Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
 • Results
 • Related
 • Featured
No results found for: "".
 • Weighted Relevancy
 • Content Sequence
 • Relevancy
 • Earliest First
 • Latest First
  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents

  KAUNAR ALLAH ZUWA GA DAN-ADAM

  Halitta da wahayi duka suna shaidar kaunar Allah. Ubammu na sama shi ne masomin rai, da hikima da farin-zuciya. Dubi abubuwa masu ban al’ajibi da jimali na halitta. A tuna da dacewarsu ga dukan bukace-bukace, ba na dan-Adam kadai ba, amma na duk sauran abubuwa masu rai. Hasken rana da ruwan sama masu wartsakad da kasa, tuddai da tekuna da sararin duniya, duka suna bayyana mana kaunar Mahalici. Allah ne ya ke biyan dukan bukatar halittarsa yau da gobe. A cikin kalmomi masu dadi, Mai-Zabura ya ce: MK 7.1

  “Idanun dukan mutane suna sauraro a gareka,
  Kana kuwa ba su abincinsu a kan kari.
  Kana bude hannunka,
  Kana biya wa ko wane mai rai muradinsa.” Zabura 145:15, 16.
  MK 7.2

  Allah ya halicci dan-Adam cikakke cikin tsarki da farin zuciya, ita duniya kuwa sa’anda Mahalici ya sifanta ta da hannuwansa ba ta da wani digo na rubewa ko wani duhuduhun la’ana. Ketare dokar Allah ne — dokar kauna — ya jawo bakin ciki da mutuwa. Amma dai, a tsakiyar shan wahalar da zunubi ya jawo, kaunar Allah a baiyane ta ke. An rubuta (cikin Farawa 3:17) cewa Allah ya la’anta kasa sabili da mutum. Su wadannan kaya da Tsarkakkiya — abubuwa masu wuya da gwajegwaje wadanda suka sa zaman duniyan nan ya zama na wahala da damuwa—an yi su ne domin jin dadin nan ya Adam, watau sashi ne na cikin horon da a ke bukata a cikin shirin da Allah ya yi domin tada dan-Adam daga cikin kaskancin da zunubi ya kawo. Amma, ko da shike duniya ta fadi, ba bakin ciki da dacin rai ne kacfai suka rage ba. A cikin halitta kanta akwai sako masu yawa na bege da ta’ aziya. Akwai furarruka bisa sarkakkiyan, fure mai kamshi kuma ya baibaye kayayuwan.MK 7.3

  “Allah kauna ne” a rubuce ya ke bisa ko wane furen da ya kusa bucfewa, da bisa ko wane sabon reshen ciyawa. Kyawawan tsuntsaye da su ke cika sararin sama da muryoyin wakokinsu na farin ciki, da furarruka da su ke dad ada iska da kamshinsu, da dogayen itatuwa na jeji da su ke rufe duniya da ganyayensu, duk suna shaida kauna irin na ma-haifi na Allahnmu, suna kuma shaida cewa muradinsa ne ya sa ‘ya’yansa su yi farin ciki.MK 7.4

  Magnar Allah tana baiyana bayyana halinsa. Shi da kansa ya furta kaunatasa mara iyaka da tausayinsa. Sa’anda Musa ya yi addu’a ya ce “Ka nuna mani darajarka,” Allah ya amsa “Zan sa dukan nagartata ta gibta a gabanka.” Fitowa 33:18, 19. Wannan shi ne daukaka — tasa. Ubangiji ya gibta ta gaban Musa, ya yi shela ya ce “Ubangiji, Ubangiji, Allah ne chike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinkai da gaske. Yana tsaron jinkai domin dubbai, yana gafarta laifi da sabo da zunubi.” Fitowa 34:6, 7. Shi mai-jinkirin fushi ne, mai yalwar alheri.” (shi “Allah mai nasiha ne, cike da juyayi” Yunana 4:2) “Domin yana jin dadin jinkai.” Mikah 7:18.MK 8.1

  Allah ya daure zukatanmmu hade da kansa ta wajen alamu marassa iyaka a cikin sama da bisa kan duniya. Ya nemi ya baiyana kansa garemu ta wurin ayyukan halittansa. Amma ko su ba su baiyana mana sosai yadda ya kamata ba. Kuma ko da shi ke an nuna wadannan shaidodi ta hanyoyi daban daban, makiyin dukan abu mai kyau ya makantar da hankulan ‘yan-Adam har ya sa suna duban Allah a tsorace. ‘Yan-Adam suna tunawa da Allah kamar wani mai tsanani wanda ba ya gafara. Shaitan ya sa ‘yan-Adam suna sifanta Allah kamar alkali mai tsanani, ko kamar mai bin bashi mara siyasa wanda ba ya rangwame. Shaitan ya sifanta Allah kamar wani ne wanda ya ke zura idanu na kishi kan ko wane irin tuntube ko kuskure da ‘yan-Adam suka yi, domin ya ziyarce su da hakunci. Sabili da a shafe wannan inuwa mai dufuntawa ne tawurin bayyana kaunar Allah mai-girma ga duniya. Yesu ya zo ya zauna tare da’ yan-Adam.MK 8.2

  Dan Allah ya zo daga Sama domin ya baiyana Uba. “Ba wanda ya taba ganin Allah dadai, Da haifaffe kadai wanda ke chikin kirjin Uba, shi ya bada labarinsa.” Yohanna 1:18. “Kuma ba mai- sanin Uban, sai Dan da dukan wanda Dan ya nufa shi bayana masa.” Matta 11:27. Sa’ad da daya daga cikin almajiran ya ce “Ka nuna mana Uban,” Yesu ya amsa ya ce “Na dade wurinku hakanan Filibbus, kai kwa ba ka san ni ba? Wanda ya gan ni ya ga Uban; kaka fa kana chewa ka nuna mamu Uban? Yohanna 14:8, 9-MK 8.3

  A cikin baiyana sakonsa ga duniya, Yesu ya ce “Ubangi ji ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa: ya aikeni domin in yi ma damraru shela ta saki, Da mayaswar gani ga makafi, in kwance wadanda an kuje su.” Luka 4:18. Aikinsa ke nan. Ya yi ta tafiy ako ina yana aikin nagarta, yana warkas da dukan wadanda Shaitan ke wahalshe su. Akwai kauyuka masu yawa lafiyayyu inda ba a jin wani nishi na rashin lafiya a ko wane gida, domin ya ratsa ta cikin su, ya warkas da duk marassa lafiyan da ke ciki. Aikinsa ya shaida lallai shi shafaffe ne daga sama. A cikin ko wane aiki nasa an baiyana kauna, da jinkai da tausayi. Zuciyatasa ta nuna taushin juyayi zuwa ga ‘yan Adam. Ya daudi kama irin ta dan-Adam domin ya iya gane bukace-bukacen dan-Adam. Matalauta da kaskantattu ba su ji tsoron kusance shi ba. Har ma yara kanana sun je wurinsa. Su kan so su haye kan guwawunsa, su dube shi a fuska sosai, fuska wadda ta ke cike da kauna.MK 9.1

  Yesu bai danne ko magana guda na gaskiya ba; amma a ko wane lokaci yana furta ta cikin kauna. Cikin dukan dawainiya tasa da jama’a, ya kan yi zurfin tunani. Bai taba yin gatse cikin magana tasa ba, ko ya yi wani furci mai tsanani ba tare da dalili ba, ko ya dauki zafin rai ba dalili. Ya kan facfi gaskiya amma cikin kauna. Ya haramta riya, da rashin bangaskiya, da laifi, amma da hawaye cikin murya tasa sa’adda ya ke tsawatawa. Ya yi kuka sabo da Urushalima, birnin da ya ke kauna, birnin da ta ki ta karbe shi, shi wanda ya ke shi ne hanya, shi ne gaskiya, shi ne rai. Su sun ki shi, Mai-ceto, amma shi ya dube su da idon rahama, da tausayi. Zamansa na duniya zama ne na musun kai da tunanin abin da zai amfani wacfansu. Ko wane mai rai yana da daraja a wurinsa. Ko da shi ke a ko wane lokaci yana kame kansa da kwarjinin nan irin na Sama, yana kulawa da sauran iyalin Allah. A ganinsa dukan ‘yan-Adam fadadcfu ne, wadanda ya zama wajibi ne a gareshi ya cece su.MK 9.2

  Haka aka baiyana halin Kristi cikin irin zaman da ya yi. Wannan ne halin Allah. Daga cikin zuciyar Uban ne rafuffukan tausayi, yadda Kristi ya baiyana, su ke gudanowa zuwa ga ‘yan-Adam Yesu, mai-ceto, mai tausayi, Allah ne ya “Bayana chikin jiki.” 1 Timothawus 3:16.MK 10.1

  Domin a panshe mu ne Yesu ya zo duniya, ya sha wahala, ya mutu. Ya zama “mutum mai bakin ciki,” domin mu zama masu taraiya cikin farin ciki har abada. Allah ya yarda Dansa kaunatacce, wanda ya ke cike da nasiha da gaskiya, ya fito daga duniya wadda darajatta ba ta misaltuwa, ya zo duniya wadda ta yi baki kirin da zunubi, wadda ta dufunta da inuwar matuwa da la’ana. Ya yarda masa ya bar jin dadi na kirjinsa na kauna, da ban-girman da mala’iku su ke ba shi, domin ya sha kunya, da ba’a da kaskanci, da kiyayya, da mutuwa. “Foro kuma mai-kawo lafiyarmu a kansa ya ke; ta wurin dukansa da ya sha mun warke.” Ishaya 53:5. Ga shi can a cikin jeji, ga shi can a Gethsemane, ga shi can bisa giciye! Dan Allah mara tabo ya sa kansa daukar Kayan zunubi. Shi wanda daya ya ke da Allah, ya ji a cikin ransa wannan irin mugun rabuwa da zunubi ya kawo tsakanin ransa Allah da dan-Adam. Wannan ne ya sa ya furta cikin radadi ya ce, “Ya Allahna, ya Allahna, Dom mi ka yashe ni?” Matta 27:46. Kayan zunubi ne, da sananin girma kayan zunubi, da sananin rabuwa da ya kawo tsakanin Allah da ruhohin ‘yan-Adam — sananin wannan ne ya karya zuciyar Dan Allah.MK 10.2

  Amma fa ba a yi wannan babban baiko domin a halicci kauaa zuwa ga dan-Adam a cikin zuciyar Uban ba, ko don a sa shi ya yarda ya yi ceto. A,a, Ba haka ne ba ko kadan. “Gama Allah ya yi kaunar duniya har ya bada Dansa haifafe shi kadai.” Yohanna 3:16. Uban yana kaunar mu, ba domin wannan babban pansa ba, amma shi da kansa ya yi tanadin wannan pansar domin yana kaunar mu. Yesu shi ne hanyar da Allah zai iya kwararo kaunar ta gangaro bisa duniya wadda ta kangare. “Allah yana chikin Kristi yana sulhunta duniya zuwa kansa.” 2 Korinth. 5:19. Allah ya sha radadi tare da Dansa. A cikin racfadi na lambun Gethsemane, da cikin radadin mutuwa a Kalvari, a can ne zuciya mai kauna mara iyaka ta biya tamanin pansan mu.MK 10.3

  Yesu ya ce “Domin wannan Uba yana kamnata, sabada ina bada raina, domin in amso shi kuma.” Yohanna 10:17. Watau “Ubana ya kaunace ku har ya fi kaunata domin ba da raina da na yi domin pansarku. Ta wajen zama lamuni domin ku, wajen ba da raina dungum, ta wajen daukar basusuwanku, da laifofinku, Ubana ya kaunace ni; domin ta wajen ba da kaina da na yi ya zama hadaya, a iya baratad da Allah, kuma shi ne mai baratad da wanda ya ba da gaskiya ga Yesu.”MK 12.1

  Ba mai iya pansar mu sai Dan Allah kadai, domin Shi kacfai ne da ya ke daga zuciyar Allah zai iya ba da labarinsa. Shi kadai ne da ya san tsawo da zurfi na kaunar Allah zai iya baiyana ta. Babu wani abu wanda ya fi baikon da Kristi ya yi domin dan-Adam facfadcfe da zai iya furta kaunar Uban zuwa ga ‘yan-Adam batattu.MK 12.2

  “Allah ya yi kaunar duniya har ya ba da tilon Dansa haifaffe.” Ya ba da dansa ba wai domin ya zauna tsakankanin ‘yan-Adam ne kadai ba, ko domin daukar zunubansu ne kacfai ba, ko don ya mutu watau hadaya kadai ba, amma ya ba shi domin daukacin ‘yan-Adam duka. Dole ne Kristi ya mai da kansa da tabi’a da dukan bukace-bukace irin na ‘yan-Adam. Shi wanda ya ke a da daidai da Allah ya ke, ya tswafa kansa hade da ‘yan-Adam da igiyoyi wacfanda ba za a tsunke su ba. Yesu “Domin wannan fa a gareshi ba wani abin kumya ba ne shi che da su yan uwa.” Ibraniyawa 2:11. Shi ne Hada- yanmu, Mai-roko sabili da mu, Dan-uwanmu, yana tsaye da jiki irin namu a gaban kursiyin Uban, kuma haka zai kasance cikin sifar abin da ya pansa — Dam-Mutum. Dukan wannan kuwa domin a dagad da dan-Adam daga kaskancin zunubi ne, domin ya haskako kaunar Allah kuma ya zama mai tarayya cikin farin ciki na tsarki.MK 12.3

  Tamanin da aka biya domin pansarmu, da baikon da Allah ya yi mana cikin ba mu Dansa ya mutu domin mu, sun isa su dagad da hankulan mu ga irin matsayin da za mu kai ta wurin Yesu. Kamar yadda aka baiyanawa Yohanna Manzo tsawo, da zurfi, da fadi na kaunar Uba ruwa ga ‘yan-Adam masu hallaka, ya cika da yabo da ban girma mara iyaka, shi kuwa da ya rasa abin magana game da wannan abin mamaki, game da girma, da taushi na wannan Kaunar, sai ya kira halitta dukata dubi irin wannan kauna, ya ce “Duba irin kamna wadda Uba ya bayas garemu, da za a che da mu yayan Allah.” I Yohanna 3:1. Wannan abu ya sa tamanin Dan-Adam ya yi tsada ainun. Ta wajen bata shari’a ‘yan-Adam suka zama talakawan Shaitan. Ta wajen bangaskiya cikin pansar hadayar Yesu, ‘yan-Adam za su iya zama ‘ya’yan Allah. Sabili da daukar tabi’ar ‘yan-Adam, Kristi ya dagad da ‘yan-Adam. An dagad da fadaddu, ta wajen haduwa da Kristi ya dagad dasu, an sa su a matsayin da za su cancanta da sunan ” ‘yanyan Allah.”MK 12.4

  Wannan kauna ba ta da abokin gami. ‘Ya’yan Sarki na Sama! Alkawari mara gami wajen tamani. Abu ne wanda ya kamata a zauna a yi tunani mai zurfi a kan sa. Kauna mara abin kwatantawa zuwa ga duniya wadda ba ta kaunace shi ba. Wannan tunani kansa Abu ne mai sa ruhu yasadduda, mai sa zuciya ta kasance cikin bautar nufin Allah. Gwargwadon yadda muka yi binciken halin mahalici ta wurin giciye, gwargwadon yadda za mu ga jinkai, juyayi, da gafara an cucfe su tare da shari’a, gwargwadon kuma yadda za mu iya ganin shaidodi marasa iyaka na kaunar nan mara iyaka, da juyayi mai tsanani wanda ya fi juyayin kaunar da mahaifiyya za ta nuna ga danta wanda ya kangare.MK 13.1

  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents