Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
  • Results
  • Related
  • Featured
No results found for: "".
  • Weighted Relevancy
  • Content Sequence
  • Relevancy
  • Earliest First
  • Latest First
    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents

    YIN FARINCIKI CIKIN UBANGIJI

    An kira ‘ya’yan Allah domin su zama wakilan Kristi, su nuna nagarta da jinkan Ubangiji. Kamar yadda Yesu ya baiyana mana ainihin gaskiyar halin Uban, haka kuma mu za mu baiyana Kristi ga duniya wadda ba ta san kauna tasa, mai taushi, mai tausayi, ba. “Kamar yadda ka aiko ni chikin duniya, haka kuma na aike su chikin duniya.” Ni a chikinsu, kai kuma chikina, . . . domin duniya ta sani ka aiko ni.” Yohanna 17:18, 23. Bulus Manzo ya ce wa almajiran Yesu, “Bayanannu ne ku wasikar Kristi.” “Sananniya che, karantachiya che ga dukan mutane.” 2 Korinthiyawa 3:3, 2. A cikin ko wane daga cikin ‘ya’yansa, Yesu yana aikawa da wasika zuwa ga duniya. Idan kai mai bin Kristi ne, yana aikawa da wasika ta cikin ka zuwa ga iyalai, kauye, titi da inda ka ke da zama. Yesu, a zaune cikin ka yana so ya yi magana da zukatan wadanda ba su rigaya sun san shi ba. Watakila ba su karanta Littafi Mai-tsarki, ko ba su jin muryar da ta ke zance da su ta cikin warkokinsa, ko ba su ganin kaunar Allah ta cikin ayyukansa. Amma idan kai wakilin Yesu ne na gaske ya yiwu ta wurin ka a bayas da su zuwa ga fahimtar wani abin nagartassa, a kuma ribato su domin su yi masa hidima, su kaunace shi.MK 97.1

    An ayanna masu bin Kristi su zama kamar masu rike da haske kan hanyar zuwa sama. Su ne za su sa hasken da suka samu daga Kristi ya haskaka bisa duniya. Sai zaman su da halin su ya zama daidai yadda ta wurin su wadansu za su samu daidaitaccen fahimta kan Kristi da hidimarsa.MK 97.2

    Idan muna wakiltar Yesu za mu sa hidimarsa ta zama mai kama hankali, kamar yadda ta ke. Masu bin Kristi da su kan tara bakin ciki da daurin fuska bisa ruhohinsu, su dinga gunaguni, suna nuna wa sauran ‘ya’yan Adam sifa na karya na Allah da zama na mai bin Kristi. Suna nunawa kamar Allah ba ya farin ciki ya ga ‘ya’yansa suna murna, cikin yin haka kuwa suna ba da shaida na karya gaba da Ubammu na sama.MK 97.3

    Shaitan ya kan yi murna sa’anda ya iya biyas da ‘ya’yan Allah zuwa cikin rashin bangaskiya da karaya a zuci. Yana farin ciki ya ga ba mu amincewa da Allah, da shakkar yarda tasa da ikonsa na cetom mu. Yana so mu ji cikin rammu cewa Allah zai yi mana lahani ta wurin nasihohinsa. Aikin Shaitan ne ya nuna Allah kamar mara juyayi da tausayi. Ya kan canja gaskiya game da Allah. Ya kan cika tunani da zace-zace na karya game da Allah, kuma, mai- makon mu zauna a kan gaskiya game da Ubammu na sama, safai mu kan kallafa ran mu a kan yadda Shaitan ya nuna Shi cikin karya, har mu ki darajanta Allah ta wajen kin yarda da shi da yin kunkuni gaba da shi. Tutur Shaitan yana nema ya sa zaman addini ya yi baki. Yana sa a ga zaman addini abu ne mai wuya da wahalarwa, ta haka fa, sa’anda mai bin Kristi ya baiyana irin wannan hali a kan addini cikin zamansa, yana goyon bayan karyar Shaitan ke nan ta wurin rashin bangaskiyarsa.MK 98.1

    Da yawa, cikin tafiya kan hanyar zaman duniya, su kan zauna a kan kurakuransu da kasawa tasu da masifunsu, kuma zukatansu su kan cika da bakin ciki da karayar zuciya. Sa’anda na ke Turai, wata ‘yar-uwa wadda ta ke yin irin wannan, wadda kuma take cikin rashin kwanciyar rai, ta yiwo mini wasika tana tambayata im ba ta maganganu na karfafawa. Kashegari, da dare, bayan na karanta wasikarta, na yi mafarki wai ina cikin wata gonar fure, kuma sai ga wani kamar mai lura da gonar yana kewayawa da ni ta kan han- yoyin cikin gonar, ni kuma ina tatsinkan furarruka ina jin dadin kamshinsu. Sai ‘yar-uwata, wadda ta ke tafiya tare da ni a barayi guda ta jawo hankalina kan wadansu dayayuwa marasa kyaun gani da suka tsare mata hanya. Ga ta can ta tsaya tana kuka da bacin rai. Ita ba tana biye da jagaba kan hanya ne ba, amma cikin sarkakiya da kayayyuwa ta ke. Sai tana fadi da kunkuni a rai wai, “Ashe ba abin tausayi ne ga gonar furen nan mai kyau haka ta zamma kuwa ta baci da kayayuwa?” Sai jagaban ya ce “Fita sha’anin kayayuwan don kuwa za su ji maki ciwo. Ke dai tsinki rozis, da su lili da jajjayen kawai.”MK 98.2

    Ba wacfansu abubuwa masu dadin tunawa cikin zamanka na duniya? Ba ka taba samun wacfansu lokatai sa’anda zuciyarka ta kada don farin cikin da Ruhun Allah ya sa ba? Idan ka duba baya cikin surorin zamanka na duniya, ba ka kan zo kan wadansu shafi masu dagadda rai ba, Idan ka duba baya cikinsu kuwa ba kakan yi baban tunani ba? Alkawaran Allah, kamar furanni masu kamshi, ba su yin girma a dama ko hagu da tafarkinka? Ba za ka bar jamalinsu da dadinsu su cika zuciyarka da farin ciki ba?MK 98.3

    Sarkakiyan da kayayuwan sai su ji maka ciwo su bata maka rai kawai, kuma idan su kawai ka ke tsinkewa kana baiwa wadansu, ashe ba hana wadnda ke kewaye da kai ka ke yi su yi tafiya cikin hanyar rai, kana kuma rage albarkar Allah da kanka ba?MK 99.1

    Ba hikima ba ne a tara tunanin dukan abubuwa marassa dadi da suka wuce cikin zama na baya — zunubai da masifu — a yi zance a kansu har karayan zuciya ya kewaye mu. Ruhu wanda ya ke da karaya cike ya ke da duhu, yana rufe hasken Allah waje daga ruhunsa, yana kuma jefa inuwa kan hanyar wadansu.MK 99.2

    Sai mu gode wa Allah sabo da hotunan da ya ba mu kyauta Bari mu tattara wuri daya tabbatawarsa mai albarka na kauna tasa domin mu rika kallonsu tutur. Dan Allah ya bar kursiyin Ubansa, ya rufe allanntaka tasa da mutunci, domin ya kwato cdn-Adam daga ikon Shaitan. Nasara tasa sabili da mu ne, bude sama ga cfan-Adam, baiyanawa idon dan-Adam farfajiyi inda Allah ya kware daraja tasa; fadaddiyar kabila an cfaga ta daga ramin lalacewa inda zunubi ya tsunduma ta, aka kawo ta cikin haduwa da Allah madauwami, kuma bayan mun daure gwaji na sama ta wurin ban¬gaskiya cikin Mai-pansarmu, muka rufe jikimmu da sutura da adilcin Kristi, daukakkakku zuwa ga kusiyinsa — wadannan su ne hotunan da Allah ya ke so mu yi tunani a kansu.MK 99.3

    Sa’anda ya zama kamar muna shakkar kaunar Allah, muna kin yarda da alkawaransa, muna kaskanta shi, muna kuma jawo bacin rai ga Ruhu Mai-tsarki. Yaya uwa za ta ji idan ‘ya’yanta suna kuka da ita ko wane lokaci, kamar ba son su da arziki ta ke yi ba, alhali kuwa duk kokarin zamanta na duniya tattalin su ta ke yi domin ta zama musu jin dad’i da kwanciyar rai? Bisa ga misali a ce suna shakkar kauna tata, wannan zai karya zuciya tata. Yaya uba ko uwa za su ji idan ya’yansu suka yi musu haka? Kuma yaya Ubanmmu na sama zai dube mu, idan ba mu yarda da kauna tasa ba, wadda ta sa shi ya ba da tilonsa Dansa haifaffe domin mu sami rai? Manzo ya rubuta cewa, “Wanda baya kebe Dansa ba, amma ya bashe shi domin mu duka, kaka za ya rasa ba mu abu duka kuma tare da shi a yalwache?” Romawa 8:32. Duk da haka guda nawa ne, ta wurin ayyukansu, balle fa da baka, su ke cewa, “Ubangiji bai yi nufin wannan domina ba. Watakila yana kaunar wacfansu, amma baya kauna ta?’’ Irin wannan duka yana cutar ruhunku, ko wace kalma ta shakka da za ka furta, kiran jarabar Shaitan ne, karfafawa ne a cikin ranka ka yi shakka, kuma yana kore maka mala’iku masu hidima. Sa’anda Shaitan ya jarabce ka, kada ka zabi ka bucfe kofa ga abin da ya ke facfi, zuciyarka za ta cika da tambaye-tambaye na tawaye. Idan ka yi zancen abin da ka ji cikin ranka, duk abin da ka furta na wajen shakka ba komowa kanka kadai zai yi ba, amma zai zama iri da zai tsiro ya ba da ‘ya’ya cikin zaman wadansu, watakila kuwa ba zai yiwu a kankare abin da maganganunka suka jawo ba. Watakila kai da kanka ka iya warkewa daga zamani na jaraba ko daga tarkon shaitan, amma watakila wadansu wacfanda suka janyu ta wurin maganganunka ba za su iya tserewa daga rashin bangaskiyar da ka furta ba. Muhimmin abu ne mu yi maganar abubuwan da za su ba da karfi na ruhaniya da rai kadai.MK 99.4

    Mala’iku suna kasa kunne su ji irin labarin da za ku kaiwa duniya a kan Ubanku na sama. Bari dai zancenku ya zama a kan wanda ya ke da rai yana roko dominku a wurin Uban. Sa’anda ka kama hannun abokinka, bari yabo ga Allah ya kasance a bisa lebunanka da cikin zuciyarka. Wannan zai jawo hankalinsa zuwa ga Yesu.MK 100.1

    Dukan ‘yan-Adam suna shan gwaji, suna da bacin rai masu wuyan dauka, suna da jarabu masu wuyan a yi musu tsayyayya. Kada ku fadi wahalce-wahalcenku ga yan-uwan ku ‘yan-Adam, amma ku kai komai ga Allah cikin addu’a. Ku maishe shi doka kada ku ambata ko magana guda na shakka ko na karya zuciya. Kua iya yin abubuwa masu yawa domin haskaka zaman wacfansu da karfafa kokarinsu ta wajen maganganu na bege da dagarwa mai tsarki.MK 100.2

    Akwai rayuka dai da yawa masu mazakuta wacfanda su ke fama da matsi na Jaraba, kusan a shirye su ke su suma cikin kokawa da kansu da kokawa da ikokin mugunta. Kada ka karya zuciyar irin wannan cikin fadan da ya ke yi mai wuya. Ka karfafa shi da maganganu na mazakuta, da bege wacfanda za su tura shi gaba cikin tafarkinsa. Ta haka hasken Kristi ba zai ba da hasken daga gareka ba. “Gama daga chikinmu ba wanda ke rayuwa ga kansa ba.” Romawa 14:7. Ta wurin kokarimmu ba da sanin mu ba, ya yiwu a karfafa wadansu, ko a karya zuciyar wacfansu, a kore su daga Kristi daga gaskiya kuma.MK 100.3

    Akwai mutane da su ke da kuskuren tunani a kan zama da hali na Kristi. Suna tsammani ba shi da wani dimin hali na fara’a, kuma suna tsammani shi mai daurarren fuska ne, mai tsanani, wanda ba shi da farin ciki. Ta hanyoyi dayawa duk al’amuran addini an sa masa launi baki kirin.MK 101.1

    Safai a kan ce Yesu ya yi kuka, amma baa taba ji an ce ya yi mur- mushi ba.Hakika Mai-cetommi mutum ne na yawan bacin rai, ya kuma san bakin ciki, gama ya bude zuciyatasa ga dukan masifu na ‘yan-Adam. Amma ko da shi ke zamansa na musun kai ne, Fuska tasa ba ta nuna wata alama ta bakin ciki ko gunaguni ba, amma tutur ta ke cikin natsuwa mai salama. Zuciya tasa rijiyar mabulbula ne na rai, duk inda ya tafi kuwa yana dauke da hutawa, da salama, murna da farin ciki.MK 101.2

    Mai-cetommu cike ya ke da kwakkwaran nufi da himma, amma dadai ba a taba ganinsa ya murtuke fuska ba. Zaman wadannan da su ke kwaikwayonsa zai zama cike da nufi mai himma, za su kasance da rike mutuncin kansu mai nauyi. Za a hana rashin daukan matsala da himma, babu annishuwa, babu shakiyanci; amma addinin Yesu yana ba da salama kamar kogi. Ba ya kashe hasken farin ciki, ba ya hana fara’a, ba ya ya dusas da fuska mai murmucshi. Kristi ya zo ba domin a bauta masa ne ba amma shi kansa ne zai bauta, idan kuwa kauna tasa tana mulki cikin zuciya, za mu bi gurbin sawunsa.MK 101.3

    Idan a cikin rammu muka fi kula da ayyukan rashin nagarta da adilci na wadansu, zai yi mana wuya mu kaunace su kamar yadda Yesu ya kaunace mu; amma idan muka bar tunaninmu a kan kauna mai ban al’ajibi da tausayi na Kristi domin mu, wannan nufi zai gudana zuwa ga wadansu. Ya kamata mu kaunaci juna, mu ba juna girma, kyale kallon laifuffukan su. Dole mu zama da tawali’u da rashin yarda da kammu. Wannan zai kashe son kai mai kuntatawa, ya maishe mu dattawa masu hannu sake.MK 101.4

    Mai-zabura ya ce “Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta; ka zamma a chikin kasan, ka lizimchi aminchi.” Zabura 37:3. “Ku dogara ga Ubangiji.” Ko wace rana tana da nata dawainiya, da aikace-aikace, kuma idan muka taru mun faya so mu yi zance a kan wahalce-wahalcemmu da gwaje-gwajemmu. Dawainiyar da ba su shafe mu ba su kan kunno kansu, fargaba iri iri, a kan furta rashin kwanciyar rai, har wani zai yi tsammani cewa ba mu da Mai- ceto, mai tausayi, mai dauna, wadda a shirye ya ke ya ji dukan roke-rokemmu, ya kuma zama mana taimako na yanzu a ko wane lokacin bukata.MK 101.5

    Kullum wadansu suna fargaba, suna aron wahala. Kullum alamun kaunar Allah suna kewaye da su; kullun suna jin dadin baiwatasa, amma su kan manta da wacfannan albarka na yanzu. Tutur hankalinsu yana zama kan wani abu mara dacfi wanda su ke fargaban zai abku, ko watakila lallai akwai wata wahala wadda ko da shi ke kankanuwa ce ta kan makantar da idanunsu daga ganin abubuwa masu yawa da ya kamata a yi godiya a kansu. Maimakon wahalce- wahlacen da su kan ci karo da su su kora su zuwa ga Allah, wanda shi ke shi kacfai ne masomin taimakonsu, sai su raba su da shi, domin sun farkad da rashin kwanciyar rai da kishi.MK 102.1

    Mun yi abu mai-kyau kenanan mu zama marasa-bangaskiya haka? Me zai sa mu zama da rashin bangaskiya da rashin yarda? Yesu aboki- mmu ne; duk samaniya ta kula da zaman kwanciyar rammu. Bai kamata mu bar damuwa na yau da gobe su tsorata hankulammu ba, ko su bata mana fuska. Idan muka yarda, ko wane lokaci za mu samu wani abin da zai cakune mu ya ba mu haushi. Kada mu yarda da rashin kwanciyar rai, wanda zai tsorata mu ne kawai, ya kare mu amma ba ya taimakon mu ga daukar jarabu.MK 102.2

    Ya yiwu ka damu cikin zuciyarka domin watakila al’amarinka zai yi duhu, watakila kuma hasara wurin ciniki ta zura maka ido; amma kada ka yi karayar zuciya; ka jefa dawainiyarka ga Allah ka tsaya a natse cikin harka. Ka yi addu’a domin hikima ta bishe al’amuranka cikin hankali, da haka sai hasara ta kawu. Ka yi iyakacin kokarinka abu nagari ya fito cikin dukan al’amuranka. Yesu ya yi alka-warin ba da taimakonsa amma fa sai da kokarin kammu. Sa’anda ka yi bakin kokarinka, kana dogara bisa Mai-cetommu, to sai ka amshi duk abin da ya samu da harka da farin zuciya.MK 102.3

    Ba nufin Allah ne rashin kwanciyar rai ya ami jama’arsa ba. Amma Ubangijin mu ba ya ludin mu. Ba ya ce mana, “Kada ka damu babu hatsari a kan hanyar ka ba,” ya sani akwai jarabobi da hatsaroril, sa’an nan yana fita mana a fili. Ba ya shirin ya cire jama’arsa daga duniyar zunubi da mugunta, amma yana nuna masu mafaka mara-kasawa. Addu’ arsa domin almajiransa shine, Ba Na yin addu’a Ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin Ka tsare su daga Mugun.” Ya ce, “A cikin duniya kuma da wahala; amma ka yi farinciki, Na yi nasara da duniya.” Yohanna 17:15; 16:33.MK 102.4

    A chikin wa’azinsa na kan dutse, Kristi ya koya wa almajiransa nassi-nassi masu daraja game da wajibin bangaskiya ga Allah. Wadannan nassi-nassi kwa an bayar da su domin a karfafa ‘ya’yan Allah na dukan tsara, gashi kwa sun zo har zamaninmu cike da koyaswa da kuma ta’aziya. Mai-ceto ya nuna wa mabiyansa tsuntsayen sama yadda suke wakokinsu na yabo, ba tare da tunanin damuwa ba, gama *’ba sua shibkawa balle su girbe.” Duk da haka Uba yana cika masu bukatunsu. Mai-ceto yana tambaya, “Ku ba ku fi su daraja da yawa ba?” Matta 6:26. Babba Mai- bayaswa wa mutum da dabba, yana bude hannunsa ya bayar wa dukan halittansa. Tsuntsayen sama basu yi nisa da ganinsa ba. Ba ya jefa abinci a cikin bakunan su, amma Ya kan yi hanyar yadda bukatunsu zasu cika. Dole su tsince hatsin da ya watsar masu. Dole su shirya shekansu. Dole su ciyad da ‘ya’yansu. Su kan tafi wurin aikinsu tare da waka gama “Ubanku na cikin sama yana ciyad da su.” Amma “ku ba ku fi su daraja da yawa ba?” Ku masu hikima, masu sujada mai-tsarki, ba ku fi tsuntsayen sama daraja da yawa ba? Ko ba Mai-bayar da rai, wanda shike mai-tsaron ranmu, wanda ya halicce mu cikin sifansa tsatsarka, zai biya mana bukatanmu idan mun bada gaskiya gare shi ba?MK 103.1

    Kristi ya nuna wa alamajiransa furannin jeji, masu girma cikin wadata da haske cikin daraja wanda Uba ya basu domin ya nuna kaunassa. Ya ce “Ku lura da furannin jeji, yadda suke girma.” Wadata da rashin alfahari na wadannan furannin sun fi dukan kawan da Solomon yake da shi. Dukan mafificiyar sutura wadda aikin hannu ya iya yi, ba za a iya kwatanta shi da kyau da wadatan wadannan furanni wacfanda Allah ya yi ba. Yesu yana tambaya “Idan fa Allah ya kan yi wa ganyaye sutura haka, abin da ke rayuwa yau, gobe ana jefawa cikin tanderu, balle ku, ku masu kankantan bangaskiya?” Matta 6:28, 30. Idan kwa Allah Mai-siffatawa Mai-Tsarki, ya kan ba furanni, wadanda suke lallacewa a cikin rana cfaya, da launuka masu sha’awa haka, wane irin lura ne ba zai iya yi wa wadanda ya halicce su cikin siffarsa ba? Wannan nasihan fadakarwa ne ga yawan tunani da shakkar zuciya mara bangaskiya.MK 103.2

    Ubangiji ya gwammace ‘ya’yansa maza da mata su kasance da murna, salama, da biyayya. Yesu yana cewa “Salama ina bar maku; salamata ni ke ba ku: ba kamar yadda duniya ke bayaswa ni nike ba ku ba. Kada zuciyar ku ta bace, kada ta ji tsoro kuma” “Wadannan maganganu nn fada maku domin farin cikina ya zauna cikin ku, domin kuma farin cikin ku ya cika.’’ Yohanna 14:27; 15:11.MK 104.1

    Farin-ciki wanda aka nema daga wurin nufofi na son kai, ba cikin hanyar da ta wajaba ba. abin muni ne mai kawo bari kuma mara jimawa; ya kan wuche hakan nan ya bar ran mutum cike da kadaici da bakin-ciki; amma akwai farin cikin da koshiya cikin bautan Allah; ba a bar Mai-bi ya yi tafiya cikin hanyoyi masu dufu ba; ba a bar shi cikin ladama da hasara ba. Idan kwa bamu sami shagalin wannan duniya na yanzu ba, muna iya yin farinciki cikin begen cewa muna da na duniya mai zuwa.MK 104.2

    Amma ko a nan ma, Masu-bi zasu iya samun farin-ciki na zama tare da Kristi; suna iya samun hasken kaunassa, da kuma jin dadin baiyanuwarsa har abada tare da su. Kowace mataki a cikin rayukanmu tana iya kara kawo mu kusa da Yesu, tana iya bamu ganewa mai zurfi cikin kaunassa, kuma tana iya kawo mu kusa kusa da gidan albarka na salama. Kada fa mu jefas da amincinmu, amma mu kasance da tabbatas- wa fiye da da. “Tun da har wa yau Ubangiji ya taimakemu,” Kuma zaya ci gaba da taimakonmu har zuwa karshe. 1 Samuila 7:12. Bari mu duba taswiran al’amurai, wadanda suke tuna mana da abin da Ubangiji ya yi domin ya ta’azantad da mu ya kuma cece mu daga hannun mai hallakaswa . Bari mu rike cikin tunanin mu, dukan jinkan da Allah ya nuna mana, - hawayenmu da ya share ,dukan azaban da ya kwantar, alhinan da ya dauke, tsoron da ya kora, bukatun da ya biya, albarkatun da ya watsar, - ta wurin haka yana karfafamu domin dukan abubuwan da suka rage mana a hanyar hajjinmu.MK 104.3

    Lallai ne mu sa zuciya ga abubuwan damuwa a cikin fada mai zuwa, amma muna iya hangan gaba zuwa ga abin da ke zuwa, kuma mu che, “Har wa yau Ubangiji ya taimakemu.” “Gwalgwadon tsawon kwan- akinka, gwalgwadon karfin jikinka ne.” Kubawar Shari’a 33:25. Jarabawan ba zai fi karfin da za a bamu mu danka ba, bari kwa mu kama aikinmu inda muka same shi, da bangaskiyar cewa, ko mene ne ya faru da mu,za a bamu karfi gwalgwadon jarabawan.MK 104.4

    Jim kadan kwa za a bude kyauren samaniya domin a shigad da ’yayan Allah, kuma daga lebunan Sarki Mai-daukaka, albarka zai zuba cikin kunnuwansu kamar mawadaciyar waka. “Ku zo, ku masu--albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya domin ku tun kafawar duniya.” Matta 25:34.MK 104.5

    Sa’an nan kuwa, za a kubutattu maraba cikin gidan da Yesu ya ke shirya masu. A chan, abokanansu baza su zama muguntan duniya, makaryata, masu bautan gumaka, mara tsarki, da marasa bangaskiya amma zasu cudanya da wadanda suka kada Shaitan kuma ta wurin alheri mai tsarki suka siffata kamilan hankula. Kowache nufin zunubi, ko-wache rashin kamila da ke damun su a nan, an rigaya an kawas ta wurin jinin Kristi, kuma martaba da hasken daukakansa, da ya fi hasken rana, an basu. Kuma darajar adalcinsa da kamilcinsa, yana haskakawa cikin su, fiye da kawan nan na waje. Kamilai ne su a gaban farin kursiyin, cikin martaba da iko irin na malaiku.MK 105.1

    A chikin tunanin gado mai daraja wanda zai zama nasa, “ina kwa abin da mutum zaya bayas musanyar ransa?” Matta 16:26. Ya yiwu shi matalauci ne, duk da haka yana da wadata da martaba wanda duniyan nan ba zai iya bashi ba. Ran mutum kubutacce kuma wakakkiya daga wurin zunubi, tare da dukan darajan ikonta, mikakkiya zuwa ga bautan Allah, yana da daraja mafi yawa; kuma akwai murna a cikin sama a gaban Allah da mala’ikunsa masu tsarki domin rai daya wanda aka kubutar, murna wanda ake nunawa cikin wakar tsatsarkar nasara.MK 105.2

    Larger font
    Smaller font
    Copy
    Print
    Contents