yesu, wanda Ya dinga aikata nagarta. Amma kalkashin kyaun nan na waje, akan boye manufofi mafi-muni. Wata muhimmiyar akidar kungiyar ita ce cewa, sakamako da ta yi kyau, ko ta halin kaka. Ta wurin wannan akidar, karya da sata da rantsuwar karya da kisan kai suka karbu, har ma aka daukaka su, sa’an da suka biya bukatun ekklesiya. Kalkashin bad da kamani iri iri, yan Jesuits sukan rika shiga ma’aikatun gwamanti, har suna zama yan majalisun sarakuna, suna tsara manufofin kasashe. Suka zama barori domin su zama masu leken asirin iyayen-gijinsu. Sukan kuma bude kolejoji don yaran fadawa da na yayan sarakuna, da makarantu don talakawa; yaran masu Kin ikon paparuma kuma aka jawo su cikin kiyaye al’adun yanpaparuma. Dukan holewa da adon sujada ta Rum an shirya su ne don rikitar da tunani, da burge zuciya, ta haka kuwa ‘yancin da ubani suka yi fama suka zub da jini a kai, yaransu suka yin banza da shi. ‘Yan Jesuit sun bazu ko ina a Turai da sauri, kuma duk inda suka je, an sami falkaswar tsarin paparuma. BJ 233.1

    Don kara masu iko, aka ba da wani umurni da ya sake kafa tsarin Binciken nan. Duk da kin shi da aka yi ko ina, har ma a kasashen marasa rinjaye, ‘yan paparuma sun sake kafa mumunan cibiyan nan, aka kuma maimaita munanan laifuka a kurkukunsa na boye. A kasashe da yawa, dubbai kan dubban shahararrun ‘yan kasa, mafiya tsabta da martaba, mafiya hikima da ilimi, masu ibada da amintattun pastoci, yan kasa masu kuzari da kishin kasa, masanan gaske, masu baiwar zane zane, kwararrun masu aikin hannu: aka karkashe su, ko kuma aka tilasta su gudu zuwa wadansu kasashe.BJ 233.2

    Irin hanyoyin da Rum ta yi anfani da su kenan don bice hasken canjin, a janye Littafi daga wurin mutane, a kuma dawo da jahilci da camfin sararakin zamanun. Amma a kalkashin albarkar Allah da aikin masu martaban nan da Ya shirya su gaji Luther, ba a hambarar da Kin ikon paparuma ba. Ba a wurin taimako ko makamai na yaran sarakuna ya sami karfin sa ba. Kasashe mafi kankanta, alummomi mafi rashin daraja da karfi, suka zama wuraren da Kin ikon paparuma ya fi karfi. Dan kankanin Geneva din nan ne a tsakiyar manyan magabta masu shirin rushe shi; Holland ne a gabar tekun da ke Arewa da shi, yana fama da zaluncin Spain, wanda shi ne mulki mafi girma da wadata; Sweden din nan mara haske, sandararre, su ne suka samo ma Canjin nasarori. BJ 233.3

    Kusan shekara talatin Calvin ya yi ta aiki a Geneva da fari don kafa ekklesiya mai-bin halin kirki na Littafin, sa’annan kuma don ci gaban Canjin ko ina Turai. An sami la’ani game da hanyar shugabancinsa, kuma koyaswoyin shi sun kasance da kurakurai. Amma yana da hannu cikin koyar da gaskiya masu muhimmanci na musamman a zamaninsa, da karfafa kaidodin Kin ikon paparuma, sabanin hanzarin guguwar paparuma din, da kuma karyar da saukin kai da tsabtar rai a ekklesiyoyin da suka canja, maimakon girman kai da lalacewan da aka koyar kalkashin koyaswar Rum.BJ 234.1

    Daga Geneva, takardu da mallamai suka fita don shelar sabobin koyaswoyin. Ga wannan ne masu shan zalunci na dukan kasashe suka duba don koyaswa da shawara da karfafawa. Birnin Calvin ya zama mafakar yan Canjin dukan Yammacin Turai. Yayin da suke gudu daga guguwa da suka ci gaba har daruruwan shekaru, masu gudun suka zo kofofin Geneva. Ga yunwa ga raunuka ga rashin matsuguni, da rashin yan-uwa, aka marabce su da kyau, aka kuma lura da su sosai; da kuma suka sami gida a nan, suka albarkaci birnin ta wurin kwarewarsu, da iliminsu da ibadar su. Da yawa da suka nemi mafaka a nan suka koma kasashensu don yin jayayya da zaluncin Rum. Da John Knox da masu tsabar addini yan Ingila, da masu Kin ikon paparuma a Holland da Spain, da kuma Huguenots na Faransa da aka dauko daga Geneva, tocilan gaskiya don haskaka duhun kasashen su na gado. BJ 234.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents