Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
 • Results
 • Related
 • Featured
No results found for: "".
 • Weighted Relevancy
 • Content Sequence
 • Relevancy
 • Earliest First
 • Latest First
  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents

  FADIN ZUNUBI

  “Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba; amma dukan wanda ya fade su ya kwa rabu da su za ya sami jinkai.” Misalai 28:13.MK 31.1

  Sharudan samun jinkai daga Allah masu sauki ne, masu adilci. Ubangiji ba ya bukatar mu yi wasu ayuka masu tsannani domin mu samu gafarar zunubai. Ba lalai ba ne mu yi tafiya mai nisa domin yin haji, ko mu yi wancfansu ayuka masu wuya na tuba, ko mu kocd rayukammu ga Allah na sama ba, ko mu biya wani abu domin laifofimmu; amma shi wanda ya fadi zunubansa ya kuma rabu da su, zai samu jinkai.MK 31.2

  Yakubu Manzo ya ce “Ku fadi zunubanku ga juna fa, ku yi ma juna addu’a, domin ku warke.” Yakub 5:16. Ku fadi zunubanku ga Allah, wanda shi ne kadai ya iya gafarta su, laifofinku kuma ku facfa wa juna, Idan ka yi wa abokinka, ko makwabcinka laifi sai ka amsa laifinka, shi kuwa wajibi ne a gareshi ya yafe maka. Sai kuma ka nemi gafarar Allah, domin Shi dan-uwan nan naka da ka yi wa laifi dukiyar Allah ne, kuma a cikin yi wa dan-uwan nan naka lahani ka yi zunubi gaba da Mahallici da Mai-pansa. An kawo karar a gaban Matsakanci wanda “an jarabce shi ta ko wace fuska kamar mu, saidai banda zunubi,” kuma wanda yana “tabuwa da tarayyar kumamanchin mu,” Ibraniyawa 4:15 shi kuwa yana iya tsabtacewa daga ko wane tabo na rashin adilci.MK 31.3

  Wadannan da ba su kaskanta zukatansu gaban Allah ba ta wurin amsa laifofinsu, ba su cika abin da ake bukata na farko game da sharakin karba ba. Idan ba mu tuba a cikin ranmu akan abinda da baza mu taba ba, kuma idan ba mun fadi zunubammu cikin tawali’u na gaskiya da karayar ruhu domin zunubammu ba, ba mu kuma yi kyamar zunubammu ba, lallai ba mu taba bidar gafarar da gaskiya ke nan ba; idan kuwa ba mu taba bida ba, bamu taba samum salamar nan ta Allah ke nan ba. Dalili guda daya ne kadai da ya ke sa ba mu samun kwancewar zunubi, shi ne rashin yarda mu kaskanta zukatammu da bin sharadun Kalmar Allah na Gaskiya. Am ba da cikakken umurni game da wannan matsala. Fadin zunubi, ko a gaban jama’a, ko cikin boye, ya kamata ya zama na zuci, a kuma fade shi da yardan rai. Kada a iza mai zunubi ya fadi kamar cikin dole. Fadin znunbi wanda ya ke daga cikin tushen ran mutum ya fito, ya kan samu hanya zuwa wurin Allah mai jinkai mara iyaka. In ji Mai-Zabura, ya ce “Ubangiji yana kusa da masu karyayyar zuciya, kuma yana ceton irin wadanda su ke da ruhu mai tuba.” Zabura 34:18MK 31.4

  Fadin zunubi na gaskiya daban ya ke, kuma yana yarda da zunubi. Ya yiwu irin wadannan zunbai sai gaban Allah kawai za a fade su, ya yiwu kuma wadansu irin zunuban za a fade su ne ga mutanen da aka yi musu wannan laifi, ba a fade su a fili gaban jamma’a ba, ya yiwu kuma wadannan laifofin da suka shafi jama’a duka, dole kuwa a fade su a fili gaban jama’a. Amma ko wane irin amsa laifi ko fadinsa dole ne a yi shi cikin gaskiya.MK 32.1

  Cikin zamanin Annabi Samu’ila ‘ya’yan Israila suka yi nisa da Allah. A lokacin sun sha hakkin zunubi, domin bangaskiyarsu cikin Allah ta bace masu, ganewa da ikonsa, da hikima na mulkin al’amura duka suka bace masu, amincewarsu da shi cewa zai iya kare su ya bace. Suka juya daga bin babban Mai-mulkin halitta, suka nemi a mallake su kamar sauran al’umman da ke kewaye da su. Kafin su sami salama sai da suka fadi zunubinsu suka ce “Gama mun kara ma dukan zunubanmu wannan mugunta da muka bida ma kammu sarki.” I Samuila 12:19. Dole ne su fadi zunubin nan da aka same su da laifin sa. Rashin godiyarsu ya nawaita rayukansu, ya yanke su daga Allah.MK 32.2

  Allah ba zai karbi fadin laifi im ba tare da tuba da sake zama ba. Dole irin zama ya sake, dole a share ko wane abu mai ba da haushi ga Allah. Wannan shi ne abin da ya kamata ya abuku idan aka ji bakin ciki domin aikata zunubi. An kaiyade mana ayukan da za mu yi a fili a gabammu game da wannan; “Ku yi wanka, ku tsabtata; ku kawas da muguntar ayukanku daga gaban idanuna: ku bar yin mugunta; ku bidi shari’a, ku hana zalumchi, ku shar’anta maganar marayu, ku taimaki da’awar gwamraye.’’ Ishaya 1:16, 17. “Watau, idan shi mugun ya mayas da jingina, ya koma da abinda ya kwache ya bi kaidodi masu kawo rai, ba ya aika wani laifi ba; lallai rai zaya yi, ba zaya mutu ba.” Ezekiel 33:15. Bulus, game da zaman tuba, ya ce, “Bachin zuchiya da aka yi maku irin da Allah ke sa, duba irin karfin hankali da ya aika a wurinku; i, duba, wache irin kariyar kai, i, wane irin haushi, i, wane irin tsoro, i, wane irin dauka pansa, i, wane irin bege, i, wache irin himma! Ga kowane abu kuka nuna kanku kubutattu a chikin wannan matsalla.” 2 Korinthiyawa 7:11.MK 32.3

  Sa’anda zunubi ya matas da gababuwan ganewa na mutunci, mai aikata mugun abu ba ya kan gane tauyewar halinsa ba, ko ya gane girman muguntar da ya aikata, kuma, idan ba ya biye ma ikon hakikantarwar na Ruhu Mai-tsarki ba, sai ya zauna cikin makantar ganin zunubinsa. Facfin laifofinsa ba za su zama na gaskiya ba, ba kuma da himma ba. Ga ko wane amsa laifi guda sai ya kara da wata ‘yar hujjar dalilin aikinsa, ya ce im ba domin haka da haka ba, da bai yi haka ko haka ba, akan abinda an yi masa facfa.MK 33.1

  Bayan Adamu da Hauwa’u sun ci daga cikin ‘ya’yan itacen da aka hana su, sai suka cika da kunya da tsoro. Tunaninsu na farko shi ne hujjar da za su bayar domin zunubinsu, da kuma tunanin hanyar da za su tsere wa hakuncin mutuwa. Sa’anda Ubangiji ya tambaye su a kan zunubinsu, Adamu ya amsa ya ce “Macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ce ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.” Ita macen kuma ta sa laifin kan maciji ta ce, “Macijin ne ya rude ni, ni kuwa na ci.” Farawa 3:12, 13. Dom me ka halitta macijin? Dom me ka bar shi ya zo cikin Addini? Wadannan su ne kamar hujjoji da ta bayar cikin amsa dalilin zunubinta, wato ta sa alhakin faduwarsu duka a wuyan Allah. Wannan hali na baratad da kai daga uban karere ya faru ga duk ‘yan-Adam kuwa, maza da mata, sun baiyana shi. Irin wacfannan facfin laifi ba Ruhu Mai-tsarki ne ya ke sa a yi su ba. Allah kuwa ba zai karbe su ba. Tuba na gaskiya ya kan sa mutum ya dauki laifinsa da kansa, ya fade shi ba tare da ha’inci ko riya ba. Kamar shi mai karban harajin nan wanda ko daga kansa sama bai yi ba, amma ya yi kuka ya ce “Ka yi mani jinkai ya Allah, ni mai zunubi.” kuma su dukan wadanda suka amsa laifinsu za a baratad da su, gama Yesu zai yi roko sabili da ruhohinsu da suka tuba ta wurin jininsa. Misalai cikin Maganar Allah na tuba mai gaskiya da tawali’u sun baiyana cewa ruhu mai fadin laifi ba ya ba da hujjar aikata zunubi ko ya yi kokarin baratad da kai. Bulus bai nemi kare kansa ba. Ya shafa wa zunubinsa bakin duhu, ya nuna shi kamar bakin tukunya ya ke, bai kuma saukaka laifinsa ba. Ya ce “Na kuble tsarkaka dayawa chikin kurkuku, bayan da na karbi izni daga wurin manyan malamai; sa’anda a ke kisansu kuma, ni kan bada bakina gaba da su. Lokachi dayawa kuma, chikin dukan majami’u ina gwada masu wuya, anni- yata in sa su su yi sabo; kuma domin na fai hauka sabada su, na bi su da tsanani har ga wadansu biranai na ketaren iyaka.” Ayukan Manzani 26:10, 11. Bai yi shakkar fadin cewa “Kristi Yesu ya zo chikin duniya domin cheton masu-zunubi; chikinsu kwa ni ne babba.” 1 Timothawus 1:15.MK 33.2

  Mai tawali’u da karyayyar zuciya, kasashshe ta wurin tuba mai gaskiya, zai gane wani abu daga cikin kaunar Allah da tamanin Kalvari; kuma kamar yadda da ya kan fada wa ubansa mai kauna tasa, hakanan mai tuba na gaskiya zai kawo dukan zunubansa gaban Allah. Kuma an rubuta “Idan mun fadi zunubanmu, shi mai-alkawali ne, mai-adilchi kuma, da za shi gafarta mamu zunubanmu, shi tsar¬kake mu daga dukan rashin adilchi.” I Yohanna 1:9.MK 34.1

  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents