Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    GWAJI NA ALMAJIRANCI

    “Idan fa kowane mutum yana cikin Kristi, sabon halitta ne: tsofofin al’amura sun shude; ga kwa sun zama sabobbi.” 2 Kor. 5:17. da suka sa dan-Adam ya fara juyawa, ba zai tabbatar cewa mutum bai juya ba. Kristi ya ce da Nikodimu “Iska ya kan hura wajen da ya ke nufa, kana jin motsinsa kuma, amma ba ka sani wajen da ya ke fitowa, da inda za shi ba: hakanan ne dukan wanda an haife shi daga chikin Ruhu.’’ Yohanna 3:8. Kamar iska, wanda ba a gani, amma ana ji, ana kuwa ganin aikinta, haka Ruhun Allah ya ke cikin aikinsa bisa zuciyar ‘yan-Adam. Ikon sabontuwa wanda ba idon dan-Adam da zai iya gani, shi ya ke haifan sabon rai cikin zuciya, yana halitta sabon rai cikin kamannin Allah. Kuma ko da shi ke aikin Ruhu ba a ganinsa da ido haka kuma jin motsinsa, amma ana lura da bain da ya aikata. Idan zuciya ta sabontu ta wurin Ruhun Allah, irin zaman mu ba da shaidar sakewa. Ko da shi ke ba mu iya yin komai domin mu sake zukatammu, ko mu kawo kammu cikin muwafaka da Allah; ko da shi ke dole ne mu ki yarda da kam mu ko ayyukammu masu kyau, zamammu zai nuna ko alherin Allah yana zaune cikim mu. Za a ga sakewa cikin haleyemmu, cikin tabi’o’immu, da abin da mu ke ciki. Bambancin zai fito a fili ya nuna yadda halayemmu na da su ke da yadda su ke a yanzu. Hali zai baiyana ba ta wurin ayyuka masu kyau ko marassa kyau lokaci lokaci ba, amma ta wurin zama tabi’a ga hali cikin magana ko aikatawa.MK 47.1

    Gaskiya ne ya yiwu a ga halaye na kirki daga waje amma ba tare da ikon sabontawa na Kristi ba. Son girma ko marmarin a ce wane shi ne wane, yana iya sa ya yi zaman kimtsuwa. Ta wacce hanyace fa za mu iya aikata abubuwa nagargaru? Ta wacce hanyace fa za mu iya tabbatar da sashin da mu ke tsaye? Neman mutuncin kai zai sa mu kauce wa mugun zama na zunubi a waje. Zuciya mai son kanta ta iya aikata abubuwa nagargaru.MK 47.2

    Wane ne ke da zuciyarmu? Tare da wa tunanimmu su ke? Kan wa mu kan so ku yi tadi? Wa ke da kaunarmu da kwazommu? Idan mu na Kristi ne, tunannimmu a wurinsa su ke, kuma tunane- tunanemmu masu dacfi a wurinsa su ke. Duk abin da mu ke da shi da yadda mu ke mu kammu, an tsarkake dominsa. Muna marmarin mu samu shaidar kama tasa a jikinmmu, mu yi numfashi cikin Ru- hunsa, mu aikata nufinsa, mu sa ya ji dadi cikin ko wane abu da muka aikata.MK 47.3

    Wadannan da suka zama sababbin halitta cikin Kristi za su fito da ‘ya’yan Ruhu, “Amma diyan Ruhu kamna ne, farinchiki, salama, tsawon jimrewa, nasi ha, nagarta, aminchi, tawali’u kamewa.” Galati- yawa 5 :22, 23. Ba za su kera kansu bisa ga kwadayi na da ba, amma ta wurin bangaskiya na Tan Allah za su bi cikin gurbin sawunsa, su nuna halinsa kamar ta cikin madubi, kuma su tsarkake kansu kamar yadda shi ke mai tsarki. Abubuwan da su ke ki a da su su ke kauna yanzu; abubuwan da su ke kauna a da kuma, su su ke ki yanzu. Mai alfarma da shishigi a da ya zama mai tawaliu da kaskantar zuciya. Mai girman kai da alfarma ta banza a da ya zama mara shishigi. Bugagge ya zama mai hankali, mara kunya kuma ya zama mai tsarki. Al’adu da yayin duniya na banza sai a jingine su waje daya. Masu bin Yesu ba za su bidi adonsu “ya zama na waje” ba “amma boyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi wadanda basu lalacewa, na ruhu mai ladabi mai lafiya.” 1 Bitrus 3:3, 4.MK 48.1

    Babu shaidar tuba na gaskiya sai da ayuka na sakewa. Idan ya mayar da lamuni, ya mayar da abin da ya kwace, ya fadi zunubansa, ya kaunaci Allah da ‘yan-uwansa ‘yan-Adam, sai mai zunubi ya tabbata ya ketare daga mutuwa zuwa rai.MK 48.2

    Sa’nda mu, kangararu, masu zunubi, muka zo ga Kristi muka zama masu taraiya cikin alherin gafararsa, kauna za ta bulbulo daga cikin zuciya. Ko wane kaya ba shi da nauyi, domin karkiyan da Kristi ya ayyana mai sauki ne. Abin da ya wajaba ya zama abin farin ciki, baiko kuma abin murna. Tafarkin da ya zama rufe da duhu a da ya zama mai haske daga hasken Rana ta Adilci.MK 48.3

    Za a ga kyaun halin Kristi a cikin masu binsa. Murna ce a gareshi ya aikata nufin Allah. Kauna zuwa ga Allah, kwazo domin daraja tasa, su ne iko mai bayaswa cikin zaman duniya na Mai-cetommu. Kauna ita ce ta kawata, kuma ta cfaukaka dukan ayyukansa. Kauna ta Allah ce. Zuciyar da ba a tsarkake ta ke ba, ba za ta iya gane wannan ba. A cikin zuciyar da Yesu ya ke mulki ne kawai a kan samu. “Muna kamna, domin ya fara kamnache mu.” I Yohanna 4:19. A cikin zuciyar da aka sabonta ta wurin alheri na sama, kauna ita ce muhimmin abu cikin aiki. Ita ta ke tausa hali, ita ta ke mulki bisa sababbin tunane-tunnanemmu, da nufe-nufen zuciyarmu, nagar¬garu ko miyagu, ita ta ke nasara bisa magabtaka, ta kuma daukaka soyaiyarmu. Wannan kauna, abin tunawa cikinzuciya, tana dadada zaman duniya tana watsa iko mai tsarkakewa ko ina kewaye.MK 48.4

    Akwai wadansu kuskure guda biyu wadanda ‘ya’yan Allah — musamman su wacfanda suka zo suka amince da alherinsa yanzu — ya kamata su lura da su. Na fari, wanda aka riga aka yi magana akansa, shi ne duba ayyukansu, suna amincewa da ko wane abu da za su iya aikatawa, domin su kawo kansu cikin muwafaka da Allah, Shi wanda ya ke kokarin ya zama mai tsarki ta wurin yyukansa na kiyaye doka, yana kokarin yin abin da ba shi yiwuwa ne faufau. Duk abin da dan-Adam zai yi im ba tare da Kristi ba kazantacce ne da son kai da zunubi. Alherin Kristi ne kawai, ta wurin bangaskiya, zai iya maishe mu masu tsarki.MK 49.1

    Kuskure na biyu kuwa wanda shi ma yana da hatfari mai yawa shi ne cewa bangaskiya cikin Kristi yana daukewa ‘yan-Adam kiyaye dokar Allah, ku kuwa cewa tun da shi ke ta wurin bangaskiya ne kadai za mu zama masu taraiya cikin alherin Kristi, ayyukammu ba su hada komai da pansarmu ba.MK 49.2

    Amma fa lura a nan cewa biyayya ba abu ne kawai na waje da za a aikata ba, amma bauta ne na kauna. Dokar Allah hanya ce ta furta aininhin tabi’arsa, shi ne ya ke kamanta manyan muhimman abubuwa na kauna, domin haka shi ne tushen mulkinsa cikin sama da duniya. Idan zukatammu sun sabonta cikin sifar Allah, idan aka dasa kauna ba-samaniya cikin zuciya, ashe ba dokar Allah ce za a aikata cikin zaman duniya ba? Sa’anda aka dasa muhimman abu¬buwa na kauna cikin zuciya, sa’anda aka sabonta dan-Adam cikin surar Mahallicinsa, an cika alkawaran sabon alkawari, “In sa doko- kina a bisa zuchiyarsu, a bisa hankalinsu kuma in rubuta su.’’ Ibrani- yawa 10:16. Idan kuwa aka rubuta dokar bisa zuciya, ashe ba sai ya sake sifanta zaman duniya ba? Biyaiya — bauta da zaman aminci ga kauna — shi ne alama na gaskiya na almajiranci. Littafi Mai- tsarki ya ce “Gama kamnar Allah kenan, mu kiyaye dokokinsa, ‘ “wanda ya che, Na san shi, amma ba ya kiyaye dokokinsa ba,makar yachi ne; gaskiya kwa ba ta chikinsa ba.” I Yohanna 5:3; 2:4. Maimakon kawas da yan-Adam daga biyayya, bangaskiya ce kacfai take maise su masu tarayya cikin alherin Kristi, ita ce take sa mu yi biyayya.MK 49.3

    Ba mua samun ceto ta wurin biyaiyarmu; gama ceto kyauta ne daga Allah, wanda 2a a karba ta wurin bangaskiya. Amma biyayya diyar bangaskiya ce “Kun sani aka bayana shi domin daukan zunubai, a chikinsa kwa babu zunubi. Dukan wanda ya ke zamne chikinsa ba shi aika zunubi ba: dukan wanda ya ke aika zunubi ba ya taba ganinsa ba ba ya san shi kuma.” 1 Yohanna 3:5, 6. A nan ne gwaji na gaske ya ke. Idan muna zaune cikin Kristi, idan kaunar Allah tana zaune cikim mu, abin da mu ke ji cikin rammu, tunane-tunanemmu, ayyukammu, duka za su zama cikin muwafaka da nufin Allah yadda aka fade su cikin dokarsa mai tsarki. “Yayana kankanana, kada ku bar kowa shi bashe ku daga hanya: wanda ya ke aika adilchi mai- adilchi ne, kamar yadda shi mai-adilchi ne.” I Yohanna 3:7. An dada ba da azancin adili bisa ga matsayin dokar Allah mai tsarki, kamar yadda aka fadi cikin dokoki goma da aka bayas a bisa dutsen Sinai.MK 50.1

    Irin bangaskiyar nan cikin Kristi wadda za ta dauke wa ‘yan- Adam biyaiya ga Allah, ba bangaskiya ba ce, rudi ce. “Bisa ga alheri an checheku ta wurin bangaskiya,” “Hakanan, kwa bangaskiya, im ba ta da ayuka ba, matachiya che chikin kanta.” Afisawa 2:8; Yakub 2:17. Yesu ya fadi a kansa kafin ya zo duniyar nan ya ce “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, Hakika, shari’arka tana chikin zuchiyata.” Zabura 40:8. Kuma ba a dade kafin ya koma cikin sama ba ya sake cewa “na kiyaye dokokin Ubana, ina zamne kwa chikin kamnatasa.’’ Yohanna 15:10, Littafi Mai-tsarki ya ce, “Ta wurin wannan mun sani mun san shi, idan muna kiyaye dokokinsa . . . Wanda ya che yana zaume chikinsa ya kamata shi da kansa ya yi tafiya kamar yadda shi ya yi tafiya.” 1 Yohanna 2:3-6. “Gama Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, ku bi sawunsa.” 1 Bitrus 2:21.MK 51.1

    Sharadin rai na har abada a yanzu daidai ya ke kamar yadda ya ke tun tuni — kamar yadda ya ke a sama kafin faduwar iya- yemmu na fari — watau cikakken biyaiyya ga dokar Allah, cikakken adilci. Idan aka ba da rai na har abada a kan sharadin da bai kai wannan ba, farin cikin dukan halitta zai shiga babban hadari. Hanya za ta budu domin zunubi, da dukan abokan tafiyarsa, su ne bakin ciki da wahala, za su kuwa dauwama har abada.MK 51.2

    Ya yiwu ga Adamu, kafin faduwa tasa, ya yi halin adilci ta wurin yin biyayya da dokar Allah. Amma ya kasa yin haka, kuma domin zunubinsa, tabi’ummu sun fadi, ba kuwa za mu iya maida kammu masu aikata adilci ba. Tun da shi ke muna da zunubi, ba mu da tsarki, ba mu iya yin biyaiya da doka mai tsarki daidai. Ba mu da adilci na kammu wanda za mu bayar musayar abin da dokar Allah ke nema a garemu. Amma Kristi ya nuna mamu tafarkin tserewa. Ya yi zaman rashin zunubi. Ya mutu domin mu, yanzu kuma ya lamunta ya dauki zunubammu ya kuma bamu adilcinsa. Idan kuka ba da kanku gareshi, kuka karbe shi shi ne Mai-cetonku, a sa’annan, komai zunubin zamanku na da, sabili da shi za a lasafta ku adilai. Halin Kristi ya tsaya maimakon halinku, kun zama abin karba gaban Allah kamar ba ku yi zunubi ba.MK 51.3

    Fiye da haka, Kristi yana sake zuciya. Yana zaune cikin ku ta wurin bangaskiya. Sai ku rike wannan mahadi tsakaninku da Kristi ta wurin bangaskiya da ba da nufinku dungum gareshi; muddan kuna yin haka kuwa, zai yi aiki a cikin ku ya nufe ku ku aikata bisa ga jin dad’ insa. Domin haka za ku iya fadi ku ce. “Yanzu kuma ba ni ba ne ina rayuwa, amma Kristi ke rayuwa daga chikina: wannan rai kwa da ni ke rayuwa chikin jiki yanzu ina rayuwa chikin bangaskiya, bangaskiya wadda ta ke chikin Dan Allah, wanda ya kamnache ni, ya bada kansa kuma domina.” Galatiyawa 2:20. Haka Yesu ya ce da almajiransa, “Gama ba ku ne kuna fadi ba, amma Ruhun Ubanku ne mai fadi a chikinku.” Matta 10:20. Sa’nnan tare da Kristi yana aiki a cikin ku, za ku baiyana daidai irin halin, kuna kuma aikata ayyuka daidai irin su ayyukan adilci da biyaiya.MK 51.4

    Domin haka ba mu da wani abu a cikim mu da za mu yi ruba da shi. Ba mu da hanyar daukaka kammu. Hanyar begemmu guda cikin adilcin Kristi muka samu, da kuma cikin abin da Ruhunsa ya aikata a cikim mu ko ta wurimmu.MK 52.1

    Idan muna maganar bangaskiya, akwai bambanci da ya kamata mu lura da shi. Akwai wani irin abin da akan gaskanta wanda ya bambanta da bangaskiya. Kasancewar Allah da ikonsa, kasancewar Magana tasa (Kalma tasa), tabbatattun abubuwa ne da ko Shaitan da rundunarsa ba su musantawa a zuci. Littafi Mai-tsarki ya ce “Aljanu kuma suna gaskantawa, suna kwa rawan jiki.” Yakub 2:19, amma wannan ba bangaskiya ba ne. Inda ba gaskantawa cikin Maganar Allah ne kadai ba, amma da ba da zuciya gareshi, inda aka ba da zuciya gareshi, aka kallafa kauna gareshi, to akwai bangaskiya — bangaskiya wadda ta ke aiki ta wurin kauna, ta tsarkake ruhu. Ta wurin wannan bangaskiya ana sabonta zuciya cikin surar Allah. Zuciyar kuwa da ta ke matsayinta na rashin sabontuwa a da, ba ta karkarshin dokar Allah, ba shi yiwuwa kuwa ta zauna karkashin dokar Allah cikin wannan matsayi; yanzu sai ta yi farin ciki cikin dokokinsa masu tsarki; ta kuwa furta tare da mai-zabura ta ce “Ina kamnar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.” Zabura 119:97. Kuma an cika adilcin shari’a a cikim mu “Babu kayaswa fa yanzu ga wadanda ke chikin Kristi Yesu. ’ ‘ Rom 8:1.MK 52.2

    Akwai wadansu da suka san kaunar nan mai yin gafara na Kristi, wadanda hakika suna da marmarin su zama ‘ya’yan Allah, amma duk da haka sun gane cewa halayansu ba cikakku ba ne, zamansu yana da aibu, a shirye kuwa su ke yi shakkan ko Ruhu Mai-tsarki ya sabonta zukatansu. Ga irin wacfannan bari in ce, Kada ku ja da baya cikin fid da zuciya. Tilas ne safai mu sunkuya mu yi kuka a kafafun Yesu sabo da tauyewarmu da kuskuremmu, amma kada mu karaya. Ko makiyi ya fi karfin mu, ba a yashe mu ba; Allah bai rabu da mu ko ya ki mu ba. A, a; ba a yashe mu ba; Allah yana lura da mu. A, a, Kristi yana hannun dama na Allah, yana roko sabili da mu. In ji Yohanna kaunataccen ya ce, “Wadannan abu ni ke rubuta maku domin kada ku yi zunubi. Idan kowa ya yi zunubi, muna da Mai-taimako wurin Uba, Yesu Kristi mai-adilchi.” 1 Yohanna 2:1. Kuma kada ku manta da jawabin Kristi da ya ce, “Gama Uba da kansa yana kamnarku.” Yohanna 16:27. Yana marmarin ya koma da ku ga kansa, ya ga tsarkinsa yana haskakawa kamar madubi a cikin ku. Idan kuwa kuna ba da kanku gareshi, Shi wadda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da yin haka zuwa ranar Yesu Kristi: Ku yi addu’a da kwazo; bangaskiya ta dada yawa. Gwargwadon rashin amincewa da ikon kammu, bari mu amince da ikon Mai-pansar mu, za mu kuwa yabe shi, wanda shi ke Shi ne lafiyar fuskokinmu.MK 52.3

    Gwargwadon matsowar ku ga Yesu, gwargwadon ganin laifofinku, domin kuwa ganinku zaizama sosai, rashin cikarku zai fito daban cikin gwaji da cikakkiyar tabi’arsa. Wannan shi ne shaida cewa rudin Shaitan sun rasa ikonsu, kuma ikon Ruhun Allah mai rayaswa yana farkad da ku.MK 53.1

    Babu wata zuzzurfar kauna domin Yesu da za ta zauna cikin zuciya wadda ba ta lura da zunubin kanta ba. Ruhun da aka sabonta ta wurin alherin Kristi zai so halinsa ba-samaniya; amma idan ba mu ga tauyewar halayem mu ba, wannan shaida ne wadda babu tantama cewa ba mu ga kayu da jimali na Kristi ba.MK 53.2

    Gwargwadon rashin ganin wani abin girmamawa cikin kammu, gwargwadon abu mai yawa da za mu gani cikin tsarki da jimali na Mai-cetommu, Ganin zunubammu zai kora mu zuwa gareshi wanda zai iya gafara, kuma a lokacin da ruhu, cikin gane rashin karfinsa, ya mika hanu zuwa ga Kristi, Shi zai baiyana kansa cikin iko. Gwargwa¬don yadda hankalimmu mai bukata ya ke kora mu zuwa garesi da zuwa wurin Maganar Allah, gwargwadon ganin daukaka da za mu yi wa halinsa, gwargwadon dada haskaka sura tasa kamar cikin madubi.MK 53.3

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents