Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
 • Results
 • Related
 • Featured
No results found for: "".
 • Weighted Relevancy
 • Content Sequence
 • Relevancy
 • Earliest First
 • Latest First
  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents

  ABIN DA ZA A YI DA SHAKKA

  Dayawa, mu samman su wadanda su ke sabbabi ne cikin zaman masu bin Kristi, wani lokaci su kan damu da abubuwan da shakka ke kawowa. Akwai abubuwa dayawa a cikin Littafi. Mai-tsarki wa¬cfanda ba za su iya ba da ma’ana tasu ba, ko kuwa ba su gane su ba, Shaitan kuwa ya kan yi amfani da wadannan domin ya girgiza bangaskiyarsu cewa Littafi masu tsarki ru’ya ne daga Allah. Su kan yi tambaya su ce, “Ta yaya zan san hanyar gaskiya? Idan hakika Litafi Mai-tsarki Maganar Allah ne yaya zan kubuta daga shakkoki?”MK 89.1

  Allah bai taba tambayar mu mu gaskanta komai ba ba tare da ba da isashshen shaida wanda za mu kafa harsashin bangaskiyar bisa kai ba. Kasancewarsa, Halinsa, Gaskiyar Magana tasa, duk an kafa su da shaida wadda ke magana da hankalimmu, wannan shaida kuwa a yalwace ya ke. Duk da haka Allah bai kawas da yiwuwar shakka ba. Dole bangaskiyarmu ta jingina kan shaida, ba nuni ba. Wadanda su ke so su yi shakka suna da damar yin haka, wadanda kuwa su ke so su san gaskiya za su samu shaida mai yawa inda za su jingine bangakiyarsu.MK 89.2

  Ba shi yiwuwa ga hankalin mamaci ya gane tabi’un ayyukan Madauwami. Ga mai kaifin hankali, ko ga rikakken masani Allah ba zai zama a nannacfe cikin asiri ba. “Ka iya binchike har ka tone zurfafan al’amura na Allah? Ka iya binchiken mai-iko duka sosai? Nisan sa kamar sama; yaya za ka yi? Ya fi Lahira zurfi, me zaka sani?” Ayuba 11:7-8.MK 89.3

  Bulus Manzo ya ce, “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binchiken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!” Romawa 11:33. Amma ko da shi ke “Hadura da dufu suna kewaye da shi,” “adilchi da shari’a tushen kursiyinsane.” Zabura 8 97:2. R.V. Za mu iya gane ma’amala da mu, da dalilin da ya sa ya ke yin haka, domin mu ga kauna mara iyaka da jinkai hade da iko mara iyaka. Za mu iya gane nufinsa gwargwadon yadda zai yi mana kyau mu sani, amma gaba da wannan sai mu gaskanta hanu wanda ya ke mai iko duka da zuciya wadda ta ke cike da kauna.MK 89.4

  Maganar Allah, kamar tabi’ar Marubucinta na sama, tana da asirai wadanda ba shi yiwuwa ‘yan-Adam su gane a zancin su. Shigowar zunubi cikin duniya, haifuwar Kristi, sabon haifuwa, tashi daga matattu, da abubuwa da yawa da ke cikin Littafi Mai-tsraki, asirai ne wacfanda zurfin su ya fi karfin hankalin dan-Adam ya kwatanta su ko ma ya gane su. Amma ba mu da wani dalilin da zai sa mu yi shakkar Maganar Allah domin mun kasa gane asiran ayyukansa. Tutur muna kewaye da asirai cikin halitta kanta wacfanda ba za mu kai ga gindin azancin su ba. Komai kankantar halitta mai-rai abu ne wanda komai hikimar malami ba shi da ikon kwatanta ta ko ya ba da dalilinta. A ko ina akwai al’ajiban da suka fi karfin ganewarmu. To ashe sai mu yi mamaki idan muka ga aikin duniya ta ruhaniya akwai asiran da ba za mu iya kai ga zurfin azancin su ba? Wuyar abin duka a rataye ya ke ga rashin karfi da rashin facfi na hankalin dan-Adam. A cikin littattafai masu tsarki, Allah ya ba mu isashshen shaida na sanin cewa tabi’arsa ba-samaniya ce, mu kuwa bai kamata mu yi shakkar Magana tasa ba, domin ba za mu iya gane dukan asiran shirye-shiryensa ba.MK 90.1

  Bitrus manzo ya ce akwai cikin litattafai masu tsarki “wadansu abu masu-wuyan ganewa a chikinsu, jahilai fa da marasa- tsayawa su kan daguladda azanchinsu, kamar yadda su ke yi da sauran litattafai, zuwa hallakar kansu.” 2 Bitrus 3:16. Masu shakka sun tura wuyar azancin Litattafai Masu-tsarki a gaba domin su zama dalilan gaba da Littafi Masu-tsarki; amma duk da wuyar hakanan sun zama shaida mai karfi na cewa Littafi Mai-tsarki daga sama ne aka ba da dai ikon rubuta shi. In da ba wani labarin Allah a cikinsa, sai abin da za mu iya ganewa nan da nan; idan da dan- Adam zai iya gane girman Allah da kwarjininsa, da littafi Mai-tsarki bai cfauki shaida ta iko daga sama ba. Wannan jimali da asiri na abubuwan da ake zancen su ya kamata don kansa ya kunna ban¬gaskiya a zuci cewa Maganar Allah ne.MK 90.2

  Littafi Mai-tsarki yana warwarse gaskiya cikin sauki da daidaitawa bisa ga bukacebukace da burin zuciyar dan-Adam har wannan ya zama abin mamaki da kayatarwa ga masana, ga shi kuma yana sa masu tawali’u da biyaiya su gane hanyar ceto. Duk da haka su wadannan saukakan gaskiya suna karaa da abubuwa masu nauyi, masu kai nesa, wadanda suka wuce ganewar dan-Adam, domin mu iya yarda da su kawai don Allah ne ya fade su. Ta haka ne aka shimfida shirin pansa a bude a gare mu, domin ko wane mai rai ya ga matakan da zai taka cikin tuba zuwa ga Allah da bangaskiya zuwa ga Ubangijimmu Yesu Kristi, domin a cece mu ta hanyar da Allah ya nufa; duk da haka a karkashin wacfannan gaskiya da aka gane su a saukake, asirai na nan kwance da su ke su ne boyewar daraja tasa — asirai da su kan faskari kwakwalwa wajen binciken su, amma suna kunna wutar zuci cikin ran mai neman gaskiya da sahihanci tare da ladabi da bangaskiya. Gwargwadon binciken na Litafi Mai-tsarki gwar- gwadon zurfin tabbatarwassa cewa Maganar Allah mai rai ce, kuma tunanin dan-Adam sai ya yi ruku’u a gaban kwarjini na ru’ya ta sama.MK 90.3

  Yarda da cewa ba za mu iya samun cikakken ganewar gaskiyan Littafi Mai-tsarki ba yarda ne kawai da cewa hankalin dan-Adam bai isa ya gane rashin iyakar ba, kuma cewa dan-Adam da gajeren hankalinsa na mutunci, ba zai iya gane nufenufen Mai-iko duka ba.MK 91.1

  Domin fa ba za su iya kai ga zurfin dukan asirin ba, masu shakka da kafirai suna kin yarda da Maganar Allah, kuma ba dukan masu cewa sun gaskanta Litttafi Mai-tsarki suka tsira daga hadarin wannan ba. Manzo ya ce, “Ku yi lura fa ‘yanuwa kada watakila mugunyar zuciya ta rashin bangaskiya ta kasance a cikinakowane dayanku da za ku ridda daga Allah mai-rai:” Ibraniyawa 3:12. Daidai ne a bi cikin Littafi Mai-tsarki da kyau a kuma yi bicike cikin “Har da zurfafa na Allah.” (1 Korinthiyawa 2:10) gwargwadon yadda aka baiyana su cikin Littafi. Ko da shi ke “Al’amura na asiri ga Ubangiji Allahnmu suke; amma wadanda an bayana, a garemu su ke duk da yayanmu har abada.” Kubawar Shari’a 29:29. Amma aikin Shaitan ne ya karkata ikon bincike na hankali. A kan hada fadin rai da tunani kan gaskiya na Littafi Mai-tsarki, har mutane su kan ji rashin hankuri d?. kasawa idan ba su iya kwatanta ko wace aya bisa ga yadda su ke so ba. Ya zama kaskanci ne a garesu su yarda da cewa ba su gane kalmomi na huruwa ba. Ba su yarda su yi hankurin jira har Allah ya baiyana musu gaskiya a lokacin da ya game shi. Suna ji a ransu cewa hikimar su kawai ba tare da wani taimako ba ya isa ya sa su iya gane Littafi Mai-tsarki, idan kuwa suka kasa sai su yi musun ikonsa. Gaskiya ne koyaswoyi da yawa da ake tsammani daga cikin Littafi Mai-tsarki aka same su, basu da tushe daga wurin ta, maimakon haka gaba suke yi da huruwan Ruhu mai-tsarki. Wadannan abubuwa sun zama abin sa shakka da rudewa ga mutane dayawa. Amma fa ba za a ce laifin Maganar Allah ne ba, saidai karkataswa da dan-Adam ya sa.MK 91.2

  Idan da zai yiwu halittattu su kai ga cikakken ganewar Allah da ayyukansa, to, idan suka kai ga wannan matsayi, ba za su dada gano wata sabuwar gaskiya ba, ba za su dada girma cikin ilmi ba, ko cin gaba na hankali ko zuciya. Allah ba zai zama shi ne mai mulkin komai ba, kuma idan dan-Adam ya kai ga kurewar ilmi, ba zai kara cin gaba ba. Bari mu gode wa Allah da shi ke abin ba haka ya ke ba. Allah ba shi da iyaka; a cikinsa “Wanda am boye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi chikinsa.” Kolosiyawa 2:3. Haka fa, har zuwa tsararraki, har abada, ‘yan-Adam za su dinga bincike su dinga koyo, ba kuwa za su iya kwashe dukiyar hikimarsa, da kirkinsa, da ikonsa dungum ba.MK 92.1

  Allah ya yi nufi ko a cikin wannan rai gaskiyar Magana tasa ta warwaru ga jama’a tasa. Hanya cfaya ce kacfai ta inda za a samu sanisa. Ta wurin haskakawar hasken Ruhun da aka ba da Maganar ta wurinsa kacfai za mu iya kaiwa ga gane Maganar Allah. “Hakanan kwa al’amuran Allah ba wanda ya sani, sai Ruhun Allah.” 1 Korinthiyawa 2:11. Gama Ruhu yana binchiken abu duka, i, har da zurfafa na Allah.” 1 Korinthiyawa 2:10.MK 92.2

  Kuma alkawarin Mai-ceto ga masu binsa shi ne, ‘ ’Amma sa’anda shi, Ruhu na gaskiya, ya fito, za ya bishe ku chikin dukan gaskiya, . . . amma dukan iyakar abin da ya ji, su zaya fadi; za ya bayana maku kuma abin da ke zuwa.” Yohanna 16:13, 14.MK 92.3

  Allah ya yi nufi cfan-Adam ya yi amfani da ikonsa na tunani, bi cikin Littafi Mai-tsarki kuwa zai karfafa, ya kuma dagad da hankali fiye da yadda ko wane irin bincike zai iya yi. Amma fa sai mu lura kada mu allahnta tunanimmu wanda ya ke da rashin karfi na mutunci. Idan ba mu so a dashe mana ganewarmu na litattafai masu tsarki har da ba za mu iya gane gaskiya mafi sauki ba, dole mu sumu saukin kai da bangaskiya irin ta yaro kankani,, a shirye domin mu koya, da kuma rokon taimakon Ruhu Mai-tsarki. Ya kamata sanin iko da hikima na Allah, da sanin gazawar mu na gane girmansa, su cika mu da tawali’u kuma ya kamata mu bude Magana tasa da kwarjini kamar sa’anda za mu shiga wurinsa. Idan muka zo ga Littafi Mai- tsarki tilas tunani ya yarda da ikon da ya fi shi, kuma dole zuciya da kwakwalwa su yi ruku’u ga babba wanda ya ce da kansa Ni Ne.MK 92.4

  Akwai abubuwa dayawa da su ke da wuya ko ba a fili ba wadanda Allah zai maishe su a fili, ko ya saukake su ga wacfanda su ke so su fahimce su. Amma im ba tare da bishewa na Ruhu Mai-tsarki ba, tutur zai yiwu mu dagulad da nassosi ko mu ba da ma’anarsu ba daidai ba. Akwai karatun Littafi Mai-tsarki mai yawa wanda ba a samun riba a cikinsa, a lokaci dayawa ma ya kan zama labari ne. Sa’an — da aka bude Maganar Allah ba tare da ladabi ba, ba kuwa tare da addu’a ba; sa’anda ba a kallafa tunani ga Allah ba, ko tunani ba ya cikin muwafaka da nufin Allah, sai hankali ya shiga shakka; kuma shakka ya dacfa karfi. Sai abokin gaba ya samu iko bisa tunani kuma ya ba da ma’anar da ba daidai ba ne. Duk sa’ad da ‘yan- Adam ba su neman muwafaka da Allah ko cikin tunani ko cikin aiki, to, hakika, komai zurfin ilmin karatunsu, yana yiwuwa su yi kure wajen fahimtar littattafi, kuma akwai hadari wajen yarda da ma’anar da za su bayar. Wadanda su ke dubuwa cikin litattafai domin su tono rashin jituwa, ba su da ikon ganin cikin abu na ruhaniya. Da karkataccen ido za su ga dalilan shakka da rashin ban¬gaskiya masu yawa cikin abubuwan da su ke a fili su ke, masu sauki kuma.MK 93.1

  Ko wane irin sake kama aka yi masa sau dayawa za a taras kaunar zunubi shi ne kwakkwaran daliiin yin shakka. Zuciya mai alfarma mai kaunar zunubi ba ta marhabin da koyaswa ko kafa iyaka na Maganar Allah, su kuwa wacfanda ba su lamunta su yi biyaiya da bukace-bukacenta ba, a shirye su ke su yi shakkar ikonta. Idan muna so mu kai ga gaskiya, dole mu kasance muna da sahihin nufi na son sanin gaskiya, kuma zuciyarmu ta lamunta ta yi biyaiya da gaskiyar. Kuma dukan wacfanda suka zo binciken litafi Mai- tsarki da wannan halin za su taras da shaida a yalwace cewa Maganar Allah ce, kuma za su ci ribar fahimtar gaskiya tasa wadda za ta sa su yi hikima zuwa ceto.MK 93.2

  Kristi ya ce, ‘ ’Idan kowane mutum yana da nufin ya aika nufin Allah, shi za ya sani ko abin da nike koyaswa na Allah ne ko domin kaina ni ke magana.” Yohanna 7:17. R.V. Maimakon yin tambayoyi ko gardama marassa karfi a kan abubuwan da ba ka fahimta ba, ka kula da hasken da ya ke haskakawa bisa kanka za ka kuwa karbi haske mafi girma. Ka aikata ko wane aiki wanda ka fahimta ta wurin alherin Kristi; za ka kuwa samu ikon da za ka fahimta ka kuma aikata wabanda ka ke shakkar su a yanzu.MK 93.3

  Akwai shaidar da ta ke a bude ga kowa — ga mai zurfin ilmi ko ga wanda bai iya karatu ba — shaida da ake samu daga ma amala na yau da gobe. Allah yana bidar mu mu tabbatawa kammu hakikanin Magana tasa, gaskiyar alkawarinsa. Yana bidan mu mu “dandana, mu duba, Ubangiji nagari ne.” Zabura 34:8. Mai makon mu dogara ga cewar wani, sai mu cfandana don kammu mu. Ya furta, Ko roko, za ku karba.” Yohanna 16:24. Za a cika alkawaransa. Ba su taba kasawa ba, ba kuwa za su kasa ba dacfai. Kuma cikin kusatowa ga Yesu, da yin farin ciki cikin cikakkiyar kauna tasa, shakkar mu da duhum mu zai bace cikin hasken kasancewarsa tare da mu.MK 94.1

  Bulus manzo ya ce Allah “Ya same mu daga cikin ikon dufu, ya mai- she mu zuwa cikin mulkin Da na kamnassa.”Kolossiyawa 1:13 Kuma dukan wanda ya ketare daga mutuwa zuwa rai ya iya ya “sa hatiminsa ga wannan, Allah mai-gaskiya ne.” Yohana 3:33. Ya iya shaida ya ce “Da ina bukatar taimako sai na samu Yesu. Am biya ko wace bukata, an kosad da yunwar ruhuna, yan zu kuwa a gareni Littafi Mai-tsarki shi ne baiyanuwar Kristi . Kana tambayar dom me na kwa ba da gaskiya ga Yesu? — Domin a gareni Shi Mai-ceto na sama ne. Dom me na ke gaskanta Littafi Mai-tsarki? — Domin na ga muryar Allah ne ga ruhuna.” Ya yiwu muna da shaida cikin kammu cewa Littafi Mai-tsarki gaskiya ne, kuma Kristi Dan Allah ne. Mun sani ba tatsuniyoyi da aka tsara su da wayo mai yawa mu ke bi ba.MK 94.2

  Bitrus ya yi wa ‘yan-uwansa galgad’i cewa, “Amma ku yi girma chikin alherin Ubangijimu Mai-chetonmu Yesu Kristi da saninsa.” II Bitrus 3:18. Sa’anda Jama’ar Allah su ke girma cikin alheri, tutur za su rika samun budaddiyar fahimtar Managa tasa. Za su ga sabon haske da jimali cikin gaskiya tata mai tsarki. Wannan ya zama gaskiya a tarihin Lkklisiya cikin tsararraki duka, haka kuwa zai daure har matuka. “Tafarkin mai-adilchi yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ke haskakawa gaba gaba har zuwa chikakkiyar rana.” Misalai 4:18.MK 94.3

  Ta wurin bangaskiya za mu iya duban gaba, mu ruski alkawarin Allah domin girman hankali, kwakwalwar mutunci tana haduwa da ruhaniya, kuma ko wane iko na ruhu ana kawo shi cikin gogaiya da masomin haske. Sai mu yi farin ciki cewa a sa’annan nan dukan abin da ya cude mana cikin al’amarin Allah za a faiyace mana shi; abubuwan da su ke da wuyan ganewa za a baiyana su; kuma inda han kulammu na mutunci suka taras da rudami da karayen nufe-nufe, za mu ga cikakken muwafaka mai jimali. “Gama yanzu chikin madubi muke gani a zauranche: amma sa’annan fuska da fuska: yanzu na sani bisa bisa; amma sa’annan zan sansanche kamar yadda an sansanche ni.” 1 Korinthiyawa 13:12.MK 94.4

  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents