Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    SANIN ALLAH

    Hanyoyi suna da yawa da Allah ya ke nema ya sanar da kansa garemu kuma ya kawo mu cikin taraiya da shi. Halitta tana zance da hankulammu ba fasawa. Zuciya budaddiya za ta gane kauna da daukaka na Allah yadda aka baiyana su cikin aikin kannuwansa. Kunne mai saurare zai ji ya kuma gane zantattukan Allah ta wurin abubuwan halitta. Ciyawa algashi, itatuwa masu tsawo, furarruka, gizagizai masu wucewa, ruwan sama, rafaffuka masu gudu, da dau- kakan sammai, suna zance da zukatammu, suna kirammu mu gane shi wanda ya halitta su duka.MK 71.1

    Mai-cetommu ya daure dukan koyaswa tasa game da abubuwan halitta. Itatuwa, tsuntsaye, furarruka na saura, tuddai, tekuna, da sararin sama mai jimali, tare da sauran abubuwan da ke kewaye da zama na yau da gobe, duka a hade su ke da zantattukan gaskiya, domin a rika tunawa da su ko wane lokaci, komai dawainiyar da mu ke ciki na yau da gobe.MK 71.2

    Allah yana so ‘ya’yansa su yaba da halittansa, su kuma yi farin ciki cikin sassaukan jimali da ya kawata mazaunimmu na duniya. Shi masoyin jimali ne amma fiye da dukan abu mai kyau na waje da ake gani, yana kaunar kyaun hali. Yana so mu shuka tsarki da rashin girman kai, kamar jimalin da fure ke bayarwa.MK 71.3

    Idan da za mu kasa kunne, sai ayukan halittar Allah su koya mana sosai nassi masu tamani na biyaiya da amincewa. Tun da ga taurari da su ke tafiyarsu cikin filin sama shekara kan shekara, har zuwa ga abu mafi kankanta, abubuwan halitta suna biyaiya da nufin Mahallici. Kuma Allah yana kula da ko wane abu yana kuma agazan dukan abin da ya halitta. Shi wanda ya ke tallafe da duniya masu yawa fiye da a kirga, Shi ya ke kula da ‘yar tsadda mai raira waka tata ba tare da tsoro ba. Sa’anda ‘yan-Adam suka fita zuwa wurin hidimarsu na ko yaushe, ko sa’anda su ke yin addu’a, sa’anda suka kwanta da dare, da sa’anda suka tashi daga barchi da safe, sa’anda mawadaci ya ke buki a fadarsa, ko sa’anda matalauci ya tara ‘ya’yansa su ci dan abin da suka samu, dukansu Uba na sama yana lura da su da kauna. Ba hawayen da zai zuba ba tare da sanin Allah ba Kuma babu murmushin da bai gani ba.MK 71.4

    In da za mu gaskanta wannan dungum, da dukan rashin kwan- ciyar rai ya kawu. Zaman mu ba zai zama da yawan rashin cikar muradimmu ba, domin ko wane abu, babba ko kankani cikin hannun Allah za mu bar su, wanda yawan abin kulawa ko nauyinsu ba su dame shi ba. A sa’annan za mu yi farin cikin kwanciyar rai wanda ya zama bakon abu ga mutane dayawa da dadewa.MK 72.1

    Kamar yadda hankulanku su ke murna a kan a abubuwan da suka kawata duniya, ku tuna da duniya mai zuwa wadda ba za ta san tabon zunubi ko mutuwa ba dadai, inda fuskar halitta ba za ta kara yafa inuwar la’ana ba. Bari hankalinku ya sifanta mazaunin cetattu, ku tuna kuma zai fi matukar kyalkyalin da hankalinku, zai iya sifantawa. A cikin baiwan Allah masu yawa daban daban, muna ganin kyallin cfaukakar halittarsa dushi dushi ne kawai. An rubuta cewa, “Abin da ido baya gani ba, kunne baya ji ba, Baya shiga zuchiyar mutum ba, dukan iyakar abin da Allah ya shirya ma wadanda ke kamnarsa.” 1 Korinthiyawa 2:9.MK 72.2

    Mawaka da mai duba fannin ilmi na halitta suna da abu dayawa da za su ce a kan halitta, amma mai bin Kristi ne ya ke jin dadin jimali na duniya, domin yana gane aikin hannuwan Ubansa, yana gani da hankalin zuciyarsa kaunar Allah, a jikin fure, ko ganye ko itace. Ba wanda zai iya gane dalilin tudu ko kwari, kogi ko teku, im ba ya dube su da kamar furtawar kaunar Allah ne zuwa ga dan- Adam ba.MK 72.3

    Allah yana magana da mu ta wurin shiryayyun ayukansa da ikon Ruhu Mai-tsarki bisa zuciya. A matsayin da mu ke da abin da ke kewaye da mu, cikin sake-saken da ke abkuwa a kewaye da mu kullun, za mu iya samun koyaswa masu tamani idan muka bar zukatammu a bude domin su gane su. Mai-Zabura da ya bincika, ayyukan shiri na Allah ya ce, “Duniya kuma chike ta ke da rahamar Ubangiji.” Zabura 33:5. ‘ ’Wanda ya ke da hikima duka, za ya lura da wadannan al’amura, su lura kuma da jiyejiyenkai na Ubangiji.” Zabura 107:43.MK 72.4

    Allah yana magana da mu cikin Kalma tasa. A nan ne mu ke ganin baiyanuwar halinsa a fili, da ma’amillansa da ‘yan-Adam da kuma babban aiki na pansa. A nan aka bucfe a gabam mu tarihin waliyyai, da Annabawa, da sauran tsarkaka na da. Su mutane ne “da tabi’a kamar lamu.’’ Yakub 5 :17. Mun ga yadda suka yi fama da katse- hanzari ga burinsu kamar mu da kuma yadda suka fadi cikin jaraba kamar mu, amma duk da haka suka dauki karfin zuciya suka kuwa ci nasarta tawurin alherin Allah, cikin ganin hakanan kuwa muna karfafa cikin kokarinmu ga yin adilci. Sa’anda muka karanta labaran abubuwan da suka abku garesu, da haske da kauna wanda suka zama abin faranta musu zuciya, da kuma aikin da suka aikata ta wurin alherin da aka ba su, sai ruhun da ya shiga cikinsu ya su yin haka ya kunna wutar kwaikwayo mai tsarki a cikin zukatammu, da kuma marmarin mu zama kamar su wajen hali — mu yi tafiya tare da Allah kamar yadda suka yi.MK 73.1

    Yesu ya ambaci Tsofon Alkawari — yaya fa gaskiyar wannan ya ke game da Sabon Alkawarin — cewa “Su ne fa suna shaida ta.’’ (Yohana 5:39), Shi Maiceto, wanda a cikinsa ne begen mu na rai na har abada ya tabbata. I, dukan Littafi Mai-tsarki yana ambatar Kristi ne. Tun daga farkon halitta, — domin “Ba a yi komi ba chikin abin da aka yi, sai ta wurinsa.” (Yohanna 1:3) — zuwa ga alkawari daga karshe wanda ya ce, “Ga shi, ina zuwa da samri.” (Ruya ta Yohanna 22:12), muna karanta labarin ayukansa muna kasa kunne ga murya tasa. Idan kuna so ku san Mai-ceto, ku karanta Littaftafai Masu-tsarki.MK 73.2

    Cika dukan zuciya da maganar Allah. Su ne ruwa mai rai, mai kashe kishirwa. Su ne gurasa mai rai daga sama. Yesu ya ce, “Im ba ku chi naman Dan mutum ba, ku sha jininsa kuma, ba ku da rai a chikinku ba’’ “Zantattuka wadanda na fada maku ruhu ne, da rai kuma.’’ Yohanna 6:53, 63. Jikunammmu suna ginuwa daga abin da muka ci da abin da muka sha; kamar yadda ya ke a cikin jiki kuwa, haka ya ke ga ruhu. Abin da mu ke tumani a kansa shi ne ya ke ba ruhum mu karfi.MK 73.3

    Zancen pansa abu ne wanda mala’iku su ke son bincikensa; shi ne zai zama fanni na ilmi da wakar pansassu cikin dukan tsararraki har abada. Ashe ba abu ne wanda ya cancanci a duba shi a yi tunam cikin hankali a kansa yanzu ba? Jinkai da kauna mara iyaka na Yesu, baikon da aka yi sabili da mu, suna bukatar a yi tunani mai zurfi a kansu. Sai mu zauna bisa kan halin kaunatacen Mai-pansarmu da Matsakancimmu. Sai mu yi tunani a kan aikin Shi wanda ya zo domin ya ceci mutane daga zunubansu. Idan muna tunanin abubuwa na sama haka, bangaskiyarmu da kaunar mu za ta yi karfi, addu’okinmmu kuma za su fi karbuwa ga Allah, domin za su dada garwayuwa da bangaskiya da kauna. Addu’oimmu za su zama masu ma’ana, kuma za a yi su da kwazo. Za a fi dada samun amincewa da Yesu, kuma kullum zamu dinga zama cikin sanin ikonsa na ceto har matuka, dukan wacfanda suka zo ga Allah ta wurinsa.MK 73.4

    Idan muna tunani a kan cika na Mai-ceto, za mu yi marmarin mu sake cfugum, za mu yi marmarin a sabonta mu cikin sifar tsarkinsa. Za mu yunwata mu kishirta a ruhu domin mu zama kamar shi wanda mu ke yi wa sujada. Gwargwadon tunanim mu a kan Kristi, gwar- gwadon yadda za mu yi wa wadansu zancensa, mu wakilce shi ga duniya.MK 74.1

    Ba domin malamai kadai aka rubata Littafi Mai-tsarki ba, an yi shi domin kowa ne. Manyan abubuwa na gaskiya da ake bukata domin ceto an nuna su a fili kamar hasken rana a tsaka; ba kuwa wacfanda za su yi kure har su bace daga hanya sai ko wadanda su ke bin shawarar kansu maimakon su bi baiyanannen nufi na Allah.MK 74.2

    Bai kamata mu karbi shaidar kowa akan abin da Littafi Mai-tsarki ya ke koyaswa ba, amma sai mu bi cikin zantattukan don kammu. Idan muka bari wadansu suka yi mana tunanin, kwazon mu da kokarim mu za su tauye. Ikokin hankali za su gajarta sabo da rashin watsa su a kan abin da ya kamatu su yi tunani a kai har za su rasa ikon da za su iya gane zurfin ma’ananr Kalmar Allah. Kwakwalwa za ta dacfa fadi idan ta maida hankali wajen binciken matsalolin da ke cikin Littafi Mai-tsarki, ta jarraba nassi da nassi, da abubuwa na ruha- niya da wasu abubuwa na ruhaniya.MK 74.3

    Babu abin da ya fi karfafa hankali kamar binciken Littattafai masu-tsarki. Ba wani littafin da ya ke da ikon dagad da tunani, ya wartsakad da kwakwalwa, kamar gaskiyarda ke cikin Littafi Mai- tsarki. Idan aka binciki Kalmar Allah kamar yadda ya kamata, ‘yan- Adam za su samu hankali mai fadi, hali mai kyau, da kafaffen nufi wanda ya ke da wuyan samu a zamani irin wannan.MK 74.4

    Amma fa ba a cin ribar kirki idan aka karanta Littafi Mai-tsarki cikin garaje da gaggawa. Mutum ya iya karanta Littafi Mai-tsarki daga farko har karshen amma ya kasa ganin jamalinsa, ko ya gane zurfin ma-ana tasa da ke boye a ciki. Idan aka dauki aya guda kadai aka bi cikinta sosai, aka kuwa gane ma’anarta, da mahadinta cikin shirin ceto, ya fi a karanta surori dayawa ba tare da wani nufi ba, ba a kuma samu wani abin koyo ba. Ka ajiye Littafi Mai-tsarki tare da kai; idan ka samu dama ka karanta, ka haddace ayoyin. Har in kana tafiya kan hanya ma ka iya karanta wata aya ka yi tunani a kanta, ka haddace ta.MK 75.1

    Ba shi yiwuwa mu samu hikima sai da kulawa da kwazo da bincike tare da addu’a. Hakika nassosi cikin Littafi Mai-tsarki a fili su ke har ba shi yiwuwa a kasa gane su, amma akwai wadansu ayoyin da ma’ana tasu ba a sama-sama su ke ba balle a gane su da cewa an duba. Dole a gwada wani nassi da wani nassin. Dole ne a bincike tare da zurfin tunani da addu’a. Irin wannan binciken kuwa zai ba da lada mai gwibi. Kamar yadda mai hakar dukiyar kasa ya kan kai ga jijiyar dalma ko karfe mai tamani a boye can cikin kasa, hakanan shi mai bicfar Kalmar Allah da naciya kamar wata boyayyar dukiya zai samu sahihiyar gaskiya mai tamani wadda aka boye ta daga idon mai nema ba tare da lura ba. Maganganu masu sukan rai, idan aka yi tunanin su a hankali cikin zuci, za su zama kamar rafuffuka masu gudu daga mabulbulan rai.MK 75.2

    Kada a yi binciken Littafi Mai-tsarki ba tare da addu’a ba dadai. Kafin mu fara bucfe warkokinsa sai mun roki wayewar azanci daga Ruhu Mai-tsarki, za a kuwa bayar. Sa’anda Natanayilu ya zo wurin Yesu, Mai-ceto ya ce “Duba, ga mutamen Israila na gaske, wanda ba shi da algus!” Daga ina ka san ni? “Kamin Filibbus ya yi kiran ka, sa’anda kana kalkashin itachen baure, na ganka.” Yohanna 1:47. 48. Mu ma Yesu zai gam mu a cikin Iollokin addu’a, idan muka neme shi domin ya haskaka mu, domin mu san abin da shi ke gaskiya. Mala’iku daga duniyar haske za su kasance tare da wacfannan da su ke neman koyaswa daga sama cikin tawali’u a zuciyar su.MK 75.3

    Ruhu Mai-tsarki yana cfaukaka Mai-ceto yana darajanta shi. Aikinsa ne ya nuna Kristi, ya nuna tsarkin adilcinsa, da babban ceton da muka samu ta wurinsa. Yesu ya ce a kan Ruhu Mai-tsarki, “Gama daga chikin nawa za ya karba, ya bayana maku kuma.” Yohanna 16:14. Ruhun gaskiya Shi ne kadai mai koyaswa na gaskiya ta sama. Ba da daraja kankanuwa Allah ya ke duban ‘yan-Adam ba tun da ya ba da Dansa ya mutu domin su, kuma ya nada Ruhu Mai- tsarki ya zama mai koya masu ya zama jagabansu tutur.MK 76.1

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents