Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
 • Results
 • Related
 • Featured
No results found for: "".
 • Weighted Relevancy
 • Content Sequence
 • Relevancy
 • Earliest First
 • Latest First
  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents

  AIKI DA ZAMAN RAI

  Allah shi ne tushen rai da haske da farin ciki ga dukan halitta. Kamar yadda haske ke fitowa daga rana, kamar yadda rafukan ruwa su kan fashe kasa daga mabulbula mai rai, haka albarka ke gudanowa daga wurin Allah zuwa ga dukan halittansa. A kuwa duk inda ran Allah ya ke cikin zukatan ‘yan-Adam, zai gudana waje zuwa ga wadansu cikin kauna da albarka.MK 63.1

  Farin cikin Mai-cetom mu a cikin dagarwa da pansar ‘yan-Adam fadaddu ya ke. Sabili da wannan bai mai da ransa abin kauna a gareshi ba, amma ya daure da radadin giciye, ya raina kuma. Haka mala’iku su ke hidima domin su samowa wacfansu farin zuciya. Wannan shi ne abin faranta musu zuciya. Abin da wacfansu zukata masu son kai za su ga kamar hidima ne na kaskanci, yin hidima ga wulakantattu, wadanda ko ta wace hanya, ko ta hali, ko ta matsayi, daraja tasu ba ta isa ba, wannan shi ne aikin mala’iku marassa zunubi. Halin Kristi na kaunar ba da kai ya zama hadaya, shi ne ya mamaye samaniya duka, wannan kuwa shi ne tushen albarkar sama. Wannan shi ne halin da masu bin Kristi ya kamata su samu, watau aikin da za su yi.MK 63.2

  Sa’anda kaunar Kristi ta kafu cikin zuciya, ba za ta boyu ba kamar abu mai kamshi. kowa da muka zo cikin ma’amala da shi zai ji wannan iko da ke tare da mu. Halin Kristi cikin zuciya kamar mabulbulan ruwa ya ke cikin hamada, yana bulbulowa domin ya wartsakad da komai, kuma yana ba wacfanda su ke bakin hallaka himma su sha daga cikin ruwan rai.MK 63.3

  Kauna zuwa ga Yesu za ta baiyana cikin marmarin yin aiki kamar yadda ya yi domin albarka da daga zaman ‘yan-Adam. Za ta bayas zuwa ga kauna da taushin rai da tausayi zuwa ga dukan halittan da ke karkashin inuwar Ubammu na sama.MK 63.4

  Zaman da Mai-cetommu ya yi a duniyan nan ba zama ne na sauki da yin hidimar kansa ba, amma da naciya, da himma, da rashin gajiya, ya yi aiki mai tsanani domin ceton ‘yan-Adam batattu. Tun daga wurin haifuwa tasa a sakarkari zuwa tudun Kalvari ya bi hanyar kin kai, bai kuwa nemi ya zuke daga ayyuka masu wuya, ko tafiyu masu tsanani, ko ayyuka masu gajiyaswa ba, ko masu sa a suke Ya ce “Kamar yadda Dan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma wadansu, shi bada ransa kuma abin pansar mutane dayawa.” Matta 20:28. Babban abin da ya kiyaye ke nan cikin zamansa, sauran abubuwa kuwa ya maishe su baya. Abincinsa ne da abin shansa ya yi nufin Allah ya kuwa gama aikinsa. Son kai da sa kai a gaba ba su da wuri cikin aikinsa.MK 63.5

  Haka ne kuma su wadanda su ka taraiya cikin alherin Kristi za su kasance a shi rye su yi ko wane irin abu domin su wacfannan da ya mutu domin su su samu ladan daga cikin kyautan nan na sama. Za su yi iyakacin iyawa tasu su sa duniya ta fi dadin zama garesu Wannan hali shi ne tabbataccen yabanya na ruhun da ya yi juyawa na gaskiya. Da zuwan dan-Adam wurin Kristi, nan da nan sai a haifi marmari a cikin zuciya tasa na son ya sanas wa wadansu cewa ya samu aboki mai tamani cikin Yesu. Ba shi yiwuwa a rufe gaskiyar nan mai cetarwa mai tsarkakewa cikin zuciya kurum. Idan muka saturtar da kammu da adilcin Kristi, idan kuma muka cika da farin cikin Ruhunsa mai zama a zuci, ba shi yiwuwa mu rufe bakimmu mu yi shuru. Idan muka dandana muka gani Ubangiji nagari ne, zamu samu abin da za mu fadi. Kamar Filibus sa’anda ya samu Mai-ceto, za mu kira wadansu su zo su gan shi. Za mu neni mu nuna musu abubuwa da ke masu jawowa na Kristi da tabbattattun abubuwan da ido ba ya gani na duniya mai zuwa. Marmari zai tsananta na son bin gurbin sawayen da Yesu ya taka. Za mu ji tsanantaccen marmari na son wacfanda ke kewaye da mu su dubi “Dan-Rago na Allah, wanda ya ke dauke da zunubin duniya.”MK 64.1

  Kuma, kokarin mu jawo albarka bisa wasu zai komo ya zama albarka a kam mu. Wannan shi ne nufin Allah da ya ba mu rabo cikin aikata shirin da ya yi domin pansa. Allah ya ba ‘yan-Adam dama su zama masu taraiya cikin tabi’ar ruhaniya, su kuma sai su hura wannan albarka zuwa ga sauran ‘yan-uwansu ‘yan-Adam. Wannan shi ne daraja mafi girma, da farin ciki mafi girma, wanda ya ke yiwuwa ga Allah ya aza bisa kan ‘yan-Adam. Su wakannan fa da suka zama masu taraiya cikin hidimar kauna ana kawo su su zama mafiya kusantar Mahallicinsu.MK 64.2

  In da ya so, da Allah ya ba da sakon bishara, da sauran dukan hidimar kauna cikin hannun mala’iku na sama. In da ya so, da ya nemi wata dabara domin ya aikata nufinsa. Amma sabo da kauna tasa mara iyaka, ya zabi ya maishe mu abokan aiki tare da shi, tare da Kristi, da kuma tare da mala’iku, domin mu samu rabo cikin albarka, da farin ciki, da dagarwa mai ruhaniya, wanda su ne ladan wannan hidima na rashin son kai.MK 65.1

  An kawo mu cikin tausayi tare da Kristi ta wurin taraiya cikin shan wahala tasa. Ko wane aiki na ba da kai ya zama baiko domin jin dadin wadansu yana karfafa ruhun yin kyauta cikin zuciyar mai bayarwa, yana dada hada zumunci ne ama sabili da mu ya zama matalauci, domin ku zama mawadata ta wurin talaucinsa.” Sai fa mun cika nufin nan na sama cikin halittammu sa’annan zaman duniya zai zama albarka a gare mu.MK 65.2

  Idan za ku tafi ku yi aiki kamar yadda Kristi ya aiyanawa alma¬jiransa, ku ribato rayuka dominsa, za ku ji bukatar zurfin karuwar sanin abubuwa na ruhaniya, za ku kuma yunwata da kishirta sabo da adilci. Za ku yi roko tare da Allah, bangaskiyarku kuma za ta karfafa, rayukanku kuma za su cika cikinsu da ruwan rijiyar ceto Cin karo da tsayaiya da gwaje-gwaje za su kora ku zuwa ga Littafi Mai-tsarki da addu’a. Za ku yi girma cikin alheri da sanin Kristi, za ku kuwa karu da wayewar kai.MK 65.3

  Tabi’ar yin aiki sabili da wadansu ba game da son kai ba yana ba da zurfi, da kafuwa, da kyakkyawan hali irin na Kristi, yana kuma kawo salama da farin ciki ga mai irin wannan halin. Buri su kan cfagu. Babu wuri domin ragwanci ko son kai. Su wadannan da su ke aikata alherin Kristi za su yi girma su samu yin aiki domin Allah. Za su samu hankula masu ganewa na ruhaniya, da bangaskiya tsayayya, mai yin girma da karuwar iko wajen yin addu’a. Ruhun Allah mai motsi bisa ruhohinsu ya kan kirawo jituwar ruhu cikin amsawar tabuwar ruhaniya. Su wacfannan fa da suka maida hankali dungum cikin kokari mara son kai domin jin dadin wacfansu, babu shakka suna hidimar ceton kansu.MK 65.4

  Hanya guda cfaye ce kacfai ta inda za mu bi mu yi girma cikin alheri, ita ce kulawa cikin aikata ainihim aikin da Kristi ya umurce mu — mu yi iyakacin kokarim mu wajen taimako da albarkata wacfanda su ke bukatar ta imakon da za mu iya ba su. Motsa jiki yakan kawo karfi; aiki shi ne matsayin zaman duniya Su wacfannan masu kokari su yi zaman alheri kawai a ciki bin Kristi, ba su kuwa aikata komai domin Kristi, aniya su ke yi su yi zaman su na duniya don su ci kawai ba tare da yin aiki ba. Kamar yadda ya ke cikin halitta haka kuma ya ke cikin ruhaniya zaya jawo masu lalacewa da rubewa. Shi mutumin da ya ki ya yi amfani da gababuwansa, ba da dacfewa ba zai rasa karfin amfani da su. Hakanan shi mai bin Kristin wanda ba zai yi amfani da ikon da Allah ya ba shi ba, ba rashin girma cikin Kristi ne kacfai zai gaza yi ba, amma karfin da ya rigaya ya samu a da zai bace masa.MK 66.1

  Ekkliziyar Kristi itace wakilin Allah domin ceton ‘yan’Adam. Aikinta shi ne ta watsa Bishara zuwa ga duniya. Wannan aiki ya rigaya ya rataya a wuyan dukan masu bin Kristi. Ko wane, gwar¬gwadon baiwar da Allah ya ba shi, sai ya cika umurnin Mai-ceto. kaunar Kristi, wadda aka baiyana mana, ta sa mun zama mabarta ga dukan wad’anda ba su san shi ba. Allah ya ba mu haske ba domin kammu ne kacfai ba, amma domin mu haskaka masu.MK 66.2

  Idan masu bin Kristi suka farka da aikata wajibinsu, za a samu dubbai yau inda da cfaya ne kawai, don shelar Bishara a kasashen arna. Kuma dukan wadanda ba za su iya yin wannan aiki don kansu ba, suna iya ba da taimako ta wurin ba da kucfi, da tausayinsu, da addu’arsu. Kuma da an fi samun himantaccen aiki domin rayuka cikin kasashen masu bin Kristi.MK 66.3

  Ba lalai sai mun tafi kasashen arna ba, ba ma lalai ne mu bar gidajemmu ba, idan wannan wajib ne a garemu, mu yi aikin Kristi. Za mu iya yi wannan aiki a cikin gidajemmu, a cikin Ekkliziya, a tsakanin abokammu da abokan cinikinmu.MK 66.4

  Yawancin zaman duniya na Mai-ceto a dakin sassaka ya yi su a Nazareth wajen zama da aiki da hakuri. Mala’iku masu hidima tutur suna tare da Ubangijin rai sa’anda ya ke yawonsa tsakanin talakawa da ma-aikata, ba tare da an san shi ko ana darajanta shi ba. Yana cika sakonsa lokacin da ya ke aiki kan sana’a tasa daidai da lokacin da ya ke warkas da marasa lafiya ko a lokacin da ya ke rafiya bias rakuman ruwa masu hauka a bahar na Galili. Domin haka komai kaskancin matsayimmu cikin zaman duniya, za mu iya tafiya ko aiki tare da Yesu.MK 66.5

  Manzo ya ce “Bari kowane mutum, inda aka kira shi, shi, zamna nan tare da Allah.” 1 Korinthiyawa 7:3, 4. Mai ciniki ko dan kasuwa zai tafiyad da aikinsa cikin hanyar da za ta daukaka Uban- gijinsa sabo da gaskiya tasa. Idan shi mai bin Kristi ne da gaske, zai dauki addininsa cikin dukan abin da ya ke yi, ya baiyana wa ‘yan- Adam Ruhun Kristi. Makaniki ya iya zama wakili mai kwazo, mai aminci, ga Shi wanda ya yi aiki na kaskanci a tsakankanin duwatsun Galili. Ko wane mutum wanda ya ambaci sunan Kristi sai ya yi aiki yadda idan wadansu, suka ga ayukansa masu kyau, za ya bishe su su daukaka Mahallicinsu da Maipansarsu.MK 68.1

  Dayawa sun yi wa kansu hujjar kin ba da sadakokinsu sabo da aikin Kristi wai domin wadansu sun fi su wadata. Akwai tunanin cewa wai sai masu wata baiwa muhimmin ake bukata su ba da dukan kokarinsu zuwa ga aikin Allah. Wadansu kuma suna tsammani cewa baiwa ana ba da ita ne ga zababu da aka fi so kawai, sauran jamma’a kuwa ba a bukatar su samu rabo wajen yin aiki ko wajen samun ladan. Amma ba haka ya ke ba cikin misalin da aka bayar. Sa’anda Mai-gida ya kira barorinsa, ya ba ko wane aikinsa.MK 68.2

  Za mu iya aikata ayyuka na kaskanci cikin dacfin rai “Kamar ga Ubangiji.” Kolosiyawa 3:23. Idan kaunar Allah tana zuci, za ta fita a fili cikin zamammu. Ba ruwanku da tunawa da yadda duniya ta ke tsammani a kanku. Muddan zamanku na yau da gobe ya zama shaida cewa bangaskiyarku tsatstsarka ce, kuma sauran jama’a sun tabbata kuna nufin ku Sami amfanin su, kokarinku ba zai tafi duka a banza ba.MK 68.3

  Komai talauci da kaskanci na almajirin Yesu ya iya zama albarka ga wadansu. Watakila ba za su gane cewa suna yin wani abin kirki ba amma ta wurin kokarin su cikin rashin sani za su iya ta da rakuman ruwa na albarka wadanda za su kara fadi da zurfi, kuma ba shi yiwuwa su san irin albarkar da suka jawo sai ranar lada ta karshe. Ba za su sani ko su ji cewa suna yin wani babban abu ba. Ba a bukata su gajiyad da kansu da tunanin nasara. Su dai sai su ci gaba ba tare da hayaniya ba, suna aiki da aminci bisa abin da Allah ya aza musu, zamansu na duniya kuwa ba zai zama a banza ba. Rayukansu za su ci gaba cikin kamantuwa da Kristi, ta haka za su iya yin manyan ayuka, su kuma cancanci farin zuciya na rai mai zuwa.MK 68.4

  “Yesu, ka zana shi bisa zuciyata
  Cewa kai kadai ne abin bukata.
  A iya raba ni da dukan abu,Amma,
  dadai, dadai, ba daga gareka ba.’
  MK 69.1

  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents