Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    YIN GIRMA CIKIN KRISTI

    Sake zuciya wanda ta wurinsa mu ke zama ‘ya’yan Allah ana kiransa haifuwa a cikin Littafi Mai-tsarki. Kuma, ana misalta shi da sabon siro na iri mai kyau wanda manoma suka shuka. Bisa ga wannan misali haka sabobin masu juyawa ga Kristi su ke, kamar “jarirai sabobin haifuwa,” “mu yi girma hikin abu duka zuwa chikinsa.” 1 Bitrus 2:2; Afisawa 4:15 sai sun kai munzulin maza da mata cikin Kristi Yesu. Ko kuma kamar iri mai kyau da aka shukka cikin gona, za su yi girma su ba da ‘ya’ya. Ishaya ya ce za a ‘ ’ che da su itatuwa na adilchi, dashe na Ubangiji, domin shi daukaka.” Ishaya 61:3. Domin haka ana cfauko misalai dga abubuwa na halitta, domin su taimake su gane asirtattun gaskiya na zaman ruhaniya.MK 55.1

    Komai hikima da gwaninta na dan-Adam ba zai iya ba da rai ga ko wace irin halitta ba komai kankantar ta. Ta wurin rai da Allah ne da kansa ya hura, itatuwa da dabobi su ke iya rayuwa. Haka kuma sai ta wurin ran da ya fito daga Allah ne kadai a ke haifan rai na ruhaniya cikin zuciyar ‘yan-Adam. “Im ba a haifi mutum daga bisa ba.’’ Yohanna 3:3. ba zai iya zama mai taraiya cikin ran da Kristi ya zo bayarwa ba.MK 55.2

    Kamar yadda ya ke game da rai haka ya ke game da yin girma. Allah ne ya ke kawo curin fure har ya bude ya zama fure sosai, furen kuma ya yi ‘ya’ya. Ta wurin ikonsa ne iri ya ke girma, “Soshiya tukuna, kana zangarniya, bayan wannan zangarniya da kwaya nunnana a chiki.” Markus 4:28. Annabi Hosea kuma ya fadi a kan Isra’ila cewa “Zasu murmure kamar hatsi, su yi fure kamar kuringar anab.” Hosea 14:7. Yesu kuma ya ce mana “Ku lura da fure fa, girman da su ke yi.” Luka 12 :27. Itatuwa da furarruka suna girma ba da wani kokari ko iko nasu na kansu ba, amma ta wurin karban abin da Allah ya tanada domin ya yi hidimar rayukansu. Jariri ba zai iya kara girman jikinsa ta wurin ikon kansa ba. Haka kuma ba ku iya sa wa kanku girma na ruhaniya ta wurin kokarin kanku. Ko itace, ko jariri, yana girma ta wurin karba daga abin da ke kewaye da shi wanda ya ke yi masa hidimar ransa — iska, hasken rana, da abinci. Abin da wadannan kyautai su ke yi ga dabba da itace, shi ne Kristi ya ke yi ga wadanda suka amince da shi. Shi ne “Amma Ubangiji za ya zama madawamin haskenki.” “Gama Ubangiji Allah rana ne da garkuwa kuma.” Ishaya 60:19; Zabura 84:11. “Zan zama kamar raba ga Israila.” “Za ya sabka kamar ruwan sama bisa sosayayyar chiyawa.” Hosea 14:5; Zaruba 72:6. Shi ne rayayyen ruwa, “Gama gurasar Allah mai sabkowa daga chikin sama che mai-bada rai kuma ga duniya.” Yohanna 6:33.MK 55.3

    Cikin kyauta mafi gaban kwatanci na Dansa, Allah ya kewaye duniya duka da iskar alheri, tamkar iskar da muka sani mai kewaye duniya. Duk wadanda suka zabi su shaki wannan iska mai ba da rai za su rayu, sua yi girma zuwa matsayin maza da mata cikin Kristi Yesu.MK 56.1

    Kamar yadda fure ya ke juyawa ga rana, domin hasken rana ya yi taimako wajen dada ba shi kyau da cikakken fasali, haka kuma sai mu juya ga Ranar Adilci, domin hasken sama ya haskaka bisam mu, domin halimmu ya yi girma cikin kammannin Kristi.MK 56.2

    Daidai abin da Yesu ya koyas ke nan sa’anda ya ce “Ku zamna chikina, ni ma a chikinku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada yaya don kansa ba, sai dai yana zamne chikin kuringar anab; hakanan kwa ku ba ku iya ba, sai dai kuna zamne chikina . . . gama im ba tare da ni ba, ba ku iya yin komi ba. Yohanna 15:4, 5. Kuna dogara ga Kristi domin ku yi zama mai tsarki daidai kamar yadda reshe ya ke dogara ga tushensa domin yin girma da ba da ‘ya’ya. Im ba tare da Shi ba ba ku da rai. Ba ku da iko ku yi tsayaiya da jaraba, ko ku yi girma cikin alheri da tsarki. Idan kuka zauna cikinsa za ku yi yabanya. Idan kuna samun rai daga gareshi ba za ku yi yaushi ba, ko ku rasa ba da ‘ya’ya. Za ku zauna kamar itacen da aka dasa a bakin kogunan ruwa.MK 56.3

    Dayawa suna tsammani dole su yi “kadan daga cikin aikin su kadai. Sun amince da Kristi domin gafarar zunubi, amma yanzu suna nema su yi zaman kirki ta wurin kokarin kansu. Amma irin wannan kokari dole ne ya ka sa. Yesu ya ce, “Im ba tare da ni ba ba za ku iya yin komai ba.” Yin girmammu cikin alheri, farin cikimmu da amfanimmu — duk ya dogara ga hacfuwar mu da Kristi. Ta wurin shawara da shi ne ko wace rana, ko wace sa’a — ta wurin zama cikinsa — za mu yi giima cikin alheri. Shi ba farkon bangaskiyamu ne kadai ba, amma karshen ta ne. Kristi ne farko, da karshe, da ko wane lokaci. Sai ya kasance tare da mu, ba a farko ko a karshen fagemmu kadai ba, amma a ko wane taki bisa hanyar. Dauda ya ce, “Na sa Ubangiji a gabana tutur: Da shike yana ga hannun damana ba zan jijigu ba.” Zabura 16:8.MK 56.4

    Kana tambaya, “Yaya zan zauna cikin Kristi?” — Kamar yadda ka karbe shi da farko. “Tunda shike kuka karbi Kristi Yesu Ubangiji, sai ku yi tafiya a chikinsa hakanan.” Amma adilina da bangaskiya za shi rayu: Idan kwa ya noke, raina ba shi jin dadinsa ba. Kolossiyawa 2:6. Ibraniyawa 10:38. Kun ba da kanku ga Allah, ku zama nasa dungum, ku bauta masa, ku yi masa biyaiya, kum kuma dauki Kristi shi ne Mai-ceton ku. Ku da kanku ba ku iya biyan bashin zunubanku ko ku sake zuciyarku, amma tun da shi ke kun ba da kanku ga Allah, kun gaskanta ya yi dukan wannan dominku sabo da Kristi. Ta wurin bangaskiya kuka zama na Kristi, ta wurin bangaskiya kuma za ku yi girma a cikinsa — ta wurin bayarwa da karba. Sai ku ba da duka — zuciyarku, hankalinku, bautarku — ku ba da kanku gareshi domin ku yi biyayya da abin da ya ke bukata; sai kuma ku karbi duka — Kristi; cikakken dukan albarka, zai zauna cikin zuciyarku, ya zama karfinku, da adilcinku, da matai- makinku, har abada — domin ya ba ku ikon yin biyaiya.MK 57.1

    Ku tsarkake kanku ga Allah da safe; ku mai da wannan aikinku na farko. Bari addu’arku ta zama, “Ka dauke ni dungum in zama naka, ya Allah. Na sa dukan shirye-shiryenka a kafafuna. Ka yi amfani da ni yau cikin bauta maka. Ka zauna a cikina, ka sa kuma dukan ayyukana in aikata su cikinka.” Wannan abu ne da za a yi kullun. Ku ba da duk shirye-shiryenku gareshi, domin a gudana su ko a ki gudana su yadda nufinsa ya ga dama. Ta wurin yin haka ko wace rana za ku ba da ranku cikin hannun Allah, ta haka kuma za a fi mulmila rayukanku cikin gurbin Kristi.MK 57.2

    Rayuwa cikin Kristi zama ne na hutu. Ba lalai mu ji wani suka cikin rammu wanda zai sa mu farin ciki farat daya ba, amma dole akwai zaunannen amincewa mai salama. Begenku ba cikin kanku ya ke ba; cikin Kristi ya ke. An hada rashin karfinku da karfinsa, jahilcinku kuma an hacfa shi da hikima nasa; kumaman- cinku kuma an hada shi da ikonsa mai jimrewa. Domin haka ba kanku za ku duba ba, kada ku bar hankali ya dogara ga kanku, amma ku dubi Kristi. Bari hankali ya zauna bisa kan kauna tasa, da bisa kan jimali da cika na halinsa, Kristi cikin musun kansa, Kristi cikin kaskancinsa, Kristi cikin sahihancinsa da tsarkinsa, Kristi cikin kaunarsa mafi gaban kwatanci — wadannan su ne abin da ruhu zai yi tunani a kansu. Ta wurin kaunarsa ne, da kwaikwayonsa, da dogara gareshi, za a same ku cikin kamaninsa.MK 57.3

    Yesu ya ce, “Ku zauna cilcina.” Wadannan kalmoni suna sifanta hutu, da kafuwa, da amincewa. Kuma, ya sake kiram mu ya ce, “Ku zo gareni, . . . ni kwa im ba ku hutawa.” Matta 11:28. Kal- momin mai-zabura ma tunanin da suka furta ke nan, “Ku huta kurum chikin Ubangiji, ka yi hankuri kana sauraronsa.’’ “Chikin komawa da hutu za ku tsira; da natsuwa da dogara karfinku za ya tabbata.” Zabura 37:7; Ishaya 30:15. Ba a samun wannan hutu cikin rashin aiki, gama a cikin kiran da Mai-ceto ya yi an hada alkawarin hutu da aiki. “Ku dauka ma kanku karkiyata, . . . za ku sami hutawa ga rayukanku.” Matta 11:29. Zuciyar da ta ke hutawa bisa Kristi za ta yi kwazo da samri cikin yin aiki dominsa.MK 58.1

    Sa’anda hankali ya kallafa ga son kai, ya juya daga Kristi, Shi Masomin karfi da rai. Domin haka kokarin Shaitan ne ko wane lokaci ya kawas da hankali daga Mai-ceto, ta hakanan ya hana haduwa ko yin shawara da Kristi. Nishadan duniya, al’amuran duniya, alhinai da bakin ciki, laifofin wacfansu, ko kuwa laifofinku, da kasawarku; zuwa ga duka ko guda daya daga cikin wacfannan zai nema ya maida hankalinku. Dayawa wadanda su ke da kuduri na kirki, wacfanda su ke da marmarin su yi zama domin Allah, sai ka ga safai Shaitan ya bishe su kan tunawa da laifofinsu da rashin karfinsu; ta wajen raba su da Kristi hakanan kuwa ya ke bege ya ci nasara. Kada ku yarda dabarunsa su bad da ku. Kada mu maida kanmu ne tsakiya, ko mu yi ta alhini, ko mu ji tsoron cewa ko za a cece mu. Duk wannan sai ya juyas da ruhu daga Masomin karfinmmu. Ku ba da ajiyar Ruhunku ga Allah, ku kuwa amince da shi. Ku yi zance da tunani a kan Yesu. Bari tunawa da kai ya bata cikinsa. Ku jingine dukan shakka, ku sallami tsoronku. Ku ce, tare da Bulus manzo, “Yanzu kuma ba ni ba ne ina rayuwa, amma Kristi ke rayuwa daga chikina: wannan rai kwa da ni ke rayuwa chikin jiki yanzu ina rayuwa chikin bangaskiya, bangaskiya wadda ta ke chikin Dan Allah, wanda ya kamnache ni, ya bada kansa kuma domina.” Galatiyawa 2:20. Ku huta cikin Allah. Yana ;ya kiyaye abin nan da kuka ba Shi ajiya. Idan kuka bar Shi wanda ya kaunace ku, kuka bar kanku cikin hannunsa, zai, kiyaye ku fiye da mai nasara ta wurin Shi wanda ya baunace ku din.MK 58.2

    Sa’anda Kristi ya dauka wa kansa tabi’ar dan-Adam, ya daura mutunci a jikinsa da igiyar bauna wadda ba wani ikon da zai iya tsunke ta sai ko da yardan dan-Adam kansa. Tutur Shaitan zai jarabe mu da nuna mana abubuwa masu kyau domin mu tsinke igiyar nan da ke tsakanimmu — watau don kammu mu zabi rabuwa da Kristi. A nan ne fa ya kamata mu lura, mu yi kokari, mu yi addu’a domin kada wani abu ya rude mu har da zai sa mu zabi wani Ubangiji, domin kuwa a ko wane lokaci a sake mu ke mu yi haka im mun ga dama. Amma bari mu zura idanummu ga Kristi, Shi kuwa zai kiyaye mu. Duban Yesu zai hana wani abu ya same mu. Babu abin da zai iya fizge mu daga hannunsa. A cikin dubansa ko wane lokaci sai “Muna sakuwa zuwa chikin wannan sura daga daraja zuwa daraja, kamar dai daga wurin Ruhun, watau Ubangiji.&rdquo II Korinthiyawa 3:18.MK 59.1

    Ta wurin haka ne almajirai na farko suka samu kamantuwarsu da kaunataccen Mai-ceto. Sa’anda wadannan almajirai suka ji kalmo- min Yesu, sun ji a ransu suna da bukatarsa. Suka neme shi ko v/ace lokaci, a cikin gida, a wajen cin abinci, a cikin lolloki, ko cikin saura. Suna tare da shi kamar almajirai tare da malami kullun suna karban koyaswar gaskiya mai tsarki daga lebunansa. Suna dubansa kamar yadda barori su ke sauraren uban-gidansu, su koyi ayukan da su ke wajibinsu ne. Su wacfannan almajirai mutane ne “Iliya mutum ne da tabi’a kamar tamu, ya kwa yi addu’a da nachiya, kada a yi ruwa: kuma shekara uku da wata shidda ba a yi ruwa a kasa ba.” Yakub 5:17. Yaki daya su ke da shi daidai da mu gaba da zunubi. Alheri daya su ke bukata domin su yi zaman tsarki.MK 60.1

    Ko Yohanna, kaunataccen almajiri, wanda ya fi sauran nuna kamanin Mai-ceto, ba don tabi’ar kansa ya samu kyaun wannan halin tawali’u ba. A hankali zuciya tasa ta gusa zuwa ga Kristi har ya manta kuncin rai. Amma da ya gane halin Ba-samaniyin nan, sai ya ga kasawa tasa, wannan gane nufin hanli nasa kuwa ya sa ya saduda. Ya lura da wadansu abubuwa da suka kayatad da shi game da halin Dan Allah cikin ma’amilla na zamansa na duniya. Ya ga a cikin halin Dan Allah akwai karfi amma tare da hakuri; akwai iko amma hade da taushin zuciya, akwai daukaka amma hade da tawali’u a hankali zuciya tasa ta gusa zuwa ga Kristi har ya manta da kansa cikin kauna zuwa ga Ubangijinsa. Halin nan nasa na alfarma da girman kai da kunci ya saduda ga ikon Kristi mai ginawa. Ikon Ruhu Mai-tsarki mai sake haifuwa ya sabonta zuciya tasa. Ikon kauna na Kristi ya sake halinsa. Wannan shi ne tabbataccen abin da zai abku cikin haduwa da Yesu. Sa’anda Kristi ya ke zaune cikin zuciya, duk tabi’a sai ta sake. Ruhun Kristi da kauna tasa su kan tausasa zuciya, su mallaki ruhu, su cfagad da tunani da nufe-nufe zuwa ga Allah na sama.MK 60.2

    Sa’anda Kristi ya hau bisa cikin sama, sanin yana nan bai rabu da masu binsa ba. Kasancewa ne da ke cikin zuci, cike da haske da kauna. Yesu, Mai-ceto, wanda ya yi yawo, ya yi tadi tare da su, wanda ya yi wa zukatansu zantattuka na bege da ta’aziya, tun lokacin da sakon salama ya izo bisa lebunansa, ga shi an dauke shidaga garesu zuwa cikin sama, amon murya tasa kuma ya komo musu sa’ anda girgije na mala’iku suka karbe shi cewa ” Gashi kwa ina tare da ku kullayaumi har matakar zamani.” Matta 28:20. Ya hau bisa cikin sama da sifar ‘yan-Adam. Sun sani yana gaban kursuyin Allah, har yanzu kuwa abokinsu ne da Mai-cetonsu, nufinsa zuwa garesu bai sake ba, ana kuwa lisafta shi da ‘yan-Adam masu shan wahala har wa yau. Yana mikawa a gaban Allah alhakin jininsa mai daraja, yana nuna raunin hannayensa da kafafunsa, abin tunawa da tamanin da ya biya domin abin da ya pansa. Sun sani ya hau bisa cikin sama domin ya shirya musu wurare, kuma sun sani zai sake dawowa ya dauke su zuwa ga kansa.MK 60.3

    Sa’anda suka taru wuri daya, bayan ya rigaya ya hau sama, sun yi himma su mika roke-rokensu ga Uba cikin sunan Yesu. Cikin ladabi mai yawa suka sunkuya cikin addu’a, suna maimaita alkawarin da ya ce “Idan kun roki komi ga Uba, zaya ba ku a chikin sunana. Ku yi roko, za ku karba, domin farinchikinku ya chika.” Yohanna 16:23, 24. Suka dada mika hannun bangaskiya gaba gaba zuwa sama da wannan roko cewa “Kristi Yesu ne ya mutu, i kwa, har ya tashi daga matattu, yana hannun damana Allah, yana roko sabili da mu.” Romawa 8:34. Pentecost kuma ta kawo musu jin kasancewar Mai-ta’aziya, wanda Kristi ya ambata ‘ ’Gama yana zamne tare da ku zashi kwa zamna a chikinku.” “Yana da anfani a gareku in tafi: gama idan ban tafi ba, mai-taimakon ba zashi zo wurinku ba; amma idan na tafi, zan aiko shi a gareku.” Yohanna 14:17; 16:7. Daga nan gaba Kristi zai zama tutur cikin zukatan ‘ya’yansa ta wurin Ruhun. Hacfuwansa da su ya . . . fi kusa da lokacin da shi kansa ya ke tare da su. Haske da kauna da ikon Kristi da ke zaune cikin zuciya yana haskakawa har waje, har sa’anda mutane suka gansu “Suka yi mamaki, suka dauki zato a kansu da suna tare da Yesu.” Ayukan Manzani 4:13-MK 61.1

    Duk abin da Kristi ya ke ga almajiransa na farko, haka nufinsa ya ke zuwa ga ‘ya’yansa a yau, gama a cikin addu’a tasa ta karshe, tare da ‘yan almajiransa kima a kewaye da shi ya ce ‘Kuma ba domin wadannan kadai ni ke yin addu’a ba, amma domin wadanchan kuma da ke bada gaskiya gareni ta wurin maganarsu.” Yohanna 17:20.MK 61.2

    Yesu ya yi addu’a sabili da mu, ya kuma roka cewa mu zama daya da shi, kamar yadda cfaya su ke da Shi da Uban. Wanne irin haduwa ne wannan? Maiceto ya yi jawabi a kan kansa ya ce “Dan ba shi iya yin komi don kansa ba,” Uban da ya ke zamne a chikina yana yin ayukansa.” Yohanna 5:19; 40:10. Domin haka idan Kristi yana zaune cikin zukatammu zai yi aiki a cikin mu — “Amma abu daya ni ke yi, ina manta da abubuwan da ke baya, ina kutsawa zuwa ga wadanda ke gaba.” Filibiyawa 3:13. Za mu yi aiki kamar yadda ya yi, za mu baiyana hali kamar nasa. Ta hakanan wajen zama a cikinsa da kauna tasa za “Mu yi girma chikin abu duka zuwa chikinsa, wanda shi ne kai, watau Kristi.” Afisawa 4:15.MK 61.3

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents