Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    AMFANIN ADDU’A

    Ta wurin halitta da wahayi, ta wurin tanajinsa, da ikon Ruhu Mai-tsarki, Allah ya ke magana da mu. Amma wacfannan ba su isa ba; ana bukata mu zazzage masa zukatammu. Idan muna so mu samu rai mai ruhaniya da zafin jiki, dole mu shiga cudaiya da Ubammu na sama. Tilas sai a jawo hankulam mu zuwa gare Shi, mu yi tunani a kan ayyukansa, da jiyejiyenkansa, da albarkansa masu yawa; amma wannan kadai ba shi ne taraiya da shi ba. Idan muna son taraiya da Allah, dole mu samu wani abin da za mu fada masa game da ainihin zaman mu na duniya.MK 77.1

    Addu’a ita ce bude zuciya ga Allah kamar ga aboki. Ba wai don lalai ne mu sanas da Allah ko mu wane ne ba, amma domin ya yiwu a garemu mu karbe shi. Addu’a ba ta sauko da Allah zuwa wurin mu amma kai mu sama wurinsa ta ke yi.MK 77.2

    Sa’anda Yesu ya ke nan duniya ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a. Ya umurce su su kai bukace-bukacen su na yau da gobe gaban Allah, kuma su rataya masa dukan ma’amalansu. Alkawarin da ya yi musu na cewa za a ji roke-rokensu alkawari ne a gare mu har wa yau.MK 77.3

    Yesu da kansa, sa’anda ya ke zaune a tare da yan-Adam addua ya ke yi a kowane lokaci. Mai-cetommu ya nuna kansa daidai ya ke da mu wajen rashin karfi da bukace-bukace domin ya zama mai roko, mai neman karfi da taimako daga wurin Ubansa, domin ya samu karfin fita wajen aiki. Shi ne abin misali a garemu cikin komai. Shi cfan-uwa ne cikin rashin karfimmu, “an jarabce shi ta ko wace hanya, kamar mu”, amma kamar mara zunubi, tabi’arsa ta yi nesa da zunubi. Ya daure kokawa da addu’a da azabar ruhu cikin duniya mai zunubi. Tsare mutuncinsa ta sa addu’a ta zama dole ne. Ya samu ta’aziya da farin zuciya cikin zance da Ubansa. Idan fa Mai-ceton ‘yan-Adam, Dan Allah, ya ji bukatar addu’a, yaya ‘yan-Adam, masu zunubi, marassa karfi za su ji bukatar addu’a da himma ko wane lokaci?MK 77.4

    Ubammu na sama yana jira ya zuba mana cikakkiyar albarkassa. Halaliyarmu ne mu sha ruwa yadda mu ke so daga mabulbulan kauna mara iyaka. Abin mamaki ne cewa ba mu yin addu’a dayawa. Allah a shirye ya ke ya ji addu’ar gaskiya daga mafi kaskanta daga cikin ‘ya’yansa, amma muna nuna rashin so a fill mu sanar da Allah bukace- bukacem mu. Me mala’iku na sama za su yi tsammani a kan ‘yan- Adam marassa karfi, marassa taimako, wadanda za su iya jarabtuwa, ga shi kuwa zuciyar Allah cike ta ke da kauna mara iyaka tana bidar su, tana shirye ta ba su fiye da abin da za su iya roko, amma duk da haka ba su yin addu’a dayawa, kuma bangaskiyarsu kadan ce? Mala’iku suna kaunar su yi ruku’u a gaban Allah, suna kaunar su kasance kusa da shi. Sun dauki taraiya da Allah ya zama babban abin farin cikin su, amma ‘ya’yan duniya wacfanda suka fi bukatar taimakon da Allah ne kadai zai bayar, sun nuna kammar sun fi so su yi tafiyarsu ba tare da hasken Ruhunsa ba, da zama ba tare da shi ba.MK 77.5

    Duhun mai muguntar yana kewaye wacfannan da suka wakala yin addu’a. Jarabun da abokin gaba ya ke yi musu rada cikin kunnu- wansu suna rudin su su yi zunubi, duka wannan kuwa domin ba su yi anfani da yarjin da Allah ya ba su ba ne cikin ayyana addu’a. Dom mene ne ‘ya’yan Allah maza da mata za su ji nauyin yin addu’a sa’anda addu’a ita ce mabudi cikin hannun bangaskiya da za ta bude gidan ajiya na sama, inda aka ajiye taimakon da ba su da iyaka na Mai-iko duka? Im ba tare da addu’a da tsaro ba fasawa ba, muna cikin hadarin zama cikin rashin kulawa da karkacewa daga kan hanyar gaskiya. Ko wane lokaci abokin gaba yana neman ya sa abin tuntube kan hanya zuwa mazaunin jinkai, domin kada mu samu alheri da ikon tsayaiya da jaraba ta wurin roko da bangaskiya.MK 79.1

    Akwai wasu sharuda wancfanda ta wurin su za mu yi begen cewa Allah zai ji ya kuma karbi addu’o’immu. Daya daga cikin na farkon wacfannan sharadu shi ne mu ji bukatar taimako daga gareshi. Ya yi alkawari cewa “Gama zan zuba ruwa a bisa wanda ya ke jin kishi, rafufuka kuma bisa busashiyar kasa.” Ishaya 44:3. Su wadanda su ke yunwata da kishirta zuwa adilci, wadanda su ke marmarin Allah, su tabbata cewa za a kosad da su. Dole zuciya ta budu ga ikon Ruhu, im ba haka ba ba za a iya karban albarkar Allah ba.MK 79.2

    Babban bukatar mu muhimmi abin mahawara ne, yana kuwa robo sabili da mu da Iafazi mai girma. Amma sai a nemi Allah ya yi wada- nnan abubuwa domin mu. Ya ce, Ku roka za a baku. Wanda baya kebe Da nasa ba, amma ya bashe shi domin mu duka, kaka za ya rasa bamu abu duka kuma tare da shi a yalwache?” Matta 7:7; Romawa 8:32.MK 79.3

    Idan muka bar mugu daya tak cikin zukatam mu, ko muka mannewa ko wane irin zunubin da aka sani, Ubangiji ba zai ji mu ba; amma addu’ar mai tuba da karyayyan ruhu abin karba ne ko wane lokaci. Idan aka daidaita dukan laifofin da aka sani, za mu iya gaskanta cewa Allah zai amsa roke-rokemmu. Kirkin mu kawai ba zai koda mu mu ruski rahamar Allah ba, isar Yesu ne za ta cece mu, jininsa ne zai tsabtace mu, duk da haka muna da aikin da za mu yi na kiyaye sharudan karba.MK 80.1

    Wannan abu game da addu’a kuma shi ne bangaskiya. “Gama mai- zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai- sakawa ne ga wadanda ke bidassa.’’ Ibraniyawa 11:6. Yesu ya ce wa almajiransa, “Dukan iyakar abin da ku ke addu’a kuna roka kuma, ku bada gaskiya kun rigaya kun karba, za ku samu fa.’’ Marku 11:24. Ko muna daukansa kan magana tasa?MK 80.2

    Wannan tabbatarwa yana da fadi, ba shi kuwa da matukan tsawo; Shi kuma wanda ya yi alkawarin mai aminci ne. Sa’anda ba mu karbi ainihin abubuwan da muka roka ba, a lokacin da muka roka, duk da haka sai mu gaskanta Allah yana ji, zai kuwa amsa addu’o’immu. Mu masu kuskure ne, marassa hangen nesa, har wani lokaci mu kan roki abubuwan da ba za su zama albarka a garemu ba, Ubammu na sama kuwa cikin kauna ya kan amsa addu’o’immu ta wurin ba mu abin da zai fi mana amfani, abubuwan da za mu so don kam mu in da tsinkayar mu ta iya hangen abubuwa yadda su ke ta wurin hasken da za mu samu daga sama. Sa’anda muka ga kamar ba a amsa addu’o’immu ba, mu dai sai mu manne wa alkawarin; gama babu shakka lokacin amsawa zai zo, kuma za mu karbi albarkar da muka fi bukata. Amma tsayawa kan cewa za a amsa addu’o’immu a daidai hanyar da muka roka da kuma ainihin abin da muka roka ba daidai ba ne. Hikimar Allah ta fi gaban ya kure, nagarta tasa kuma ta fi karfin ta hana abubuwa masu kyau ga wacfanda su ke tafiya sosai. Don haka kada ku ji tsoron amincewa da shi ko ya zamana ba ku ga amsar addu’o’inku nan da nan ba. Ku dogara kan tabbataccen alkawarinsa da ya ce, “Ku roka, za a ba ku.” Matta 7:7.MK 80.3

    Idan muka shiga cikin yin shawara da shakkokimmu ko tsoracce- tsoracemmu, ko muka so mu warware ko wane abu wanda ba mu san kansa ba, tun kafin mu samu bangaskiya, sai rudamu ya dada karuwa da zurfi kawai. Amma idan muka zo ga Allah da sanin rashin karfim mu da bukatar madogara, kuma da bangaskiya mai tawali’u, mai amincewa, muka sanas da shi wanda ba shi da iyaka bukatammu, Shi wanda ke ganin komai na cikin halitta, Shi wanda ya ke mulkin komai, da nufinsa da magana tasa, zai iya, zai kuma ji kukammu, zai kuwa bar haske ya haskaka zukatammu. Ta wurin addu’a ne ake kawo mu cikin haduwa da hankalin Madauwamin watakila ba za mu samu wani shaida mai ban mamaki a lokacin ba cewa fuskar Mai-pansarmu tana sunkuyawa bisa kam mu cikin tausayi da kauna, amma kuwa lallai haka ne. Ya yiwu ba za mu ji tabawar hannunsa a jikim mu ba, amma hannuwansa suna bisa kam mu cikin kauna da juyayi mai taushi.MK 81.1

    Sa’anda muka zo rokon jinkai da albarka daga wurin Allah, ya kamata mu kasance da ruhun kauna da gafara cikin zukatam mu. Yaya za mu iya yin addu’a mu ce “Ka gafarta mana bassussuwan mu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.” Matta 6:12. amma mu zauna cikin halin kin yin gafara? Idan muna so a ji addu’o’immu, sai mu gafartawa wacfansu daidai gwargwadon yadda mu ke begen za a gafarta mana.MK 81.2

    Naciya wajen yin addu’a yana cfaya daga cikin sharudan karba Sai mu yi addu’a ko wane lokaci idan muna so mu yi girma cikin bangaskiya da wayewar kai. Sai mu lizima cikin addu’a mu ‘ yi tsaro da godiya kuma a cikinta Romawa 12:12; Kolosiyawa 4:2. Bitrus ya hori masu ba da gaskiya cewa, “Ku yi rai shimfide zuwa ga addu’a.” 1 Bitrus 4:7. Bulus kuma ya yi umumi cewa “Chikin kowane abu, ta wurin addu’a da roko tare da godiya, ku bar roke-rokenku su sannu ga Allah.” Filibbiyawa 4:6. “Kuna addu’a chikin Ruhu Mai-tsarki, ku tsare kanku chikin kamnar Allah.” Yahuda 20:21. Addu’a ba fasawa shi ne maganin ruhu da Allah wanda ba ya karyewa, domin rai daga Allah ya dinga gudano zuwa cikin rayukanmu, daga ram mu kuma sahihanci da tsarki su koma ga Allah.MK 81.3

    Akwai dalilin bukatar naciya cikin addu’a; kada ku bari komai ya hana ku. Ku yi iyakacin kokarinku ku bude hanyar zance tsakanin ruhohinku da Yesu. Ku nemi ko wane dama da za ku tafi wurin da ake yin addu’a. Duk wadanda su ke ne man zance da Allah da gaskiya, za a gan su wajen taron addu’a, da amincin aikata wajibinsu, kuma suna himma domin su girbe duk iyakacin albarkan da za su iya samu. Za su gyara daman da suka samu domin su sa kansu inda za su iya samun haske daga sama.MK 81.4

    Ya kamata mu yi addu’a tare da iyalin mu, gaba da komai kuma kada mu bar yin addu’a ta kadaituwa, gama wannan shi ne cibiyar ruhu. Ba shi yiwuwa ruhu ya yi girma idan aka bar yin addu’a. Addu’a cikin iyali ko cikin tare kadai bai isa ba. Addu’ar boye Allah mai jin addu’a ne kadai ke jin ta. Ba kunnen wani da zai ji. A cikin addu’ar boye ruhu a sake ya ke daga daukewar hankali, abubuwan da ke kewaye da shi, ga kuma natsuwa. Cikin hankali, amma da himma, za ta isa wurin Allah. Iko ne mai zaki, mai tsayawa wanda zai fito daga gareshi Mai-gani daga cikin boye, wanda kunnensa a bude su ke domin ya ji addu’ar da ke tasowa daga zuci. Ta wurin bangaskiya natsatstsiya ruhu ya ke zance da Allah ya kuma tattara wa kansa haske na sama domin ya ciyad da shi, ya karfafa shi cikin fada da Shaitan. Allah shi ne hasumiyar kaifim mu.MK 82.1

    Ku yi addu’a can cikin boye, bari kuma zukatanku su daga kansu ga Allah a ko wane lokaci ko cikin tafiya zuwa wajen dawainiya na yau da gobe. Ta haka ne Anuhu ya yi tafiya tare da Allah. Wadannan addu’o’i na zuci kamar turare mai kamshi su ke a gaban kursiyin alheri. Shaitan ba zai iya rinjayar shi wannan wanda zuciya tasa ta ke dogara ga Allah ba.MK 82.2

    Babu wani lokaci ko wuri wanda za a ce bai yi kyau a roki Allah ba. Babu abin da zai hana mu daga zukatammu cikin ruhun addu’a mai himma. Cikin jama’a a kan hanya, ko cikin wani kasafi, za mu iya aikawa da rokom mu zuwa ga Allah domin mu samu bayaswa daga sama, kamar yadda Nehemiah ya yi sa’anda ya yi rokonsa a gaban Sarki Artaxerxes. A iya samun kebabben wuri a ko ‘ina domin a yi zance da shi a inda mu ke duka. Sai mu bar kofar zuciya a bude tutur, kuma mu aika mu gaiyato Yesu ya zo ya zauna ya zama bakon cikin ruhu.MK 82.3

    Ko da a ce a kewaye da mu akwai iskar kazanta, ba lalai sai mun shake ta ba, amma za mu iya rayuwa cikin sahihiyar iska ta sama. Ya yiwu mu rufe wa miyagun tunai ko wace kofa ta wurin daga ruhu zuwa gaban Allah cikin addu’a sahihiya. Wadannan da zukatan su a bude su ke su karbi tallafa da albarkar Allah, za su yi tafiya cikin iska wadda ta fi ta duniya tsarki, za su kuwa kasance cikin zance da Allah tutur.MK 82.4

    Ba lallai sai mun sami wani kwakkwaran tunani kan yadda muka mai da Yesu ba, ko dada ganewar tamanin hakikatattun al’amura madawami. Jimalin tsarki shi ne zai cika zuciyar ‘ya’yan Allah, idan ana son haka kuwa sai mu nemi wayewar kai daga sama a kan abubuwa na sama.MK 84.1

    Bari a jawo ruhu waje zuwa sama domin Allah ya ba mu numfashin iskar sama. Za mu iya kasancewa kusa da shi har zai zamana a cikin ko wane gwaji wanda zai zo mana ba tare da shiri ba, za mu iya juyawa ga Allah kamar yadda fure ya kan juya ga rana.MK 84.2

    Ku ajiye dukan bukace-bukacenku, da farin cikinku, da bakin cikin ku da abubuwan da suka dame ku a rai, da abubuwan da ku ke ban tsoro, a gaban Allah. Ba za ku iya nawaita masa ba, ba za ku iya gajiyad da shi ba. Shi wanda ya kididdige gasusuwan kawunanku bai manta da bukace-bukacen ‘ya’yansa ba. “Ubangiji da shi ke chike da tausayi, mai-jinkai ne kuma.” Yakub 5:11. Zuciya tasa ta kauna ta kan soku da bakin cikim mu, ko ambata su muka yi kawai. Ku kai masa dukan abin da ya faskari tunanin ku. Babu abin da ya yi masa girma domin dauka, gama shi ke rike da duniyoyi. Shi ke da mulki bisa dukan matsalan halita. Babu wani abin da ya shafi salamar mu wanda ya cika kankanta har da ba zai kula da shi ba. Babu wata sura cikin abubuwan da suka shafe mu wadda bakinta ya yi yawa har da ba zai iya karanta ta ba. Babu wata dagulalliyar matsala da ta cika wuya har da ba zai iya warware ta ba. Babu wani mugun abu da zai samu mafi kankanta daga cikin ‘ya’yansa, babu wani tashin hankali da zai dami ruhu. ko farin ciki ya karfafa zuciya, ko sahihiyar addu’a ta fita daga lebuna, wanda Ubammu na sama bai sani ba, ko kuwa wanda bai kula da su ba. “Yana warkadda masu-karyayyar zuchiya, yana damre miyakunsu.” Zabura 147:3. Dan- gantaka tsakanin Allah da ko wane mai rai daban ya ke, cikakke ne kuma, har ya zama kamar ba wani mai ran da kaunataccen Dansa bai mutu dominsa sai Shi kadai ba.MK 84.3

    Yesu ya ce “Za ku yi roko a chikin sunana: kuma ban che maku, ni yi addu’a ga Uba domin ku ba, gama Uba da kansa yana kamnarku.” “Ni ne na zabe ku, na sanya ku kuma domin ku tafi ku bada yaya. . . . domin dukan iyakar abin da za ku roka ga Uba a chikin sunana, shi ba ku.” Yohanna 16:26, 27; 15:16. Amma a yi addu’a cikin sunan Yesu ya fi gaban ambaton sunan nan a farko ko a karshen addu’a. Sai a yi addu’a cikin hankali da ruhu na Yesu, sa’anda mu ke gaskanta alkawaransa, muna dogara ga alherinsa, muna aikata ayyukansa.MK 84.4

    Allah ba ya nufi dukammu mu zama waliyyai, ko sufi ko mu janye kammu dungum daga duniya mu mayar kan ibada. Zamam mu sai ya zama kamar na Kristi — tsakanin dutse da taron mutane. Shi wanda ba ya yin komai sai addu’a, ba za a dade ba zai bar yin addu’a, imma ba haka ba addu’oinsa za su zama maimaitawa ne kawai. Sa’anda yan-Adam suka tsame kansu daga cudanya da sauran ‘yan-uwansu, suka saukakewa kansu wajibin mai bin Kristi da daukan giciye, sa’anda suka daina aiki da himma sabo da Ubangiji wanda ya yi aiki da hikima domin su, lallai kuwayar addu’a ta bace musu, kuma ba su da abin da zai iza su ga ibada. Sai addu’o’insu su zama don kansu su ke yi da son kai a ciki. Ba za su iya yin addu’a sabo da bukatar ‘yan-Adam ba ko domin ginin mulkin Kristi, ko rokon karfin da za su iya yin aikin.MK 85.1

    Muna yin hasara sa’anda muka yas da daman cudanya da juna domin mu karfafa juna cikin hidimar Allah. Gaskiyar Kalmominsa su kan rasa ma’ana tasu ko nauyinsu cikin han kulammu. Zukatammu sai su daina samun haske ko su kasa farkawa ta wurin ikonsa mai tsarkakewa, kuma sai mu ragu cikin ruhaniya. Cikin goguwar mu da juna kamar masu bin Kristi, mu kan yi rashi dayawa sabo da rashin jin tausayin juna. Shi wanda ya je ya boye kansa ba ya cika mutsayin da Allah ke nufinsa da shi ba. Cudanya da juna bisa ga tabi’armu ta ‘yan-Adam cikin hanyar da ke daidai za su sa mu ji tausayin junan mu, kuma han>. ce ta ciyad da mu gaba da karfi cikin hidimar Allah.MK 85.2

    Inda masu bin Kristi za su yi cudanya da juna, suna zance da juna kan kaunar Allah da kan gaskiya mai tamani na pansa, sai zukatansu su wartsake kuma su wartsakad da juna. Ya yiwu kullun mu dada koyon wani abu game da Ubammu na sama, muna cin riban dada wayewar kai na alherinsa, sa’annan za mu yi marmarin yin zance kan kauna tasa; idan muna yi haka, zukatammu za su yi tuni, su dacfa karfafa. Idan muna dada tunani da zance kan Yesu ba kam mu ba, za mu dacfa fin samun kasancewarsa tare da mu.MK 85.3

    Idan da za mu yi tunanin Allah a ko wane lokaci kamar yadda mu ke ganin shaidar kulawa da mu da ya ke yi, za mu kiyaye shi tutur cikin tunanimmu, mu yi farin ciki cikin zance a kansa da yabonsa. Mu kan yi zance a kan abubuwa na duniya masu wucewa domin muna kula da su. Mu kan yi zance a kan abokanmu domin muna kaunarsu; farin cikimmu da bacin ram mu a daure su ke da su. Duk da haka akwai babban dalili mara iyaka da zai sa mu fi kaunar Allah da abokammu na duniya, ya kamata kuwa ya zama tabi’a a garemmu mu maishe shi na farko cikin dukan tunanimmu, mu yi zancen alherinsa, mu fadi ikonsa. Ba a ce wadatattun baiwan da ya yi mana su dauke hankulammu da kaunar mu har da za mu rasa abin da za mu ba Allah ba, su ne za su rika tuna mana da shi tutur, su daure mu da igiyoyin kauna da godiya ga Ubangijimmu. Mazaunimmu ya cika kusa da kwarurukan duniya. Bari mu daga idanummu mu dubi budaddiyar kofa ta mafaka a sama, inda hasken darajar Allah ke haskakawa bisa fuskar Kristi wanda “Domin wannan yana da iko ya yiwo cheto ba iyaka domin wadanda ke kusantuwa ga Allah ta wurinsa.” Ibraniyawa 7:25.MK 86.1

    Dole mu fi yabon Allah “Da dai mutane suka yarda su yabi Ubangiji domin alherinsa, Da al’ajibansa da ya ke yi ma yan adam kuma.” Zabura 107:8. Bai kamata dukan ayyukan ibadarmu su zama na roko ne da karba ba. Kada ko wane lokaci mu rika tunani a kan bukace-bukacemmu, kada kuma mu tuna da abubuwan da muka karba. Kada mu yi zaton addu’o’immu sun yi yawa, amma godiyarmu ta yi kadan. Mu masu karban jinkan Allah ne tutur, amma duk da haka godiyar da mu ke furtawa kacfan ne, yabonsa da mu ke yi kuma sabili da abin da ya yi mana kadan ne ainun.MK 86.2

    A zamanin da Ubangiji ya ce wa ‘ya’yan Isra’ila, sa’anda suka taru domin su yi masa sujada, “Chan fa zaku chi a gaban Ubangiji Allahnku, za ku yi murna kuma da iyakachin abin da ku ke sa hannu gareshi, da ku da iyalanku, abin da Ubangiji Allahnka ya albarkache ka a chiki. Kubawar Shari’a 12:7. Abin da za a yi shi domin darajar Allah sai a yi shi da dadin rai, da wakokin yabo, da godiya, ba cikin bacin rai da daure fuska ba.MK 86.3

    Allahmmu Uba ne mai jinkai. Bai kamata a dubi hidimarsa kamar aiki ne mai bakanta rai ba. Ya kamata sujada ga Allah da taimakawa cikin yin aikinsa su zama abin dagadda zuciya. Allah ba ya so ‘ya’yansa, wadanda sabili da su aka shirya ceto mai girma, su aikata kamar cewa shi Ubangida ne mai fitina, mai matsa wa barorinsa. Shi abokinsu ne fiye da kowa, kuma lokacin da su ke yi masa sujada, yana so ya kasance tare da su, ya albarkace su, ya yi musu ta’aziya, yana cika zukatansu da farin ciki da kauna. Ubangiji yana so ‘ya’yansa su ta’azantu cikin hidimar sa, su kuma fi samun dadin rai fiye da wahala cikin hidimarsa. Yana sa wacfanda suka zo yi nasa sujada su koma da tunanin kulawa tasa da kauna tasa, domin su karfafa cikin dawainiyarsu na yau da gobe, domin su sami alherin yin gaskiya da aminci cikin dukan abubuwa. Dole mu taru kewaye da giciye. Kristi da Shi giciyayye shi ne zaya zama abin tunawar mu, abin tadim mu, da abin farin cikim mu. Sai mu kiyaye cikin tunanimmu ko wace albraka da muka karba daga wurin Allah, kuma idan muka lura da kauna tasa mai girma, sai mu lamunta mu danka ko wane abu cikin hannun da aka kafa da kusa bisa giciye domim mu.MK 86.4

    Ruhu ya hau sama kusa da aljanna bisa fukafukan yabo. Ana yi wa Allah sujada da waka da bushe-bushe a can fada ta sama, kuma sa’anda mu ke furta godiyar mu, kwatacin rundunar sama mu ke yi.MK 87.1

    Dukan wanda ya bada hadaya ta godiya yana daukakata.” Zbura 50:23. Bari mu zo gaban Allah cikin farin ciki mai saduda da “Ban godiya, da muryar rairawa.” Ishaya 51:3.MK 87.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents