Loading...
Larger font
Smaller font
Copy
Print
Contents
 • Results
 • Related
 • Featured
No results found for: "".
 • Weighted Relevancy
 • Content Sequence
 • Relevancy
 • Earliest First
 • Latest First
  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents

  BANGASKIYA DA YARDA

  Da shi ke Ruhu Mai-tsarki ya rayad da lamirinka, ka ga wani abu na muguntar zunubi, ka ga ikon zunubi, da laifinsa, da kaitonsa, kuma kana duban sa da kyama. Ka ji a ranka cewa zunubi ya raba ka da Allah, kuma kana cikin bautar ikon mugunta. Gwargwadon kokarin ka tsere, gwargwadon ganewar rashin iyawarka. Nufe-nufenka ba su da tsarki, zuciyarka ba ta da tsabta. Ka gani zamanka na duniya cike ya ke da son kai da zunubi. Kana marmarin ka samu gafara, a tsabtace ka, a ‘yantad da kai. Muwafaka da Allah, zama kama tasa — Me za ka yi ka samu wannan?MK 41.1

  Salama ne ka ke bukata — Gafaran Ubangiji da salama da kauna cikin zuciya. Kudi ba zai iya saye ba, hankalin kwakwalwa ba zai iya samo shi ba, hikima ba za ta kai gareshi ba, ba shi yiwuwa ka yi ko bege, ta wurin kokarin kanka, cewa za ka kai gareshi. Amma Allah ya ba ka shi kamar kyauta “Ba da kurdi, ba da abin biya ba.” Ishaya 55:1. Naka ne idan dai ka yarda ka mika hanunka ka kamo shi. Ubangiji ya ce “Ko da zunubanku sun yi kamar mulufi, za su yi fari kamar snow: ko da suna jawur kamar garura, zasu zama kamar adbuga.” Ishaya 1:18. (tsakiyansa) “Sabuwar zushiya kuma zan ba ku, sabon ruhu kuma zan sa a chikinku.” Ezekiel 36:26.MK 41.2

  Kun fadi zunubanku, kuma a cikin zukatanku kun jingine su waje daya. Kun kudurta za ku ba da kanku ga Allah. To, ku je wurinsa yanzu, ku roke shi ya wanke zunubanku, ya ba ku sabuwar zuciya. Sa’ annan ku gaskanta ya aikata wannan domin ya rigaya ya yi alkawari. Wannan shi ne abin da Yesu ya koyas sa’anda ya ke duniya, cewa kyautar da Allah ya ba mu, dole mu tabbata mun karba, kuma namu ne. Yesu ya warkas da mutane daga cuce-cucensu sa’anda su ke da bangaskiya cikin ikonsa; ya taimake su cikin abubuwan da suka iya gani, ta haka ya hura musu bangaskiya cikinsa a kan abubuwan da ba su iya gani ba — wato biyas da su zuwa gaskanta ikonsa na gafarar zunubai. Ya fadi wannan a fili sa’anda ya ke warkas da mai ciwon inna; “Amma domin ku sani Dan mutum yana da iko a duniya shi gafarta zunubai (daga nan ya che ma mai-chiwon inna), Tashi, ka dauki shimfidarka, ka tafi gidanka.” Matta 9:6. Haka kuma Yohanna Manzo ya fadi sa’anda ya ke magana a kan ayyukan al’ajibi na Kristi, “Amma an rubuta wadannan, domin ku bada gaskiya Yesu Kristi ne, Dan Allah, chikin bada gaskiya kuma ku sami rai a chikin sunansa.’’ Yohanna 20:31.MK 41.3

  Daga labaru masu sauki na cikin Littafi Mai-tsarki wadanda aka bayar a kan yadda Yesu ya warkas da masu ciwon za mu iya koyon wani abu na yadda za a ba da gaskiya gareshi domin gafarar zunubai. Bari mu juya ga labarin mai ciwon inna a Bethesda. Shi wannan mai ciwo ba shi da hanyar taimako; shekara arba’im-biyu-babu bai yi amfani da gababuwansa ba. Duk da haka Yesu ya ce masa “Tashi, dauki shimfidarka ka yi tafiya.” Ya yiwu mai ciwon ya ce “Ubangiji, idan za ka iya warskas da ni, na yi biyaiya da kai.” Amma bai fadi haka ba, ya gaskanta maganar Kristi, ya gaskanta an warkas da shi, ya kuwa yi kokarin tashi nan da nan, ya kudurta ya yi tafiya cikin ransa, ya kuwa yi tafiya. Ya aikata bisa ga cewar Kristi, Allah kuwa ya ba shi ikon yin haka. An warkas da shi.MK 42.1

  Ta hakanan kuma ka ke mai zunubi. Ba shi yiwuwa ka samu gafarar zunubanka na da, ba shi yiwuwa ka sake zuciyarka, ka mai da kanka mai tsarki. Amma Allah ya yi alkawari zai yi maka wadannan duka ta wurin Kristi. Ka gaskanta wannan alkawari? Ka fadi zunubanka, ka ba da kanka ga Allah. Ka yi kuduri za ka bauta masa. Muddan ka yi wannan, Allah zai cika nasa alkawarin. Idan dai ka gaskanta alkawarin — ka gaskanta an gafarta maka an kuma tsabtace ka — Allah yana ba da tabbatawa; an maishe ka lafiyayye, daidai kamar yadda Kristi ya ba da iko ga mai ciwon inna ya yi tafiya sa’anda shi mutumin ya gaskanta an warkas da shi. Ya rage kai ka gaskanta.MK 42.2

  Kada ka jira sai ka ji an maishe ka lafiyayye, amma ka ce, “Na gaskanta an warkas da ni, hakannan ne, ba domin ina ji a jiki ba, amma domin Allah ya alkawarta.”MK 42.3

  Yesu ya ce, “Dukan iyakar abinda ku ke addu’a kuna roko kuma, ku bada gaskiya kun rigaya kun karba, za ku samu fa.” Markus 11:24. Akwai sharad’i game da wannan alkawari — Shi ne mu yi addu’rf daidai da nufin Allah. Amma nufin Allah ne ya tsabtace mu daga zunubi, ya maishe mu ‘ya’yansa, ya kuma sa mu iya zama na tsarki. Domin haka muna iya rokon wandannan albarka, ku kuwa gaskanta mun karbe su, mu kuma gode wa Allah domin mun karbe su. Daidai ne, kuma haka ne, ba mai ikon hana mu zuwa wurin Yesu domin a tsabtace mu, kuma mu tsaya gaban shari’a ba tare da jin kunya ko nadama ba. “Babu kayaswa fa yanzu ga wadanda ke chikin Kristi Yesu.’’ Romawa 8:1.MK 42.4

  Daga nan gaba kai ba naka ne na kanka ba, an saye ka da tamani “Ba da abubuwa masu-lalachewa ba, da su azurfa ko kwa zinariya, . . . amma da jini mai-daraja, kamar na dan rago mara-aibi; mara- chikas, watau jinin Kristi.” I Bitrus 1:18, 19. Ta wurin wannan sassaukan aiki na ba da gaskiya ga Allah Ruhu Mai-tsarki ya haifi sabon rai cikin zuciyarka. Kai kamar jariri ka ke da aka haifa a cikin iyalin Allah, yana kuwa kaunarka kamar yadda ya ke kaunar Dansa.MK 43.1

  Yanzu fa da shi ke ka ba da kanka ga Yesu, kada ka ja da baya, ka da ka kawas da kanka daga gareshi, amma ko wace rana ka ce “Ni na Kristi ne, na ba da kaina gareshi,” ka kuma roke shi ya ba ka Ruhunsa, ya kiyayye ka ta wurin alherinsa. Da shi ke kuma ta wurin ba da kanka ga Allah, da kuma bangaskiya cikinsa, ka zama da a gareshi, don haka ne za ka zauna a cikinsa. Manzo ya fadi ya ce “Tun da shike kuka karbi Kristi Yesu Ubangiji, sai ku yi ta tafiya a chikinsa hakanan.” Kolosiyawa 2:6.MK 43.2

  Wadansu su kan ji ya kamata su kasance cikin kwanaki na gwaji, kuma wai sai dole sun tabbatarwa Ubangiji cewa sun sake kafin su ruski albarka tasa. Amma suna iya ruskar albarkar Allah ko a yanzu. Dole ne su samu alherinsa, su samu Ruhun Kristi domin ya taimaki rashin karfinsu, im ba haka ba ba za su iya tsayawa mugunta ba. Yesu yana kaunar mu zo gareshi yadda mu ke, cike da zunubi, raunanu masu neman madogara. Ya yiwu mu zo da dukan rashin karfimmu, da wautarmu, da zunubammu, mu fadi a gabansa cikin tuba. Darajatasa ce ya rungume mu cikin hannuwan kauna tasa, ya daure raunukammu, ya tsabtace mu daga dukan rashin tsarki.MK 43.3

  Ga inda dubbai su kan gaza: ba su gaskanta cewa Yesu ya gafarta musu don kansu su kacfai ba. Ba su cfaukan Allah kan maganatasa. Wajibi ne ga dukan wadanda suka cika sharudan kan su su sani don kansu cewa gafarar nan kyauta ake mika ta sabo da ko wane zunubi. Ku jinginar da ko wace shakka na cewa alkawaran nan na Allah ba domin ku ba ne. Alkawarai ne domin ko wane mai zunubi da ya tuba. An tanada karfi da alheri ta wurin Kristi domin mala’iku masu hidima su kawo su ga kowane ruhu mai ba da gaskiya. Ba wanda zunubansa suka yi yawa har da ba zai iya samun icarfi, da tsarkakewa, da adilci cikin Yesu ba, wanda ya mutu domin su. Yana jira ya yaye musu tufafinsu da suka yi dauda da kazanta cikin zunubi, ya kuma yafa musu fararen sutura na adilci, yana cewa su rayu, kada su mutu.MK 44.1

  Allah ba ya yi da mu kamar yadda dan-Adam ya ke yi da wani dan-Adam Tunane-tunanensa na jinkai ne da kauna, da juyayi. Allah ya ce “Mai-mugunta shi saki hanya tasa, mara-adilchi kuma shi bar tunaninsa: shi komo wurin Ubangiji, shi kuwa za ya jikansa; wurin Allahnmu, gama za ya yi gafara a yalwache.” “Na shashafe laifofinka kamar hadari baki kirin, kamar girgije kuma zunubanka.” Ishaya 55:7; 44:22.MK 44.2

  “Ga ma ba na jin dadin mutuwar kowa, in ji Ubangiji Yaweh: ku tuba fa, ku yi rai.” Ezekiel 18:32. Shaitan a shirye ya ke ya saci tabbatattun alkawaran nan masu albarka na Allah. Nufinsa ne ya dauke ko wane dan kyalkyali na bege, da ko wane dan haske mai haskakawa daga cikin zuciya, amma dole mu ki yarda ya yi haka. Kada ku kasa kunne ga mai-jaraba, amma ku ce “Yesu ya mutu domin ni in rayu. Yana kauna ta, kuma ba nufinsa ba ne in hallaka. Ina da Uba na sama mai tausayi; kuma ko da shi ke na zagi kauna tasa, ko da shi ke na batar da albarkar da ya bayar a lalace, duk da haka “Ni tashi, in tafi wurin Ubana, in che masa, Ubana na yi zunubi gaban sama, da kuma gabanka: ban isa ba a kara che da ni danka: a maishe ni kamar wani a chikin barorinka.’’ “Amma tun yana da nisa tukuna, ubansa ya hange shi, ya yi juyayi na tausayi, ya yi ta yi masa sumba.” Luka 15:19-20.MK 44.3

  Duk da haka ko shi wannan misali, da ban tausayinsa, bai kai munzulin nuna juyayi mara iyaka na Uba na sama ba. Ubangiji ya fadi ta bakin annabinsa ya ce “Hakika, na yi kamnarka da mada- wamiyar kamna; domin wannan na jawo ka da rahama.” Irmiya 31:3. Tun mai zunubi yana nesa da gidan Uban, yana batar da dukiya tasa a can wata bakuwar kasa, zuciyar uban tana nan tana begen sa, kuma ko wane marmari da ya zocikin zuciya don ya sa a koma ga Allah, roko ne na Ruhu Mai-tsarki, yana nema, da naciya, yana roko yana jawo mai-gantalin zuwa ga zuciyar Ubansa ta kauna.MK 44.4

  Da sauran yin shakka duk da wadatattun alkawaran nan na cikin Littafi Mai-tsarki a gabanka? Kana iya gaskanta cewa sa’anda mai zunubi, abin tausayi, ya yi marmarin komowa, ya yi marmari rabuwa da zunubansa, Ubangiji zai hana shi zuwa kafafunsa cikin tuba? Yi nesa da wadannan tunane-tunane! Ba abin da ya fi ji ma ranka ciwo kamar ka bar wadannan tunane-tunane cikin ranka game da Ubammu na sama. Allah ya ki zunubi, amma yana kaunar mai zunubi, kuma ya ba da kansa cikin surar Kristi domin duk wanda ya ga dama ya tsira, ya samu albarka na har abada cikin mulkin sa mai daraja. Wacce murya ce ta fi karfi ko taushi da za a yi amfani da ita wadda za ta furta kauna tasa zuwa garemu? Ya furta cewa,MK 45.1

  “Ya yiwu mache ta manta da danta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin dan chikinta ba? i, ya yiwu wadannan su manta, amma ni ba ni manta da ke ba.” Ishaya 49:15.MK 45.2

  Ku ta da kanku ku dubi sama, ku da ku ke shakka kuna rawan jiki, gama Yesu yana da rai domin ya yi roko sabili da mu. Ku gode ma Allah domin bada Dansa kaunatacce, ku yi addu’a kuma domin kada ya zama ya mutu domimmu a banza. Ruhu yana kiranku yau. Ku zo ga Yesu da dukan zuciyarku, ku ruski albarka tasa.MK 45.3

  Idan kuna karanta alkawaran nan, ku tuna kalmomi ne masu furta kauna tasa da tausayi wadanda ba a iya fadin su da baka. Ana jawo babbar zuciya ta kauna mara iyaka zuwa ga mai zunubi tare da tausayi mara iyaka “Wanda muna da pansarmu a chikinsa ta wurin jininsa, gafarar laifofinmu.” Afisawa 1:7. Hakika, sai ku gaskanta kawai Allah ne mai taimakonku. Yana so ya mayar da sifa tasa cikin dan- Adam. Idan kuka kusanto gareshi da fadin zunubi da tuba, shi kuma zai kusanto gareku cikin jinkai da gafara.MK 45.4

  Larger font
  Smaller font
  Copy
  Print
  Contents