Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
 • Results
 • Related
 • Featured
No results found for: "".
 • Weighted Relevancy
 • Content Sequence
 • Relevancy
 • Earliest First
 • Latest First
  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents

  TSARKAKEWA

  Alkawarin Allah shi ne “Za ku neme ni, ku same ni kuma, lokacin da ku ke nemana da zuchiya daya.” Irmiya 29:13.MK 35.1

  Sai a ba da dukan zuciya ga Allah, im ba haka ba, sakewar da ake bukata wadda za ta maishe mu ga soyaiya tasa ba za ta samu ba. Bisa ga tabi’a mu kebabbu ne daga Allah. Ruhu Mai-tsarki ya kwatanta matsayimmu da wadannan maganganu: “matattu cikin laifofi da zunubi.” “dukan kai yana ciwo, dukan zuciya ta yi suwu”; “babu lafiya a ciki.” A rike mu ke tsantsan cikin tarkon Shaitan, “Yayinda ku ke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku,” “dukan kai yana chiwo, zuchiya duk ta yi suwu;” “tun daga tafin tsawu har zuwa kai babu lafiya a chikinsa,” “Da shike bawan Ubangiji ya kama su da rai zuwa nufin Allah.” Afisawa 2:1; Ishaya 1:5, 6; 2 Timothawus 2:26. Allah yana so ya warkas da mu, ya ‘yantad da mu. Amma tun da ya ke ana bukatar sakewa dungum, da sabontuwar tabi’armu, sai mu bada kammu dungum zuwa gareshi.MK 35.2

  Yaki tsakanin dan-Adam da kansa shi ne yaki mafi tsanani da aka taba yi. Sai an yi kokawa mai tsanani idan ana so a ba da kai dungum cikin biyaiya da nufin Allah. Amma dole ne ruhu ya saduda Allah kafin a sabonta shi cikin tsarki.MK 35.3

  Mulkin Allah ba kan makantaccen biyaiya aka kafa shi kamar yadda Shaitan ya kan sifanta shi ba, ba kuma mulki ne mara ma’ana ba. Mulkin nan ya shafi hankali da lamiri. “Mu zo yanzu, mu yi binchike tare, in ji Ubangiji.” Ishaya 1:18. shi ne kiran da Mahalici ya ke yi ga halitta tasa. Allah ba ya tilasa nufin halittattunsa. Ba zai iya karbar sujada wadda ba tare da son rai da hankali aka yi ta ba. Baiyaya na tilas ya kan hana ci gaba na kwakwalwa da hali. Irin wannan ya kan mai da danAdam kamar keke da aka sa ya yi aiki ko da mai lurad da shi ko babu, kamar agogo. Ba wannan ne nufin Mai-halitta ba. Nufin sa ne dan-Adam, wanda shi ne gaba cikin halittasa, ya ci gaba ya kai matukar cin gaba. Ya sa matsayin albarkar da ya ke so ya kai mu ta wurin alherinsa a gabammu. Yana kiram mu mu ba da kammu gareshi, domin ya aikata nufinsa a cikimmu. Ya rage a wurimmu mu zaba ko za a yantad da mu daga bautar zunubi, mu zama masu taraiyar ‘yanci mai daraja na ‘ya’yan Allah.MK 35.4

  Cikin ba da kammu gareshi, dole ne mu bar duk irin abubuwan da za su raba mu da shi. Sabo da haka ne Mai-ceto ya ce, “Hakanan fa kowanene da ke chikinku da ba ya rabu da dukan abinda ke nasa ba, ba shi da iko shi zama mai-bina ba.” Luka 14:33. Sai a bar ko wane abin da zai janye zuciya daga Allah. Duniya ita ce gumkin ‘yan-Adam masu yawa. Kaunar kudi, son wadata, su ne sarka ta zinariya da ta daure su hade da Shaitan. Wadansu kuwa samun suna da girman duniya su ke yi wa sujada. Wadansu kuma zaman son kai mai sauki da rashin daukar nawaiyar komai su suka mayar gumakansu. Amma dole a tsintsinka wadannan igiyoyi na bauta. Ba shi yiwuwa rabim mu ya zama na Allah, daya rabin kuwa ya zama na duniya. Mu ba ‘ya’yan Allah ba ne sai mun ba da kammu dungum. Akwai wadansu da su ke ce suna bauta wa Allah, amma suna dogara ga karfin kansu wajen biyaiya da doka tasa, suna dogara ga karfin kansu su yi hali mai kyau, suna dogara ga karfin kansu su samu ceto. Zukatansu ba su motsu da sanin zurfin kaunar Kristi ba, amma suna nema su aikata abubuwan da ya kamata Mai bi ya aikata kamar shi ne abin da Allah ya ke bukata daga garesu kafin su samu mulkinsa. Irin wannan addini bai dada komai ba, ba shi kuwa da wani amfani. Sa’anda Kristi ya shiga ya zauna cikin zuciya, ruhu zai cika da kauna tasa zai cika da farin cikin zuciya da taraiya da shi, har ya manne masa, kuma cikin tunawa da shi, sai ya manta da kansa. Kauna zuwa ga Kristi shi ne zai zama masomin aiki. Su wadanda suka ji rinjayar kaunar Allah ba sua tambayar kankantar abin da za a bayar domin a cika muradin Allah, ba su’a tambayar matsayi na kasa, amma suna da burin cikakken muwafaka da nufin Mai-pansarsu.Da himma su kan ba da duka, kuma su nuna kulawa tasu gwargwadon tamanin abin da su ke bida. Furta ban- gaskiya ga Kristi ba tare da wannan kauna mai zurfi ba, maganar lebe ne kawai, busashshen abu, aikin wahalaswa kawai.MK 37.1

  Kana ji a ranka cewa bayar da duka ga Kristi babban hadaya ne da bai kamata ba? Tambayi kanka wannan tambaya, “Me Kristi ya ba ni?” Dan Allah ya ba da duka, — rai, da kauna, da radadi, — domin pansarmu. Ya zama fa mu, wacfanda ba mu cancanci wannan babbar kauna ba, mu hana shi zukatammu? Ko wane minti na zama- mmu na duniya muna diba daga cikin albarkar alherinsa, sabili da wannan ne ba za mu iya gane zurfin jahilci da bacin zuciyar da aka tsamo mu daga ciki ba. Mua iya dubansa wanda zunubammu suka soka, sa’annan mu ki yarda mu aikata nufin kaunarsa da hadaya tasa? Idan muka duba kaskancin da Ubangijin daraja ya sha, ya yiwu mu yi wani gunaguni idan ya zamana kafin mu samu rai sai mun sha gwagwarmaya da kaskantar da kanmu.MK 38.1

  Tambayar da masu fadin rai su ke yi shi ne, “Me zai sa sai na tuba na kaskanta kaina kafin in samu tabbatawar cewa Allah zai karbe ni?” Na ce ku dubi Kristi. Shi ba shi da zunubi, kuma har ya fi haka, Shi sarkin sama, amma domin dan-Adam ya zama zunubi sabo da jama’a. “Aka lissafta shi wurin masu-laifi: duk da haka ya dauki zunubi na mutane dayawa, ya kuma yi roko sabili da masu- laifi.” Ishaya 53:12.MK 38.2

  To, amma me muka bari idan muka bayar da duka? —Zuciya kazantacciya da zunubi, domin Yesu ya tsarkake, ya tsabtace ta ta wurin jininsa na kansa, kuma ya cetar ta wurin kauna tasa mafi abin kwatantawa. Amma duk da haka ‘yan-Adam suna tsammani abu ne mai wuya a bayar da duka. Ina jin kunya in ji an fadi haka, kuma ina jin kunya in rubuta hakanan.MK 38.3

  Allah ba ya so mu bar irin abin da shi ke yana da amfani a garemu wanda ya yiwu mu rike. Cikin dukan abin da ya ke yi, jin dadin ‘ya’- yansa shi ne ya sa a gaba. Duk sammai suna kula da jin dadin dan-Adam. Ubammu na sama bai rufe wa ko wane daga cikin halitta- ttunsa kofofin jin dadi ba. Bukace-bukacen Allah su ne yana kiram mu mu bar nishacf-nishacfe da za su jawo mana wahala da karayar zuciya, wacfanda za su rufe mana kofofin farin ciki na sama Mai-pansar duniya yana karban yan-Adam yadda su ke, da bukace-bukacensu, da rashin cikassu, da rashin karfinsu, kuma ba tsabtace su daga zunubi da ba su pansa ta wurin jininsa kadai zai yi ba, amma zai biya dukan muradin wadanda suka yarda suka sa karkiya tasa a wuyansu, suka yarda su dauki kayansa. Nufinsa ne ya ba da salama da hutu ga dukan wadanda suka zo wurinsa domin su samu gurasa ta rai. Ayyukan da ya ke bukata daga garemu su ne wadanda za su bi da sawayen mu zuwa ga matukar albarka wadda kangararru ba za su iya kaiwa ba dacfai. Farin ciki mai gaskiya na ruhu shi ne samun Kristi ya sifantu daga cikin zuciya, ya zama begen daraja.MK 38.4

  Dayawa suna tambaya “Yaya zan ba da kaina dungum ga Allah?” Kana da nufin ka ba da kanka gareshi amma ba ka da karfin ran da za ka yi hakanan in kana cikin bautar shakka, kuma idan tabi’unka na zunubi su na mulki da kai. Dukan alkawaranka da kudurinka kamar igiyoyin rairayi ne suke. Ba ka iya mulkin tunaninka da tunanin da su kan zo maka farat daya ba tare da shiri ba, ba ka da iko kan nufe-nufen zuciyarka. Sanin karya alkawaranka da lamuninka da ka dauka su kan raunana bangaskiyarka cikin gaskiyar nufinka, su kan sa ka ji a ranka cewa Allah ba zai karbe ka ba, amma kada ka fid da zuciya. Abin da ya kamata ka gane shi ne karfin gaskiya na nufi. Wannan shi ke mulki bisa tabi’ar dan-Adam, ikon zartaswa ko zabe. Komai ya rataya ga aikatawa daidai na hankali. Allah ya ba ‘yan-Adam ikon zabe, nasu ne su yi aiki da wannan iko. Ba shi yiwuwa ka sake zuciyarka; ba shi yiwuwa don kanka ka ba Allah kaunar nan ta zuci, amma ka iya zaben ka bauta masa. Ka iya ba shi hankalinka, a sa’annan ne zai iya aiki ya sa ka nufa ka kuma aikata daidai da jin dadinsa mai kyau. Ta haka nan za a kawo duk tabi’arka karkashin ikon Ruhun Kristi; duk kaunarka za ta tattaru bisa kansa, tunaninka za su zama cikin muwafaka da shi.MK 39.1

  Nufin aikata abin kirki da kasancewa cikin tsarkaka daidai ne don kansu, amma idan ka tsaya nan ba za su dada komai ba. Dayawa za su bata idan suka tsaya kan bege da nufin su zama masu bin Kristi kawai. Ba su kai ga matasayin ba da hankalinsu ga Allah ba. A yanzu ba su zabi su zama masu bin Kristi ba.MK 39.2

  Ta wurin aiki da hankali yadda ya kamata za ya yiwu ka sa ke irin zamanka dungum. Ta wurin ba da hankalinka ga Kristi, sai ka shiga cikin amana da iko wanda ya fi dukan mulkoki da ikoki. Za ka samu karfi daga bisa wanda zai rike ka a tsaye sosai, kuma ta wajen ba da kai dungum ga Allah za ka iya zaman sabon rai, i, zaman ran nan na bangaskiya.MK 39.3

  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents