Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    MAI-ZUNUBI YANA DA BUKATAR YESU

    A cikin farko am ba Dan-Adam iko da hankali kintsatstse. Cikakke ya ke cikin tabi’a tasa, da cikin jituwa da Allah. Dukan tunaninsa sahihai ne, abubuwan da ya ke buri kan su kuma tsarkakakku ne. Amma ta wajen rashin biyayya tasa aka karkatadda ikonsa, kuma son kai ya dauki matsayin kauna. Tabi’arsa kuma ta ci gaba cikin rashin karfi sabo da laifofi har ya zama ba shi yiwuwa a gareshi, cikin karfin kansa, ya iya sayaiya da ikon mugunta. Ya zama kamame na Shaitan, da kuwa ya kasance cikin wannan matsayi im ba domin Allah ya shiga tsakani ba. Nufin mai jaraba ne ya rusa wannan shiri da mahalici ya yi wajen halittar dan-Adam, domin ya cika duniya da kaito da lalacewa. Kuma nufinsa ne ya rataya duk wannan magunta kan halitta mutum da Allah ya yi.MK 15.1

    Acikin kasancewarsa tun zunubi bai shigo ba, mutum yana zance da Allah cikin farin ciki da shi “Wanda an boye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi chikinsa.” Kolosiyawa 2:3. Amma bayan aikata zunubinsa, ba zai kara iya samun farin ciki tsarkaka ba, domin haka ya nemi ya buya daga fuskar Allah. Har yanzu kuwa haka zuciyar da ba ta sabonta ba ta ke. Ba ta cikin muwafaka da Allah, kuma ba ta jin wani dadi cikin yin zance da shi. Mai zunubi ba zai iya farin ciki a gaban fuskar Allah ba; sai ya ja da baya daga taraiya da tsarkakun halitta. Da ma za a bar shi ya shiga sama ba wai samu wani dacfin rai ba. Ruhu na kauna mara iyaka da ya ke mulki a sama — inda ko wace zuciya tana muwafaka da Zuciyar kauna mara iyaka — ba zai iya motsa komai da zai iya nuna alamar rai a zuciyar mai zunubi ba. Dukan tunaninsa, da abubuwan da ya ke so, da nufinsa, za su zama baki ga mazauna a can. Sai ya zama tsirkiya wadda amonta ta fita daban da na sauran wakokin sama. A gareshi sama za ta zama wurin azaba, zai yi marmari a boye shi daga fuskar shi wanda ya ke Shi ne haske da tsakiyar farin ciki na aljanna. Ba wata shela ce ta tilas wadda Allah ya yi ba da za ta hana miyagu shiga sama, rashin isa su zama abokan taraiya shi zai rufe musu kofa. Darajar Allah a garesu sai ta zama wuta mai hallakaswa. Za su fi kaunar a hallakansu domin su buya daga fuskar shi wanda ya mutu domin ya panshe su.MK 15.2

    Abu ne wanda ba shi yiwuwa mu, don ikon kammu, mu tsira daga ramin zunubi inda muka riga muka nutse. Zukatammu cike su ke da “mugunta, ba kuwa za mu iya sake su ba.“Da ma ya yiwu abu mai- tsabta shi fito daga chikin mara-tsabta! amma ko daya babu!” ‘ ’ Domin himmantuwar jiki gaba che da Allah; gama ba ta chikin biyayya ga shari’ar Allah ba, ba ta iya kwa.” Ayuba 14:4; Romawa 8:7. Ilimi, al’ada, nufi kokarin dan-Adam, ko wane yana da nasa amfani muhimmi, amma ba su da wani karfi .Ya yiwu su nuna halin Kristi a fuska, amma ba su iya sake zuciya, ba su iya tsarkake mabulbulan rai. Dole a samu wani iko mai aiki daga can ciki, sabon rai daga sama, kafin a sake ‘yan-Adam daga zunubi zuwa ga tsarkaka. Kristi shi ne ikon. Alherinsa kadai ya iya ya rayadda matattun tabi’u na ruhu, ya jawo shi zuwa ga Allah, zuwa ga tsarkaka. Mai-ceto ya ce Im ba a haifi mutum daga bisa ba, ba shi da iko shi ga mulkin Allah ba.” Yohanna 3:3- Fadin da akan yi cewa tabi’a ce kawai. za ta ci gaba da kirkin da ke cikin dan-Adam mugun rudi ne kawai. “Mutum mai-tabi’ar jiki bashi karba al’amura na Ruhun Allah ba: gama wauta su ke a gareshi; ba shi kwa da iko shi san su gama ana gwadasu chikin ruhaniya.” “Kada ka yi mamaki da na che maka Dole a haife ka daga bisa.” 1 Korinthiaywa 2:14; Yohanna 3:7. An rubuta game da Kristi cewa “A chikinsa akwai rai, rai kwa hasken mutane ne,’ “Gama babu wani suna kalkashin sama, da aka bayas wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” Yohanna 1:4, Ayukan Manzani 4:12.MK 16.1

    Gane halin alherin kauna na Allah, da kyauta tasa, da sonsa irin na ma-haifi ba su isa ba, Gane hikima da adalcin shari’a tasa, da lura da cewa a kan kyakkyawan tushe mai karfi na kauna aka gina su bai isa ba. Bulus manzo ya gane wadannan duka sa’adda ya ce “Na amsa shari’a mai-kyau che.” “Sharia tsatsarka che.” “Amma ni ba jiki ne, sayayye ne kalkashin zunubi.” Romawa 7:16, 12, 14. Ya yi marmarin ya kai ga matsayi na tsarki, da adilci, wanda ba shi yiwuwa ya samu don ikon kansa, sabo da haka ya yi kuka ya ce “Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi! Wannene za ya tsamo ni daga chikin jikin nan na mutuwa?’’ Romawa 7:24. Irin kukan da ya hau sama ke nan, daga cikin zukata labtattu, cikin dukan kasashe kuma tun adun adun. A garesu duka amsa guda ce, “Duba, ga Dan rago na Allah wanda yana dauke da zunubin duniya!” Yohanna 1:29.MK 16.2

    Akwai alamu da yawa da Ruhun Allah ya nemi ya kwatanta wannan tattibin gaskiya ta wurin su, kuma ya baiyana su a tili ga zukatan da su ke marmari su ‘yantu daga kayan zunubi. Sa’anda Yakubu ya gudu daga gidan ubansa bayan zunubin da ya yi na rudin Isuwa, ransa ya yi nauyi da zunubin da ya yi. Ko da ya ke yana cikin kadaici, yasashshe, ya rabu da duk irin abin da su ke kawo farin ciki da dadin zaman duniya, abin da ya fi tunawa gaba da komai a lokacin shi ne tsoron cewa zunubi ya raba shi da Allah. Cewa Allah ya yashe shi. A cikin wannan matsayi na bacin rai ne ya kwanta bisa tsandaurin kasa, kewaye da shi sai duwatsu kawai, a sama kuwa sai hasken taurari. Yana cikin barci, sai wani irin haske ya baiyana gareshi cikin wahayin da ya ke ciki, ga shi kuwa, daga nan sararin da ya ke a kwance, ya ga kamar inuwar matakai sun nufi sama har kofar sama, a kan matakan kuma ya ga mala’ikun Allah suna kai da komowa daga sama zuwa dasa, kuma daga darajar da ta ke sama, aka ji murya na samaniya da sako na ta’aziya da bege. Ta hakanan aka sanas da Yakubu da abin da zai biya masa muradin zuciya tasa wadda ya fi bukata a lokacin — Mai-ceto. Da farin ciki da godiya ya ga aka baiyana masa hanyar da shi mai zunubi, a iya maida shi cikin zumunci da Allah. Wannan wahayi na asiri da ya gani cikin mafarkinsa yana kwatanta Yesu ne, wanda Shi ke Shi kadai ne hanyar ma’amala tsakanin Allah da dan-Adam.MK 17.1

    Wannan ne alamar da Kristi ya ke nufi a cikin zancensa da Natanayilu sa’anda ya ce “Za ka ga sama a bude, malaikun Allah kuma suna hawa suna sabka bisa Dan mutum.’* Yohanna 1:51. A kan wannan rami mai fadi da ke tsakani, ba za a iya wani ma ma’amala ba. Amma ta wurin Kristi an sake hada duniya da sama. Ta wurin isar kansa Kristi ya gina kadarko bisa wannan rami wanda zunubi ya haka, domin mala’iku masu hidima su iya shiga ma’amalla da dan-Adam. Kristi yana hada dan-Adam fadadde, rarrauna, mara madogara, yana hada shi da Masomin iko mara iyaka.MK 17.2

    Amma dukan mafarke-mafarken ‘yan-Adam da ci gaba, da ko wane kokari nasu na cfaga matsayinsu a banza su ke idan suka bar wannan masomin bege da taimako domin fadaddu. “Ko wache kyakkyawar baiwa da kowache cikakkiyar kyauta daga bisa take.” Yakub 1:17. daga Allah su ke. Babu wani hali mafifici na gaskiya illa daga gareshi. Kristi ne kuwa hanya daya kacfai zuwa ga Allah. Kristi ya ce “Nine hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai.” Yohanna 14:6.MK 17.3

    Zuciyar Allah ta kallafa kanta bisa ‘ya’yansa na duniya da kauna wadda ta fi karfin mutuwa. Cikin ba da Dansa, ya zubo mana dukan sama cikin kyauta guda cfaya tak. Zaman Mai-ceto da mutuwa tasa da roko da ya ke yi sabili da mu, hidimar mala’-iku, da godon da Ruhu ke yi, kuma da Aikin da Uban ya ke yi bisa duka ta wurin duka kuma, da kulawa na mazauna cikin sammai, duk sai da aka hada su domin pansar dan-Adam.MK 18.1

    Kai! bari mu tsaya mu yi tunani a kan wannan baiko mai ban mamaki da aka mika sabili da mu! Bari mu yi kokari mu gane wahala da kwazo wadda Samaniya ta ke batarwa domin ta dawo da batattu ta komo da su gidan Uban. Ba wasu nufe nufe ko wadansu hanyoyi da suka fi su, da za su iya sa wannan abu ya abku; mafificin lada sabo da yin abin da ke daidai, farin cikin sama, zama tare da mala-iku zumunci da kauna na Allah da na Dansa, dagawar da dada facfada ikommu har abada — wadannan duka ba manyan abubuwa ne da suka isa su zuga mu, kuma su karfafa mu, domin mu ba da hidimar kaunar zuci ga Mahalicimmu da Mai-pansarmu ?MK 18.2

    Idan kuwa muka duba ta wata hanya, hukuncin Allah da ya furta gaba da zunubi, sakamako wanda ba shi kawuwa, kaskancin hallimmu, da hallaka daga karshe, duk an nuna su cikin Maganar Allah domin a facfakad da mu gaba da hidimar Shaitan.MK 18.3

    Ashe bai kamata mu kula da Alherin Allah ba? Me kuma ake bukata ya dacfa yi wanda ya fi wannan! Bari mu sa kammu cikin dangantaka da shi wanda ya kaunace mu da kauna mai ban mamaki. Bari mu yi amfani da hanyar da aka bucfa mana, domin a sabonta mu cikin kamaninsa, a komar da mu cikin zumunci da malaiku masu hidima, cikin sulhuntaka da taraiya da Uban da Dan.MK 18.4

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents